Sashe 248
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A airport muka sameshi yazo taron mu aka dauke mu zuwa gidan da yake zaune akwai gajiya sosai a jikin mu lokacin don haka ba wani zumudi zuwa sai neman wurin hutawa. Gidane mai kyau a saman bene don lifter zaka hau ya kaika gidajen nasu dakuna hudu da falo kitchen sai stor don ajiya komai na bukata kuma akwai a gidan. Wanka nayi na bude jakkata na dauko kwallon tumfafiyana na dinga shaka kafin ya shigo har barci ya daukeni baiyi gigin tayar dani ba duk da yana son muci abinci amma ya kyaleni hakana don yasan lalurana. Idonshi ya sauka a kan kwallon tumfafiyan da aka labarta mashi shine abokin arkalla na a yanzu murmushi yayi ya kai hannu da niyar ya dauke kwallon a hannu na nayi zubur na mike. Subbahanallahi kin farkane kuma nace eh me zakayi dashi yace zan dauke a wurin nan ne kada ki danneshi wurin barci baki sani ba ya fada. Wanan shine lafiyata a yanzu shi nake shaka naji daidai a rayuwata shi nake dan jin saukin akan abubuwa idan na shakashi barmin shi a nan komai dare ina amfani dashi. Ba mamakin abinda nake fada ba yakeyi a lokacin kallon bani bace yake mani don yadda yaga ina magana ba sauke numfashi kamar yadda na saba maganata a tsanake don haka ya gane akwai abu a tare dani. Dan lokaci yana kallona yana kallon yadda na shaka abin a hancina ina lumshe idanuwana kafin a hankali in mayar da idanun nawa rufe na sani kuna kan zahra amma zan rokeku da kubar jikinta a nan don kadata wahala da yawa. Har in sone na Allah da Annabi kukewa mutum bai kamata tana cikin lalura ace kuma kuna jikinta zaune ba haka kuna bata wahala da shakan wanan abin . Nasan da kuna jina don naganku a jikinta saboda ba haka zahrata take ba ina rokon ku don darajan Annabi har in ku musulmai ne kuyiwa Allah da Annabinsa kubar ta haka ta samu lafiya bana son mu kai inda ba a so daku nasan son mu kukeyi kuke tare damu amma ku tuna akwai bambamci rayuwa a tsakanin mu. Mungode da kariyan da kuke bamu kuma mun sani don munsan kuna tare damu mun gode amma ku bar min matana hakana don Allah. Wani irin ajiyan zuciya na sauke duk a cikin barcin yana tsaye a kaina saye da farar jallabiya ya kura min idanu shi kadai yasan abinda yake Nazari a cikin zuciyar shi. Sannu a hankali labulen dakin ke wani dagawa kamar ana iska mai karfi a garin kana ya dan lafa har lokacin yana tsaye yana karanta addua a bakin shi. Kafin yaji komai yayi tsit ya fito ya kashe komai na gidan yazo ya kwanta zuciyarshi cike da tunanen dalilin wanan abin shi dai a saninsa tun yana yaro haka ya tashi baida tsoro. Yasha kwana wajen unguwarsu shi kadai daga wajen wasa ko hira barci zai daukeshi kowa ya shige gida a barshi wajen shi kadai don rashin gata ya kwana a nan. Haka kuma zai iya raba dare ya biyo hanya ya dawo bai haduwa da kowa a lokacin sai karnuka da akuyoyi a hanya wata rana kuma idan yan uwan kakansa yayi masu laifi kan zuwa gona din sun mayar dashi jakin gonan su a lokaci da duk wani aikin wahala shine maiyi masu suda matayensu. To haka zai gudu ya kwana cikjn garken awakai don kawai kada a ganshi a dukeshi yasha ganin abubuwa ma bambamta data mutane amma ko Dije dake kula dashi bai taba fada mata komai ba kan hakan. Dole yasan abubuwan a yanzu sune suke barazana a rayuwanshi dana matarshi in har hakane ita zahra me tayi masu suke kokarin binta haka ji yadda suka sauyata ta koma wata iri kamar dai ba zahran farko daya sani ba yar gayu. Washe gari da kyar na tashi nayi sallah asuba amma kuma ina mamaki da mamare a zuciyana na yaushe mukazo saidai na bar komai a kasan zuciyana ina wayancewa . A gurguje ya shirya yayi muna sallama akan zai tafi offoce bayan tafiyanshi ne muka samu zama da Dije da har lokacin tana dunkule wai sanyi take ji sosai ita don haka ya bata wani katon rigan sanyin daya sayo don mu saboda ya shiryawa zuwan namu. Wai mama yanzu gaskiyane ashe tafiyan zahra kuwa ni abin kallonshi nake kamar almara ana fadin fakiri fakiri muna mata dariya gashi yau fakiri ya kaita wajen da muke fatan zuwa. Ajiyan zuciya mama din dake zaune tana tunane ta sauke kafin tace gashi ko kinga gaskiyan hakan tunda kinga zahiri ai ba zuwa turaine wani abu ba Aisha. Zama wani abin shine magana yanzu ni hankalina yanzu bai tashi kamar farko don maganan da mukayi da iya bisi take fada min wasu cleaner's suke zuwa yi wasu kuma wani aikin karfi yake kaisu ke wasu har wanka gawa suke aikin yi acan da daukan gawa. To kilama shi yakaisu can din