← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 286

Sashe 33

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safara da marwa ta fara yi a cikin daki lokaci guda abu ya taru ya zama biyu a kanta lokaci daya ga mamakin hjy Salma ga kuma na Abba da yanzu ya barta dashi. Meke shirin faruwa danine a yanzu mama ta tambayi kanta kafin ta wani juyo tana fadin wallahi karyan ki salma ko zan tafi ba komai a gidan nan kinyi karya ki hau kaina a gidan nan kun tabbata a bayan mu har abada keda zurian ki a gidan nan. Mama kinga har an fara min magana wai anga zarah ta faso gari yau kowa sai zancen motar ta yakeyi garin nan Aisha yar kwalisan gidan mu ta fada daga kofa. Jin hakan yasa uwar juyowa tana fuskantar diyar nata don jin abinda take fadi din ta faso gari tafi wa a cikkn ku don wanan motar data shiga shine finku da tayi ko me ? To mama su mutane suna iya ganewane sai su dauka ita wata abuce a cikin gidan nan tunda gashi har su samira na fadi a group wai da motar da ita sun zama celibirty a garin nan ko ina sai zancen ta akeyi yau. Ana tura photunan ta da motar haba dai mama saida nace kada ki bari ta shiga motar nan yanzu ga abinda hakan yaja muna kaskanci a idon jama,a da komawa baya. Aisha zaki barni naji da abinda nakeji yanzu ko sai kin kara bata min rai zaki fice yanzun nan da kika ganni nan mun gama waya da baban kune yake fada min wai shi yabada kudi aka saya mata motar ashe ba baba ya sayaba shine ya saya nasan dai baban yaje mashi da zancen . Shine tunda saida ya fara zancen dake anan kafin ya tafi shine dayaje gun abba yayi zancen da Abba din Aisha ke fadin hakan a hasale. Rukkaiyace ta turo kofan ta shigo lokacin tana fadin wai kinji yan iskan nan har kirana sukayi suna min sheri wai sun san idan zamu fasso gari tamu tafi wanan ke nan. Ina ruwan su yan sa ido da gulma ni mutane na ban mamaki ga sa ido kan abinda bai shafesu ba wanan ai tsaban gulmane da munafunci dama ai haka ake son gani a wurin mu ko yaushe. To mama meyasa Abba zai yi muna haka yasaiwa zarah din ita kadai muya ware mu bai saya muna ba gaskiya ki tambaya muna muji dalilin shi nayin hakan ? Ke Aisha ki fita min ido ki barni inji da abinda ke damuna a yanzu ko kin fini sanin abinda ya dace inyi ne kan hakan yanzu ? Ganin ta dauki waya ta fara magana da yar uwarta yasa suka fice a dakin ransu bace har lokacin suna ci gaba da zancen wai ashe Abbane ya saya ma zarah mota bama ya musa ba yadda suke zato . Don haka dolene suma Abban ya canza masu mota wanan lokacin wace tafi nawa idan yazo zasu sameshi da zancen hakan tunda basu gane kan mama ba lokacin. Bai koma gida ba sai bayan sallah isha,i lokacin hankalin Dije ya tashi don bai saba yin haka ba ya kai wani lokaci yana waje duk ritsi magariba a gida take mashi. Sai gashi yau din har yakai karfe tara saura yana waje yana shigo sukayi kicibis da Dije data yafa zani a kai zata fita neman shi suka hade da ita a kofan su mai dan guntun katanga a wurin. A,a Amadi yau lafiya haka ka tayar min da hankalina kaida uwar garke dataki ci abinci ko ruwan gidan nan taki ci tunda ta dawo gidan nan. Wai ina kashiga haka tun sallah asuba da kafita kabar gidan nan baka dawo ba har wanan lokacin haba Dije kin manta dani na mijine ? Ban fita ba saidana fada maki cewa yau asubanci zanyi naje kasuwa daga can kuma na wuce zuwa school muna fitow na bazama cikin gari ina tallata kayana gashi kuma har Allah ya taimaka an kwashe don haka wana somawa akayi indai kaiwa darene ai yanzu. Meya samu uwar garke din kuma wai ana nufin har yanzu mutumin nan bai biyo bayanta bane ko me abin ya fara daure min kai wallahi gashi kuma ban san gidan shi ba balle nabi sawun shi na mayar mashi da ita ai. Yana magana yake kaiwa duke gaban uwar garke dake kwance tana tuka kamar wace tayi kiwo mai tsayi tana hadiyewa a cikinta. Hannu ya kai ya shafa bayan ta a hankali yana magana da ita kamar da mutum dan uwanshi yake zance yace haba uwar garke ko fushi kike da mune wai ? Kiyi hakkuri muma dole yasa muka badake ga wani gashi kuma da rabon mu sake zama dake Allah ya nufa kin dawo garemu kuma kiyi hakkuri kici abinci ko ruwane kada kisamu illa a jikin ki. Kici don Allah ko kisha ruwan yana kokarin mika mata ruwa a bakinta tare da shafan bayanta a hankali tayi dan kuka lokaci guda tana mikewa tsaye ta wani girgiza jikinta lokaci guda. Zagayen shi ta farayi kamar tana sunsunan jikin