← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 281 OF 286

Sashe 281

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai jinan bashi ya kawo ni ba kasani nidai din da kake gudu yanzu nice na haifeka da cikina don haka ban haifarwa kowa daba a duniya. Kuka dije ta saka tana fadin shike nan aida ki fito fili Rashida kice na kwace maki da yanzu ba kizo ki fake kina zagin dan mutane ba . Lai Rashida kin nuna min ke yar dije yi hakkuri don Allah kada ki karasa saboda Allah badake inna take ba danine dana auri danta shine kiyayyan mu da inna amma ke take nufi ba. Itama inna din kuka tasa lokaci guda tana fadin umma ko kin min baki a kan wanan maganan ba zai kamani ba tunda ban ambaci sunan ki ba. Yanzu dai dada bukatanki Asma ya biya tunda kin hada wanga fadan duk kece mai wanan hadin in anyi magana kice wai ba a son inna gashi yanzu abinda kika haddasa a tsakaninsu ai. Tunda kuka fara irin zancen nan nake fadin ki bari kada innan mu ta dauka gaskiyane haka zancen yake gashi har kin zugata takak ga dauka yanzu anyi yadda kike so. Indai gidan namu kike son zuwa ai kije su inna tumba sunan nan zaune kin dai san zaman da sukayi da innan mu ai sai ki koma ki zauna ku zuba dasu. Karshe zama nayi kamar yadda ya zauna na zuba masu ido ina kallon ikon Allah har dai a karshe ita inna tace ta wuce tunda umma kin juya maganan ya koma gareki yanzu amma ni ba manufata ke nan ba. Kina farashi ki canza zance yanzu don idonki ya rufe da farko nasan ba yau kika fara fadan haka da dai kowa yasan ke kika haifi abinki ai ni kuma uwarki na tayar maki dashi tsakani da Allah har ya zama hakan da kikeyiwa. Dije don Allah ki bar fadan hakan in ma naki inna shin laifine aima nayi kokari tunda har nasan ke mahaifiyatace har nake kokarin sauke maki hakkin ki na haihuwa gareni. Nan Dije ta matsa sai naje inda kuke muka tara kudi nabi malam Auwalu ya kaini wurin ki a gaba mijinki yace sai nasan inda zan sauka shi ba zai yarda ki kawo mai dan agola gida ba. Inna maimakon ki nuna min ni dankine a lokacin budan bakinki sai cewa kikayi naje wani makarantan allo in kwana can washe gari in koma gida. Naje na kwana a cikin almajirai ban san ya akayi ba dana zo da safe kan komawata gida kikace na bari amma zan dinga bin mijin ki gona muna aiki tare. Kirikiri inna zanje in wuni a gona inyi aiki in dawo da yamma kuce abinci ya kare sai naje nayi bara garin Nufawa in samu abinda zanci. Har aka kare aikin gona mijinki yace sai na shirya in dawo gida shiya gaji da agola yana shigo masa gida haka kuka turoni cikin babban mota na dawo gida ranan nayi kuka nayi dana sanin zuwa duniya. Amma danazo gida har yau ban fadawa dije komai ba illa dai ita dijen tayi fada ganin yadda na dawo kuma na koma wani iri sai ragga amma duk da haka ban fada mata komai ba. Yaran ki kawai kika sani inna daga Aisha sai Asmau ban nuna komai ba amma yau ke da kanki kike kyashi akan matar data rikeni tsakani da Allah don Allah inna bakiji nauyi fadan hakan ga Dije ba. Banyi fushi ba da mijin ki ya mutu ya barki da yara banda komai lokacin amma haka na zauna da duk wani lalura naku har lokacin dana auri zahra tana dan taimaka min amma duk baki ganin hakan. Inna ya kike so yanzu ki fadi don Allah na tura a gyara maku gida da wurin ku da inda muke da amma yarki ta koro min masu aiki tace wai ban fada mata zan turo su ba shin inna duk wanan bai isa ba ke nan ? Sai kin biyo mu nan kin dagawa mahaifiyar ki hankali kuma kina sukanta da magana a kaina ni Dije tayi min komai wallahi don da Allah na dogara ga dije kuma na dogara don itace uwana itace ubana. Duk abinda na zama yau su biyun nan sune silar hakan don ta dalilinsu na samu komai don haka inna ki tausasa lafazin ki garesu don Allah a zauna lafiya. Gida kuma yau din nan mukayi da masu aiki zasuje su fara kafin nazo ki tabbatar da kin kwashe komai naki kin koma gidan mahaifinki kinji na fada maki don ba zan yarda inbar ki a tsakaninsu ba kina hadasu fada irin haka. Sai dai in tare zamu bar maku gidan har in kace sai Asma ta koma gidan mahaifinta ba zan yarda taje can tana gantali ba tsakiyan gida gidan dako daki baibar masu gado ba ina kake son taje. Kai nikan naga tujara ranan wurin wanan ahalin don master ya turje kan lalai sai Asmau tabar gidan nan a wanan ranan, inna zatayi magana dije tace gidansane halak malak kowa ya sani a garin nan. Don haka yana da ikon yin komai dayaso da abinsa ran innace ya baci