don kinga ai shi yarone mai karfi sai duk suka kwashe da dariya lokaci guda nan suka kafe da fadin ai kuwa a nan zamu fake ga duk wanda ya tambayemu sai muce masa ai wankan gawa aka daukeshi yi a can ba sunce iskanci suka iya ba. Iya bisi ta fada min cewa bisi ya fada mata basu dauki wasu ma,aikata ba a wurin su kinga ke nan ba anan inda yace yana aikin ba suke a wani wajen dai yake ke nan. Rukkaiya dake gefe tana dariya tace za ai irin na su ya musa ke nan tunda haka muke fadawa mutane cewa suna turai a da ashe suna nan cikin Africa tare damu ta fada tana dariya. Wani kallo uwar tayi mata kafin Aisha tace kefa Rukky wawuyace da yannan naki zaki kwatantasu kuma kodai ba a turai suke ba ai dai ba a Nigeria suke ba dai ko ? Sai dai idan ke kikaje kika fada wurin katobaran bakin ki yanzu uwar ta fada a dan hasale a,a wallah me zaisa in fada da ina da niyar fada aida na fada tun baya dana sani. Amma ai ummah ta sani saidai kawai tana nuna bata sani bane don ranan hjy karima ke fadi a gaban ta sai cewa tayi Allah dai ya tsaresu a duk inda suke. Kaji wata yar banzan ke nan wanan matar ta shigo gidan nan cike da ahurin ta wullakantani Allah bai yarda ba yar banza ashe macuciyar gaskece ta karshe. Wai mama shike nan yanzu Abba ya barta da dukiyan shi Aisha ta tambaya dolen shi ai tunda ta lauyeshi tayi mai wayau kuma ta nuna mashi tasan manya tana tare dasu. Shima Alh kamar kame kame yakeyi yanzu ai ni tsorona kada ace ta kwashe komai a hannunshi shinakewa tsoro wallahi tunda yaki fadawa kowa gaskiya har yanzu. A tunda kikaji bai fada ba ta kwashe din ke nan amma abin da mamaki yadda har ta iya yiwa Abba wanan dabaran ta kwashe komai duk wayau irin na Abba din. An fada maki matan birni irin kine da dabara da asiri yadda ta shiga jikinshi akaji aurensu kwatsam haka tayi mai dabara kuma ta kwashe komai ta tafi ina wanan matar zata iya zama a famile house irin wanan ai sai su mama da aka saba da hakan. Ke ni ku rabani da zancen Alh yanzu ba shine a gabana ba zancen wanan yar iskan sarkin naci shi yake damuna don inba nayi da gaske ba sai salma ta zamo min kaya a gidan nan nan gaba don alama ya nuna hakan. Ta yaya haka zai faru mama Aisha ta tambaya yaya ba zai faru ba ga zahiri kin gani kuwa ita da yarta duk abinda zanyi a kansu sai sun tsallakeshi shegiyar yarinya shiyasa take kama da uwarta kamar an tsaga kara. Mama yaya ko zakiyi nifa naga kuna son dorawa kan ku wahala a barsu mana tunda haka Allah ya nufa don zahra taje kasan waje da mijinta shine me mama zata hanamu numfashine ko me ? Shine kuwa komai ke rukky bansan irin zuciyar ki ba keda yannen ki ana fahintar daku abu baku fahinta bari kawai mama lokaci zai fahintar da ita hakan ai Aisha ta fada a hasale. Barta barta kawai yanzu ke kina son ace wanan abin ba a dakin nan yafito ba ace a cikinkune wata tafi koda muncewa mutane aikin gawa yakeyi a can ai idan wasu sun yarda ai wasu kallon mu zasuyi a yan hassada. Ga wa yan nan yannen naku narasa gane kansu kullun cikin yi min karya suke na yau daban na gobe daban dole kuga na damu haka da wanan zancen. Kowansu shiru yayi suna nazarin maganan mahaifiyar tasu saidai ita rukky da bataga wani abin damuwa ba a nan tasan dai tafi zahra gata da uwa to me zai dameta yanzu da zancen zahra can. Matsalanta daya shine mijinta da yanzu baida abinyi tunda yayyenshi suka kwace kudin da yake juyawa don sunga kudin zai salwanta shine kawai damuwanta a yanzu ita. Daga cikin dabarun master tare da tunanen shi ya samu na farko don yanzu ya dasawa mahaifinshi kaunarshi tare da shakkarsa a zuciyarsa daman haka yake son abin ya kasance kamar yadda suka shirya da malam musa. Don idan ya shiga cikinsu haka zikau daga sama ba zaiyi wani tasiri mai ma,ana ba ko agun mahaifin nasa yasa sukai ta ja masa aji tun farko yanzu ko dabaransu yayi don ya dasawa nahaifin nasa kaunarsa tare da dan shamaki a kansa don gudun kada yaki zuwa gareshi. Yasan duk abinda za ayi a yanzu mahaifin nasa ba zai shagala a kansa ba dole yana da muhinmanci a zuciyar mahaifin nasa gashi a yanzu suna waya sau uku ko biyu suna fadawa juna matsalan su. Sannu a hankali gaya yanzun wata irin shakuwa mai karfi ta shiga jikin junan su baya shaka ko nauyin kiran dan nasa a gaban kowa yauma a irin hakan yana zaune a falo da dukkan iyalansa. Wanan wata sabuwar dokace a gidan nasa nayin hakan a ranan jumma,a duk wani wanda ke rayuwa a cikin gidan dole zai fito falo ya zauna kowa na fadin bukatunsa. Dama suna hakan