← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 286

Sashe 97

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tsaye inda suka parker motan a wani dan kauye wani mutum yazo wucewa yake fadin yau tun karfe goma ai hanyar ba lafiya kunyi arziki da kuka tsaya nan din ai. Jin haka yasa driver fadin sai mu kwana a nan ke nan da safe sai mubi hanya zaifi idan mun fara ganin motoci sun fara tafiya dama wani lokaci sukanyi haka irin wurin nan saidai ba ko wani lokaci hakan ke faruwa ba. Da zakabi zance na kawai mu mike in sha Allahu ba abinda zai faru damu dattijon ya fada da sauri driver ya tareshi da fadin a,a baba kada muyi gangancin yin hakan mu dawo muna da mun sani mu dai bari ido na ganin ido mubi hanyan da safe kawai. A nan suka kwana cikin motan zaune barci rabi da rabi sai da sukai sallah asuba suka ga wata babban mota tabiyo ta wuce da kyat suka samu drivern motan ya tsaya suka tambayeshi yace hanya da sauki yanzu. Suma suka dauki hanya zuwa hawan mambila lokacin duk suna a takure don sanyin da yaiyawa a lokacin gashi babu wasu tufafi masu nauyi a jikin su da zai kare masu sanyi a lokacin. Ikon Allah Ahmed din ke kallo a lokacin don yanayin wanan wajen da bai taba zaton ko tunanen cewa akwai irin wanan yanayin ba a kasan nan. Don dubaga yanayinsu na zamfara na zafi daya fito cikin shi ga iskan zafi da rana a ko wani lokaci suna cikin hakan su a zamfara. Amma sai ga yanayin nan din ya bambanta da yanayin su kuma wai a kasa daya duk ake da wanan bambamcin yanayi din yana faman kiyasta hakan a zuciyar shi. Samari mun fara shiga yankin mambila fa daga nan da ace kasan barin da mahaifin naka ya fito kaga sai mu ajeka a daidai inda zai sadaka da gurin shi cikin sauki. Zama ya dan gyara don fahintar cewa dashi drivern ke magana a lokacin yace wallahi baba ban san ainihin garin da yafito ba na dan san cewa ance yace shi din mutumin chedewane. Zaka sha wahala koda zaka gane amma sai ka wahala sosai a gaskiya don gane mutum irin haka bai yuyuwa cikin lokaci daya haka kai tsaye dole yana son lokaci mai tsawo sosai don bincike drivern motan ke fadi. Hakane kan gaskiya na gaba motan ya amsa shima yana fadin ai irin wanan tafiyan yana son bincike sosai kafin mutum ya fito daga gida. Amma ka fito haka bakai bincike ba ka kamo hanya daga kai saikai zuwa neman mutum a irin wanan wuri haka kamata yayi kazo tare da wani ko ka bincika yadda zakayi saurin ganewa kafin kazo din. In sha Allahu ganewa zaiyi ai me tambaya baya bata tunda ya fito da niyar alheri a zuciyan shi Allah zai sadasu a cikin salama wanan tsohon na gefen Ahmed din ya fada. Allah yasa don yana da wuya a wanan zamanin ya iya ganeshi haka kai tsaye babu wani sheda da zaikaishi inda yake drivern ya kara fadi. Gaskiya yana da wuya kan ya gane haka kai tsayen nan yadda ya fito neman shi nan saidai a gwada kawai ko za,ayi sa,an hakan daya mutumin ya fada. Ina ganin aiga baba nan don yace shi a Gembo zai sauka kaga sai yai masa masauki ko wani taimako ga hakan don gaskiya idan ba haka ba kan zaka sha wuya gaskiya ga wana lamarin drivern ya fada a cikin muryan kulawa. Haka ba matsala bane idan zai iya zama dani mu dai tallakawane sosai ba wani gidan zamanine gareni ba donshi naga kamar dan masu haline ? Ta hali akeyi yanzu ya samu wurin mafaka shine abu na farko da yakamata ya farayi idan ya sauka din inji diban motan. A a fa ai kaji abinda baba ya fada daganin shi gidan masu hali yake ciwon hakane kawai ya fito dashi daga gida kaga kuwa aisai hotel irin wanan. Ba irin gidan su baba don baba yace shi tallakane baida hali kaga saukan irin wanan bakon ai matsalane wanan dayan mutumin ya fada. Ahmed din yana zaune yanajin zancen da kowansu ke fadi a lokacin har saida yaji driver na fadin kaiko dai ai sauki ake nema mashi yadda zai samu saukin lamarin ba zancen jin dadi bane a nan kaji yaro. Ahmed din yace hankalina yafi kwanci da nabi baba gidan shi tunda har ya amince da hakan saukine ai Allah ya kawo min ga hakan. Kaji gaskiyan kenan yaro ka fadi gaskiya ba karya Allah ne ya kawo saukin lamarin ya hadaka da baba a motan nan har tafiya ya hadaku inji drivern. Ya kara da fadin Allah yasa a dace kaji nasan irin abinda kakeji a zuciyan ka na zafin hakan don wasu ma na iya shegantaka su kiraka da sunan banza duk da sun san hakan ba laifin ka bane laifin iyayyen nakane ya jama hakan ? Insha Allahu zanyi iya kokarina kaji yaro ai da na kowane Allah dai yasa mu dace aganshi a cikin sauki yanzu