← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 286

Sashe 171

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra kiyi hakkuri don Allah nasan duk nina ja maki wanan abin da yan uwanki ke maki don da ace bani kike aure a yanzu ba wani can hamshaki nasan da dole sunayi dake. Amma yanzu aurena yasa duk suna ganin ke ba kowa bace a cikinsu yanzu don ban taba zaton har hjy da girmanta zata iya fadin wanan maganan haka a gabana ba sai gashi a yau ta fada naji. Uhumm ka dauka donkane take wanan maganan wai itafa hjy haka take ga duk wani dan dakin mu duk sanda muka hadu ba a kwashewa lafiya da ita saita yaba muna magana. Ni na saba da irin wanan halin nata don ba yau ta fara nuna min hakan tun ina gaban ummah haka muke kwasa da ita dama. Amma duk da haka na yanzu yafi dukda bansan nada din ba yadda kuken sai nake ganin kamar don kina aurena a yanzu ina fakiri hakan murmushi kawai nayi ba tare da nayi magana ba shima bai sake fadin komai ba lokacin. Munkai bakin wani shago ya tsayar da mashin din yana fadin bari na dan shiga in fito ya sauka saman mashin din zuwa cikin shagon. Yadan jima ya fito dauke da ledoji guda biyu ya miko min na karba ya hau mashin din yana fadin kayan teane a ciki naga wanan sun kusa karewa kuma zan dade wanan karon ban dawo ba gashi teane abincin ki ke. Na karba har lokacin banyi magana ba don raina ya gama baci da abinda hjy tayi min a lokacin don koba komai ya kamata ta raga min tunda muna tare ai. Washegari sammako yayi yabar garin zuwa zaria don haka danayi barcina na tashi na fara gyaran dakina daduk part dina ina tsaka ga aikinne na fara jin kukan dabbobin har yana shiga raina. Gashi nayi alkawarin ba zan sake zagawa baya inda suke daure ba don na tsorace da lamarinsu sosai gaskiya don hakane na kyale ban zaga inga ko kukan me sukeyi ba. Kukan yayi yawa don haka nayi tunanen yunwa sukeji gashi da alama ba wanda ya damu da kukan nasu lokacin haka kuma nayi tunanen ina Dije take don tana da kokari dasu gaskiya. Kamar wace akaba umurnin tashi haka naga na tashi na nufi wajensu kai tsaye tun daga nisa na hangosu tsatsaye sai kuka sukeyi. Suna ganina duk suka maida hankalinsu gareni lokaci guda basu da komai na abinci wurin don hakane na dauki tsitsiyan gyaran wurin a karo na farko na fara share wurin a tsorace. Na koma part dina na debo masu ruwa don ni baya tafiya ba wadatani da ruwa ba sai ya cika min komai nawa na zuba ruwa yadda zai wadataceni zuwa wani lokaci. Na debo na dawo ina zuba masu naji muryan Dije a bayana tana fadin yauwa yar albarka yanzun nake fada da yaran banzan nan su taso su duba minsu sunki zuwa shine na lalabo nazo in duba . Tun safe ina daki kwance bana jin dadin jikin nan nawa sannu nayi mata tare da tambayanta meke damunta lokacin tace jikintane ke ciwo alaman zazzabi a jkkin nata dai. Abincinsu dake cikin buhu na jawo na zuba masu banyi aune ba saiji nayi a bayana kamar za a kasheni ashe uwar garkene daga inda take ta sako min kahonta ajiki tana dona kanta jikina. Bansan lokacin dana sake sauran abincin ba ya zube kasa na kwasa da gudu zuwa wurin Dije ina haki don na tsorata da hakan. Lah akuyan kike tsoro kuma diyar nan me akuya zatai maki kuma ta fada tana karasawa zuwa wurin dana fito ta duka tana kwashe abinda ya zube din . Aike amarya godiya take maki da hakan idan dabba taji dadi hakan takewa mutum ta shige a jikinshi shine godiyansu ai sai kuma ta koma fadin yaudai angon namu ya tafi. Allah ya tsare muna shi ya kare yanzu kan ai yayi nisa ga tafiya da yardan Allah ta fada duk hankalina nakan wanan bakar akuyan banyi aune ba naji ta saki wani irin kuka lokaci guda saida na kara kaduwa a hankali na sulale nabar wurin a tsorace da ita. Shigowan ta falon bai hanashi wayan da yakeyi din ba wanan karon bai kuma fasa fasin abinda yake magana a kai ba don ta shigo falon lokacin saici gaba da fadin da yayi. Dane na cikina shekara ashirin da bakwai zuwa takwas ke nan yanzu rabona dashi a nan cikin zamfara suke indai ba barin garin sukayi bayana kai bama inda zasu don kowa nasu yana garin. Gabatane yayi wani irin mugun faduwa lokaci guda zancen da bata taba kawowa kusa ba ke nan a ranta sai gashi taji yana waya akan hakan don haka take duk wani annurin jikinta ya gushe lokaci guda. Karfi hali tayi ta zauna har zuwa lokacin da ya gama sauraren abinda mai wayan ke fada masa a lokacin don ba jinsu takeyi ba daga inda take zaune din ba. Nagode Alh ina sauraren ka insha Allahu zan kara jira inji inda zancen ya kwana don