sosai da jin kalamin mahaifiyarta data goyawa danta baya sai kawai ta mike tana fadin shike nan ai yanzu na gane umma. Har ni dai kuke son nabar gidan ke nan yau din ko dayace a yau din zamu bar gidan dagani har Asmau din basai gobe ba yayi yadda ya keso ga duniyan nan. Ta fita tana kuka ya mike zai bita dije ta daga mai hannu ya zauna kyaleta ko ina bata zuwa wanan duk burgan aikine take maka yace dawai zansa driver ya kaisu gidane tace ka barsu kadai kawai tura masu aiki suje su fara aikinsu. Inna tana fita tare suka fita da Asmau din da take tafiya tana waigen baya ko zataga yayan nasu ya fito amma har suka fice get din gidan basuga kowa ya lekosu ba. Ga kuma hadari ka,in dana,in ya game gari ko ina har an fara yayyafi a lokacin daga bayan inna Asmau tace yanzu inna yaya zamuyi ke nan ki dai bari mu karasa gidan muyi magana. Allah ya taimaka suka samu mashi sukai overload su biyu amma saida ruwa ya bugesu kafin sukai gida haka suka shiga tsamo tsamo cikin gidan. Bayan sun kwabe tufafin jikinsune har wayau din Asmau tace yanzu inna gidanwa zanje gidan mu dai kinsan su inna tumba ba zasu barni na zauna dakunan su ba. Asmau kema kin faye iya shege da tsiyan banza kinsa yaron nan yana iya bakin kokarinsa damu amma kedai kullun abinda zaki hadani dashi kike nema kiyi don kawai kinga nafi sonki dashi. Yau ga irin abinda kika ingizani nayi masa bai fadi karya ba don mahaifinku akanku ba irin abinda baiyi masa da yake raye don mashi din mai dubaiyane wallahi da wanine ba zai rike mashi kuba bayan ransa. To ai baba yai masa bamu ba duk dije take saka yai haka dama kin nuna zaki mai baki ai dole ya saitu yabi abinda kike so wani kallo tayiwa yar nata kafin tace. Yau nasan baki da hankali nayi mai baki mu lalace tare mu koma zaune duk wanan kokarin da yakeyi damu ina masa baki nima ban dagawa ai umma zatayi min baki kedai in kina binsa ki aje duk wani tsayatakun ki ki aje kibi dan uwanki a zauna lafiya shine rufin asirin mu gaba daya. Ita Aisha data bisu ake zaune lafiya kinga ya tsanane koya korota gidanshi ba gata can ta saje dasu ba an zauna lafiya kece dai bansan irin halinki ba sai kije ki dauko rigiman ki kice sai nashiga nayi maki yaki ke karama a cikinsu kice baki bin manya. Nina gaji wallahi in ba iskanci ba da tsiya irin naki ko bakin cikine meya kaiki wurin masu aiki ki koresu ai yanzu ga abinda kika jawowa kanki nan sai ki koma ki bashi hakkuri. Tace cabdi Dije na gidan da matarsa zan koma yadda dije ta tsaneni din nan ai sai tasa yayi min dan karan duka a gidan ni dai yanzu kisan yadda zaki gyara maganan don gaskiya ba zan koma gidan wanzamai ba in zauna saidai in kama dakin haya. Wai ma da gaskene dama gidan nan nasane danaji dije na fadi kullun nasane mana mahaifin mu ya bashi tun yana karami kowa kuma yasan da wanan zamcen sai ta danyi shiru tana tunane kafin can tace. Shi komaima da zamu samu duniya ya kwashe shi kadai da yaranshi shine uba mai kudi shine shine shine haba don Allah gashi kuma ke baki samu kansa kina juyashi yadda ya dace ba. Uwar ranta yana bace bata samu bakin bata amsan wanan maganan banzan da take sakewa ba a lokacin sai suka koma kowa na tunane gashi ruwa ya hana fita balle su dan fita su samu abinda zasuci ga kamshin soye soye a can gidan zuciya ya hana su tsaya suci. Kai shima baba kome yasa ya tsanesa haka har yake fadi yanzu a gaban mu uwar tace a hasale abinda yasa kika tsaneshi ke ma a yanzu hassada da bakin ciki kikewa dan uwan naki ashe ya kwashe komai . Kada ki manta shi arzikinsa gada yayi gun ubansa nice dai matsiyaciyar da banci na ubasa baci na naku uban ba sai tsiya sai kawai Asmau tasa kuka wai inna tayi mata gori ta fada mata magana a cikin zance. Mama ke zaune a falonta tayi shiru tana tunane abin duniya ya isheta ga talauci ga bakin ciki tana kallo ba yadda zatayi maganinsa sai kallo. Uban tsuki taja tana fadin makaryatan banza a fili sunci kudina kawai a banza har yau banga komai ba sai cigaba a wurinsu maganganu takeyi ita kadai a dakin don ranan ba wace tazo gidan don basu da kudin mota Aisha ta bugo zatazo intazo akwai na Napep tace wallahi ban kwana da ki kwandala ba a gidan nan jiya. Wanan yasa Aishan bata shigo ba a ranan ta zauna a dakinta sai zuwa yamma da wata kawarta ta shigo ta bata dari biyar kamar tsafi ta shirya zuwa gida din wurin mama. Suna nan zaune a tare ya musa ya shigo dubu biyu ya zaro yaba mama tana
Chapter 281 · 0% Book details