dai muyi fatan Allah ya kaimu lafiya tsohon ya fada. Dijece tunda duku dukun safiya ta sallamawa malam Tanimu a cikin tashin hankali tana fadin malam tanimu kasan yaron nan bai taba irin tafiyan nan ba. Yaje haka ya dade ba tare da ansan inda yake ba ko yaje ni abinda nake son ku gane ke nan hankalina yaki kwanci jiya a raye na kwana ina tunanen ko wani halin yake can ciki ? Malam Tanimu ya nisa yace Dije nima lamarin ya fara dan taba zuciyana don tun jiya nakai dare a waje ina dakon ko zanga dawowan shi banga ya dawoba har na shiga gida. Bakaji ba ina fadi kuna ganin damuwata yanzu ba a wasa da lamarin batan mutum gashi ya tafi bai fadi inda zai tafi ba balle aje can din aduba ko lafiya yake ? Shike daga min hankali Tanimu Dije ta fada a cikin wani murya mai rauni yace yanzu dai barin fita zuwa bakin kasuwan su na yan hatsi in tambaya ko Allah zaisa in samo labarin shi a can. Tare suka fito cikin gidan malam Tanimu din iyalinshi na masu fatan Allah yasa a gano inda Amadi din ya shiga bayan sun fito wajene malam Tanimu din yacewa Dije ta koma gida shi zai karasa zuwa bakin kasuwa din ya binciko halinda ake ciki. Ya kama hanya ya ita kuma ta kasa shiga gidan sai kawai ta juya ta shiga dayan gidan dayafi kusa da gidan nata ta shiga taba labarta masu halinda take ciki na tashin hankali din. Suma sun nuna nasu tashin hankalin sosai a hakan sun dai dan jajanta mata sun bata baki ta danji sanyi ta koma gida tana dakon dawowan malam Tanimu din daga bakin kasuwa daya tafi. Malam tani ko a kasuwa yayi neman labari amsa daya yake samu shine rabonsu da Amadi kwana biyu ke nan amma dai yabada kudin hatsin shi ga ubangidan shi kuma an sawo mai har sun samu shiga sun zama kudi. Haka ya juyo ya dawo zuwa gida a sabule jiki ba karfi don rashin sanin inda yaron ya shiga ya samu iyalinshi a cikin jimamen maganan. Nan yake fada masu abinda ya jiyo a kasuwan tare da uwargidan shi suka dunguma zuwa gidan Dije suje su sanar mata da halinda ake ciki. Sunyi sallama sun samu Dije saman dutse da suke zama suyi alwala a sama ta zauna tayi tagumi da hannu daya tana faman tunane. Sallaman su yasa ta dagowa tana amsa masu ta gaida malam Tanimu din da dawowa gida tare da tambayan shi a gagauce da anyi sa,a ab gano inda yake din ? Girgiza kai Malam Tanimun yayi yana fadin wallahi Dije abin ya fara cin tura don kaf wurin nan nasu na zagaya babu labarin shi labari daya na samu shine yaba da kudin hatsin shi yace ba zai samu zuwa daukowa ba a ranan. Kuma har sun dauko mai suma suna dakon zuwan shine a yanzun don har sun sayar mashi dashi kudin yana hannun shugabansu na wurin da suke aiki tare. Kuka Dije ta saka masu lokaci guda tana fadin shike nan dan marayan Allah ya bata ke nan sun ingiza min keyan shi ya shiga duniya dan anga ya fara tasowa mun fara fita a cikin talauci shike nan sun kaimu sun baro. Yau in yaron nan ya bata har ya tabbata kurciya akai mashi me zan fadawa iyayyen yaron nan ni Dije sai kuma ta sake sake kuka cikkn tasshin hankali da ban tausayi. Har makwabta suka fara shigowa gidan kafin ance haka gida ya cika da mutane masu zuwa jaje labari ya fara baza gari cewa Amadi ya bata an masa kurciya ya shiga duniya. Sai gashi har an fara sakawa a median cewa ya bata abu ya fara yawo a cikin gari wa yanda suka sanshi sun shiga damu hankalinsu ya tashi a irin hakane har hanne ta gani a wayanta ta fara neman layin zahra hankali a tashi . Barci nakeyi wayan hanne ya shigo min da kyar na iya dagawa na amsa sallaman da take min din na dauka take tambayana wai naga labarin dake yawo a yanan gizo kowa ? Ban gani ba hanne na fada gabana na faduwa tace wallahi nima yanzu nagani cewa wai Ahmed ya bata ya bar gida an masa kurciya a wurin sana,an shi abokan gaba sunga ya taso sun batar dashi cikin duniya. Ahmed din na sake tambayan Hannatu din tace wallahi Zahra ashe bakiji ba shine ai yasa na kiraki yanzu in sanar dake ki san halin da ake ciki. Dan murmushi nayi nace to naga jiya munyi waya dashi da dare yace min yana Taraba state ya tafi wurin mahaifin shi kinga ko ashe ba bata yayi ba ke nan ai. Dan Allah ki bari Zahra kunyi wayafa dashi kikace nace zan maki karyane kan hakan nikan wallahi munyi waya yana hanya yake fada min. Amma kinga don Allah ki iya bakinki tunda bai fadawa kowa inda yake ba don yanzu kina furta hakan sai a canza maganan kuma ya koma wani magana na daban har Abba yazo yaji ya gane muna tare dashi har yanzu. Hakane kuma
Chapter 97 · 0% Book details