Allah aimin kokarin hakan ina cikin wani hali kan wanan zancen a yanzu. Nan kan ta kasa hakuri ta danne zuciyarta don saida ta kalloshi a cikin wani irin razana ya kashe wayan yana dorawa saman dan karamin table din gabanshi tare da dago kai ya kalleta . Alh wani zancen naji kanayi yanzu ta fada daidai lokacin da yake kawar da kai daga kallonta lokacin hakan yasa yayi wani irin juyowa a ciki mamaki ya jefa mata wani irin kallo lokaci guda kafin yace. Meya shafeki da wayana yanzu ko dama kin zauna ki sauri abinda nake fadane wai inma son ki sani kikeyi to ina zance akan dana Ahmed mai sunan baba dana haifa da matana ta farko a zamfarane. Zubur ta mike tare da nunashi ido rufe tana fadin wana zancen ma karyane wallahi dan da ka samo a cikin duniya kabaro shi can yanzu zakace zaka daukoshi a matsayin dan cikin ka kuma ? Ohh dama haka kuka dauka shine zatonku bata hanyar sunna na haifeshi ba shine dalilin watsar dashi danayi a rayuwana kome inma zatonku ke nan ku jaye don dane na halas kamar ko wani da a cikin gidan nan shima. Kaika san wanan zancen don duniya bata sheda hakan ba gareku don haka ina da ja akan wanan zance nida yayana kan hakan ta watsa mai wani irin kallo ta nufi hanyar fita daga falon a fusace. Tsuki yaja ya bita da kallo shima ya mike a fusace ya fito daga falon ko kallon abincin data aje mai baiyi ba a lokacin driver shi na ganinsa ya taso da sauri ya bude mota suka shiga sauran motan ma suka biyosu a baya lokaci guda. Bai tsaya ko ina ba sai airport inda jirginsu zai tashi zuwa adamawa daga can zaibi motan dake jiranshi a can zuwa mambila garinsu na haihuwa. Hjy kuwa tana fita dakinta ta nufa ta figi waya tanayi da yarta a cikin kuka take labarta mata abinda ya faru tsakanin su hankali tashe. Saida yar nata ta gama saurarenta ta katseta da fadin ke kam yabi baki da wayau wallahi kin fa san da zancen nan a baya. Don me yanzu zaki nuna hakan don da daya ya shigo cikin ku yanzu me zai fiku dashi ko me zai kaiku a rayuwa yaron dama ya rayu a cikin talauci da tsiya yabi in kin kwantar da hankalin ki aisai yadda kikayi dashi dagashi har uban nasa. Dama na fada maku wanan ranan yana tafe ki shirya mashi kikace a,a keda hjy aikun gama da wanan matsalan ba zaisake wawayen yaron nasaba a rayuwanshi yanzu gashi ba aje ko ina ba ya fara wanan zancen. Don Allah Nkki ki bar wanan zancen yazu bashi bane a gabana mafita nake duba a yanzu ta fadawa yar uwanta cikin zafin rai taci gaba da fadin na kulla Nkki baki san zafin hakan ba ka hada dan uba da diyanka yafi komai muni a rayuwa. Nkki din tace ina zan sani nida da guda na taba haihuwa a duniya ai ba zansa hakan ba yanzu tunda da yan uba na samu ubanshi. Yanzun dai ki nuna masa kinyi kuskure a fili inyaso daga baya in mun gama tunane mayi wanan maganan mu nemi mafita jin hakan ya dan kwantar mata da hankalinta ta mike zuwa part din mijin nata. Bayan fitan ashi daga gidan da kamar da minti ashirin ta shiga ta samu baya ciki asalima an rufe kofan daga baya duban inda abinci yake aje tayi. Yadda aka jera mai ko cibi bai taba ba daga ciki hakana ya barshi ya tafi hakan yasata dan runtse idonta kadan tayi tana jin wani irin daci a zuciyanta kamar kafafuwanta ba zasu dauki jikinta ba lokacin. Ba komai takewa takaici ba sai irin kudin data bayar aka kashe don ketarawa cameron wurin karbo maganin datayi amfani dashi a girkin yanzu duk ya tashi a banza ke nan gareta don ko sau daya tunda ta fara amfani da maganin tana kula ko ruwan gidan ya daina sha yanzu balle abincinsu na gidan. Ya isa lafiya sai karfe hudu da rabi ya samu kiran gida yaji lafiyansu inda layin zahra din ya kira a lokacin don wayan inna yana da wuya ta dauka idan an kira layin. Daidai lokacin nayi wanka na saka dogon riga a jikina sai hula dana kafa a kaina na hada cornflake ina sha ina zaune ina tatara takarduna da nake bukata wanan zangon. Naji wayata yana ringing daga gefena nakai hannuna dauka bakon lamban kasan wajene naji tsoro da farko kamar ba zan dauka ba na danna ina fadin Assalamu Alaikum. Naji an amsa min da amsa na musulunci a lokacin hankali ya dan kwanta naji maishi na fadin ko yana magana da zahra mayanace zamfara state ? Na amsa da eh nice naso sheda mai maganan a lokacin amma na kasa gane inda na sanshi namijine kuma nasan wanan muryan a baya gaskiya. Kina magana da brother din ki BISI Abdulbasti dana nan US ko kin tuna da mai sunan ya fada cikin zolaya sai yai shiru. Aiko bai rufe baki ba na dan sake ihu tare da
Chapter 171 · 0% Book details