shi kafin ta dan tura kafanta na gaba ta kada kwanon ruwan da ake zuba masu ruwan shansu ciki sai kuma ta dona kai a ruwan tana sha har lokacin hannun shi na saman bayanta yana shafanta a hankali. Ikon Allah yanzu uwar garke haka zaki mani kiyi fushi dani kike karban abincin hannuna saina Amadi, kinyi fushi ke nan dani ko me ? Dan murmushi Amadin yayi yana dagowa daga duken da yake yana fadin tayi fushi mana Dije tunda ke kikaba da shawaran sayar da ita. Dana bada shawaran wa yakaita kasuwa ya sayar kawai dai har dabbobi sun san kitihi yanzu baiyi magana ba ya dan tara yayin kara yaje murhun dije ya debo rushin wuta tazo ya saka masu ya dan gyara wurin . Hannayen shi ya dauraye yayin da Dije ta juya zuwa cikin dakinta bai shigo dakin kai tsaye ba saida ya kai kayan gwajon shi ya aje dakinshi kafin ya nufo wurin dije din yayi sallama ya shiga. Tana gaban fitilan kwai donsu har lokacin basu da wuta a gidan su sai hasken na makwata dake dan shigo masu kasancewan ginan su yayi kasa sosai a cikin shiya. Yayi sallama ya shiga yana fadin Dije yaya gidan ta amsa da gida lafiya Amadi ya kasuwan kace ka taba ciniki a yau din ya amsa da wallahi Dije ni har abin ya bani mamaki sosai wallahi. Na dauka ai ba zasu shiga ba sai gashi mutane na yaba min wurin zaben kaya haka masu kyau ashe sana,a dadi gareshi Dije yau din nan da farawa kinga abinda na samu yana fito mata da kudin tare da fadin ba wani riba sosai na dora sama ba. Don maishi yace min har in ina son naci riban abin kada na cika kudi da yawa a sana,a na zanfi gane kan abin da sauri gashi ko nabi shawaran shi naga alheri a cikin harkan. Ya baka shawaran kwarai sosai gara daka bi shawaran nasa Allah ya umfana muna abin baki daya, kudin ya jawo gaban shi ya kirga ya ware wasu yana fadin. Wanan Dije a sai abinci mu dinga girka abinci muma a gidan nan kamar gidan kowa sau uku yanzu a rana don Allah kada ki matse kanki da yunwa kuma Dije. Yaro ke nan banda abinka Amadi farawa da iyawa saimu zauna mu kurmushe uwar kudin a cikin mu kuma tun yanzu. A, a Dije ba zamu kurmushesu ba da yardan ubangiji Allah ne fa yai muna mafita ga hakan dama tuntuni nabi shawaran ki da ban tsaya aiki da madam kan dan kudin da take ban bai ko isa biyan kudin karatu na balle kuma muci daga ciki. Datuntuni wanan sana,an nakeyi mu huta zama a cikin kunci irin hakan ki dauka ki sayo kayan abinci ko nan cikin unguwane kafin naje kasuwa idan na samu lokaci nasayo muna . Amadi kudin nan yayi yawa ka rage don bakin mu mu kadai ko dari uku na saya muna abinda zamuci ba tare da riya ba in sha Allahu. To Dije yadda kikace din ya mayar da sauran kudin nasa cikin aljihun shi yayi shiru na dan lokaci zancen karatun yaran nan ne ya fado mai a rai lokaci guda yaja tsuki don yana ganin zasu ja mashi cikas a cikin sana,anshi kan wanan karatun nasu . Shiya rasa yadda akayi ma har ya bari sabo da shakuwa ya shiga tsakanjn shi da wani wani ma macen kuma yar mai kudi irin haka da zasu moreshi a banza. Taimakone ai taimako taimako kuma baka san inda za a rama makashi ba gashi dai shine mai taimakon nasu har yanzu dai. Washe gari kamar jiya ya fita amma bai yarda ya bar gida ba saida ya duba uwar gareke ya gyara masu wuri ya aje abinci ya dan shafa bayanta yana fadin kiyi kiwo ki koshi kinji uwar garke don Allah. Yana fita masalaci yaje yabi jam,i daga nan ya fito kasuwa ya nufa ya samu babu mutane sosai ya zabi irin kayan daya kula ana so da ake tambayan shi. Ya baro kasuwa zuwa school ya kasance jumma,a don haka daga masallaci ya shiga yawata kayan shi a cikin gari ya samu ya taba ciniki sosai a rana . Yana ganin abubuwan amfani irin su kayan miya yana dan tsunta a gari har su alaihu da shinkafa don yasan Dije ba zata sayo ba tunda ba wasu kudi masu yawa a hannunta . Wanan sayayyan da yayi sashi shawaran komawa gida da wuri ya sake biyawa kasuwa ya kara zaban kaya gredi daya samu an bude a lokacin. Daga nan yayo gida ya samu Dije a bakin murhu tana hada miya don har ta kwashe tuwon garin masara data sayo a cikin unguwa miya ya rage ta hada. Sallaman shi yasata juyawa tana amsa mashi sallaman tare da fadin yau an dawo da wuri ke nan yace to kinyi fadan dare jiya Dije. Kayan da ya dauko niki niki ya aje a gefen ta bau tsaya ba ya nufi garke ya duba yar amanan shi uwargarke tana tsaye tana kiwo ya kara mata abinci ya kara gyaran wurin. Dije
Chapter 33 · 0% Book details