Sashe 258
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kanki yasan zan rike mashi ke amana zan jajirce na zama abin kwatance dije gata nan itace ta fara fassara min me yake nufi a lokacin. Nima dai nakanyi tunane meyasa Abba din ya yarda a lokacin haka kai tsaye ba tare da yaja ba kamar yadda ya nuna fushinshi a fili gareni ? A yanzu din nakance what god has join together no one should put asunder on it dama Allah ya yomu a tarene kawai amma su mama dasu hjy tsohuwa sun nuna min zuciyarsu a fili a kaina. Do master nida ummah munga abu a lokacin auren mu ummah tayi kuka kamar ranta zai fita amma kuma haka take ban karfin gwiwa kada in yarda wani ya fahinci abinda nake ciki har a kare bukin mu. Ranan dai munyi ta hira a kan lokacin auren mu kafin Dije ta fito mu canza zance bayan kwana biyu yake tambayana ko nayi masa list din sai lokacin na tuna. Na zauna na rubuta shi kuma ya karba ya copy a wayan shi Shehu ya turawa kudi aka sai komai yazo dasu nan part din ummah aka ta aikawa gida gadan yan uwana. Har gun Aisha da Rukky akai gana gidan su hjy tsohuwa abinka da babban gida take kowa ke fadin albarkacin bakinsa lokacin hjy ko sai faman mere baki takeyi ta juya kayan shayin da turmin zani gami da kudin dinki da aka dora sama. Shi wanan dan har yai kudin rabon kaya hakane dan tafiyan nan nasu hjy tsohuwa take tambayan gwaggo uwa dake dakin zaune lokacin. Hjy tunda kikaga hakan ai kema kinsan arziki ya budu ke nan dama haka abin Allah yake ai ga bawa duk mai rai ba agama halittansa ba sai idan ya mutu. Ni yadda naji ance babane shi yanzu a can turai din kuma wai wanan rikicin da mai sunan baba tela yayi shida mahaifinshine suka fito dashi don ance sun kashe kudi sosai ga maganan. Ke rabani da karyansu na banza shi yayan ku baida kudin anso dansa ne sai wani ya saka mashi hannu yanzu da sauri ta dago tana kallon tsohuwar tace. Wai hjy baki san halinda yaya yake ciki bane yanzu halan yayafa yanzu baida komai sheria suke tayi da wanan matar daya saka wai ta kwashe takardun kaddarorinshi tace natane . Uwa a ina kikaji wanan zancen wallahi hjy a na dai boye maki maganan ne kada ki tayar da hankalinki ni yadda najima ance wai yanzu mijin ita zahra din aike rike da gidan nasu. Baki kula ko hjy maimuna yanzu in zatazo da motar haya take shigowa ba ko inta samu wani yaje ya dauko ta duk motocinsu babusu yanzu. Shiru tsohuwar tayi tana tunane kafin tace nikan nayi wanan tunanen don ko dan kudin da yake turo min yanzu ya daina sai in yazone ya hadani da dan dubu biyu ko ukku yace inyi hakkuri. To wallahi kan hjy yayan mu ya samu kariyan arziki akan wanan auren kowa kuma ya sani ke daice ake boyewa akai sallama a dakin suka dakatar da zancen. Matan su babane sukayo gungiya sukazo yin godiya gun hjy din don a dalilinta ai aka sameni don haka itama taci ai mata godiya a lokacin don hakane sukazo part dinta din. Hjy munga abin arziki da zahra ta aiko muna wallahi mun gode ace a haifi da arzikin shi yafi a mutu abarmai gado inji uwargidan baba Ado. Sai matan baba haruna tace aike baki sani ba yaya ance zakaran da Allah ya nufa da cara ana mazuru ana shaho sai yayi caran to shine nan. Ana cewa mijjnta fakiri shegene baida asali yau gashi Allah ya azurta ta shiyasa ankace mai hakkuri yakan dafa dutse yaci. Wane irin abune zahra bata gani ba ga wanga aure nata sai gashi yau Allah ya nufa sune masu bayarwa ana godiya. Donshine Alh babba har hawaye yayi yau don ya rasa bakin da zaiyi godiya ga azumi tafe mazan mu suna cikin wani hali saiga wanga kyauta haka da rana tsaka ai dole kai hawayen godiya ga Allah. Kowa na fadin albarkacin bakinsa hjy kan shiru tayi tana tunane kafin kowa ya koma part dinsa su barta da yaranta a dakin abin duniyane ya dameta jin halin da danta ke ciki. Shiyasama bata iya tankawa kowa ba a lokacin don hakane kuma aka boye mata sai gashi gwaggo uwa yau ta fada mata kuma hakan ya tayar mata da hankali. Azumi da kwana uku aka kwatar da hjy asibiti sakamakon jin halinda danta ke ciki yanzun da tayi shine akaga zata mutu a gida aka kwasheta zuwa asibitin. Anyi sa,a Abba na gari yazo likita ya karbeta ga Abba nata kukan baida kudi lokacin duk master ya turo mashi da kudi masu yawa ummah ta kirani ta fada min halinda ake ciki don jikin nata sosaine lokacin . Muna zaune tarene muna buda baki a nan wajen master ya kira mahaifinshi ya sanar dashi yace azo da ita nan abuja ta jirgi. Abinka da hali nan danan aka shirya komai aka dauki hjy sai Abuja da yake tana da sauran kwana ta dai dan sha wahala ta mike. Tare da mama sukai tafiyan ta karamci a wurin Abban Master don wani lokaci da kansa yake zuwa ya dubasu kuma duk iyalinsa sunzo. Shi da kansa yake fada masu cewa Ahmed shine dana na farko dana fara haifa a duniya kaddarace ta rabamu a wani lokaci dashi. Duk da hakan baku dubi yanayinsaba kuka dauki yarku kuka bashi don haka nake kaunan ahalinku ga baki daya don kun min komai a rayuwata.