Sashe 34
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
data gama duban ledan tace kai dan nan har shinkafa ka sayo muna yau gidan tana mamaki Allah ne ya bamu sa, a ya nufemu da cinta a yau. Nikan na riga dana tuka tuwon masara ga miyan yakuwa dana tsunko gidan malam Tanimu nan ina muna miya dashi yanzu muci. Dan guntun murmushi ya sake a fuskanshi yana fadin ai bai baci ba Dije Allah ya kaimu gobe lafiya sai a girka a ci naman daine sai an gyara shi yau kada ya lalace. Har nama ka sayo kace yau take sallah a wurin mu ke nan yau din nan nama kan dole a gyarashi kada ya lalace kafin gobe. Tana magana tare da jawo ledan zuwa gabanta kaikai Amadi wanan ai kudi ya wahala a nan Allah yasa albarka sai ayi a hankali kada mu murkushe kudin mu koma zaune kuma. Dan murmushin gefen baki yayi daga inda yake zaune dirsha a kasa yana kallonta kafin ya mika hannunshi zuwa wajen butan dake gefenshi ruwa ya gunda a baki ya kurkure bakin kafin ya zauna da kyau ya fara alwala.. Na dawo a gajiye Rukkaiya muka fara haduwa da ita daga irin kallon data watsa min na gane akwai wata a kasa ke nan don ko dan tsayawa ko mu gaisa irin yadda muka saba a ranan bamu yishi ba a tsakanin mu. Sai ta wuce na wuce kowa yaja iska a tsakanin mu ya wuce dan uwa naga karfin halina ga yin hakan na shige part din ranan kanne na basu da lesson sun dawo gida da wuri duk suna falo. Na yaye gyalen dana yafa a kaina nan suka shiga gaidani da dawowa ina amsa masu na nufi bedroom din mahaifiyar mu don in gaida ita . Tana zaune bakin gado tana waya da hjy maryam kawar ta dake Abuja har yanzun da zama ita da mijinta da yaranta. Zan iya cewa hjy maryam ce makwaciyar da tun zuwan ummah Abuja suke tare sun koma kamar yan uwa a yadda naji suna maganan zuciyana ya bani wani abu mai muhinmanci ya faru tsakanin mama da ummah ko Abbah. Ganin hankalita naga wayan yasa nayi mata sannu ummah ya gida ta gyada min kai na juya na tafi na barta yadda na sameta zaune din hankalin ta a kan wayan. Kamar yaddana saba ina shiga na wurgar da jakkana saman gado ban daki na shiga na gyaro jikina tsab ta hanyar rage wanke matse matsina da sabulu mai kamshi tare da dan tsane jikina na da tawul na fito na kwabe kayan jikina na saka na zaman gida. Yunwa nake ji don haka na nufi falo don in samu abinda naciwa cikina lokacin abincina yana ajiye kamar kullun. Zama karamin kanin mu ya taso shima zaici nan sauran suka nufo suma macen na tura ta dauko masu spoon muka zauna tare dasu munaci a haka ummah ta fito ta samemu. Salati ta saka kafin ta nufo su tana masu fada don me ba zasu barni naci hankali kwance ba suka zauna min ga abinci ? Ummah idan inaci dasu nafi cin abincin da yawa wani kallona ke kika sani ta watsa min nayi murmushi har takai kofan fita zuwa kitchen ta juyo tana fadin. Ina kika aje key din motar taki tana tambaya take kallona taji amsan da zan bata na gyarawa kanina dake saman jikina zama nake fadin yana cikin jakata na aje. Ki kula kada wani ya dauko ko idan kin dawo ki rika ajeshi a dakina don mutanen nan sherinsu yawa gareshi tunda ban bata key din da girma da arziki ba yadda taso. Don haka ki kula sosai da tuki da kuma kanki a yanzu komai da kikeyi idon mutane yana kanki yanzu don komai ya canza yadda kuka sanshi a baya gidan nan. Abban kuma yace naje maki kunne da kikula kada samun motan nan ya canza maki rayuwan ki a yanzu kici gaba da dabi,un daya sanki dasu abaya kinayi. In sha Allahu ummah na fada a sanyaye tare da dukar da kaina kasa kafin na dago tashige ciki ta barni da kannena surutu suke min amma ban fahintar me suke fadi a lokacin. Tunda na shige dakin kwanana ban sake fitowa falon ba na kwanta iya tunane nayishi a lokacin narasa gano dalilin sauyawan gidan mu yanzu cikin dan kankanin lokacin komai ya dagule a tsakanin iyayyen kuma. Wace ta haifi mahaifin mu tana raye a duniya gidan mu baida nisa sosai da inda take don inda iyayyen mu suka fara zama da farko yanzu itace ciki zaune don kamar a family house din mu suke. Don haka ganin ba school da safe na na kwashi yan kannena mukaje gida mu gaida ita kusan duk sati haka muke zuwa gidan duk da har na fahinci ba wani sin mu takeyi sosai kamar yadda take son su Aisha ba amma ban bari wanan yayi tasiri a zuciyana ba game da ita. Da sabon motan muka fita zuwa gidan muna zuwa naga motan mama pack a kofan gidan kafin mu fito muka hangosu suna fitowa daga cikin gida ina kallon suna nuna mata motan namu. Kafin su karaso sun tsaya magana muka nufi wurin iyayyen mu maza muka fara gaidasu don suna kofan gida suna shan hantsi a lokacin. Har suka wuce bamu shiga wurin kakan tamu ba muna can muna gaisawa da mutanen arziki lokacin a cikkn gida don gidan namua babban gidane sosai. Mun fito mun samu sun tafi kai tsaye wurin kaka tamu muka nufa sallama nakeyi amma muryan tsohuwa yana tashi a cikin hausan mutanen zamfara tana fadin . Ni za a kawowa iya shege da raina ka fara nuna bambanci a tsakanin diyan ka dame ita takwaran nawa tafi yan uwanta da zai saya mata mota ya kyale sauran. Sallama na karayi cikin daga murya sai lokacin aka amsa muna muka shiga tana fadin watace mune hjy na bude labule na shiga don tun ban shiga ba na fahinci a taikace kara mama da yaranta suka kawo wurin hjy ke nan . Au jikokin gal ne haba mama wata gwaggon dake zaune tare da ita ta fada cikin bacin rai kafin ta dora da fadin haba hjy bai kamata ba hakan nan don Allah. Kamar ban fahinci me suke zancen ba na aje mata ledan da muka saba zo mata dashi a gefe nakai zaune gefenta ina fadin tsohuwa mai ran karfe kin tashi lafiya ? Har lokacin akwai sauran bacin rai a fuskanta ta amsa min kadaran kada ham tana fadin kema kin tashi lafiya yaya uwar taku ? Tana lafiya tace mu gaida dake ga wanan tace a kawo maku nan muka gaida gwaggon namu muna dan hira sama sama tsohuwar ta fuske damu. Can nace hjy akwai fura a fridge din ki ban sayaba uban naki bai aiko min da kudin saya ba tunda yanzu ya fara mikawa yara kanana kaddarorin miliyoyi suyi yadda ransu keso dashi. A, a hjy badai Abbamu ba kan idan bashi ba wane zai dinga wullakanta kudi haka ke wanan motar da kike shige yanzu bai isheki ba sai kun tursasashi ya sayo maki wani ?