Sashe 46
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kwaso bare kabila kin kawowa yan uwa. Ita zata hada ita kuma zata dawo tana kulla sheri a cikin dangin ki don a samu abin zagi da barnan suna a garemu ni fatana kullun shine ubangiji Allah ya baki miji mai albarka mai mutunci da sanin ya kamata ba tarana arziki ko kwadayin duniya ba maamah. A, a ki natsu kiyi karatun ki don gaskiya Dale ya fada maki nan gaba dakene zan fara alfahari a cikin gidan nan shine dalilin maman ku nason dakushe rayuwan ki kota halin kaka. Ummah me nayiwa mama haka yanzu take jin haushina ba yanzu ba kawai tun haihuwan ki take jin haushin ki maamah bado komai ba kuma don kawai kin kasace yar kishiyanta da bata kauna wace tafi tsana yanzu a duniya. Ummah kin mata wani abune haka me kuwa nayi mata idan ma yine itace tayi mun tunda a gidan nan tazo ta sameni ban daki zafi da ita ba akan mijina sai itace zata dauki zafi dani daku har yakai yanzun bata kaunar taga mun rabi Alh ko kadan. Tanice ta shigo falon jiki a sanyaye tana fadin sun tafi har da hjy maimuna wai tare zasu haka ya dace dama ummah ta fada kafin tani din ta sake fadin amma hjy ta fada maki zasu tafine ? Allah dai ya tsare hanya yasa su ganshi a can din shine fatan mu yanzu mu don hakan ba karamin tashin hankali bane tunda ba a san halinda yaron ke ciki ba yanzu duk inda yake. To wai ina zashine ko ya taba zuwa arewane dama ni shi nakewa mamakin inda yaje ga hjy kuma sai wani zance takeyi a dunkule wai daman haka akeso dasu aga bayansu, towa ke son ganin bayan nasu take nufi ? Wai Amadi kasan dabbobin nan ganinka yasa suke wanan kukan haka toke Dije ba kuna wuni gida dasu ba ko wani lokaci suna ganin ki ni kuma sai wanan lokacin idan na shigo. Haba dai wani sabon abu dai suka samu hakan gashi uwargarke gabadaya tun dawowanta gidan nan sam ban gane mata abubuwa takeyi yanzu dabo dabo kamar , , , , Shiru tayi domin idon ta daya sauka kan uwargarke irin kallon mutum uwar garken kemata a take taji tsikan jikinta ya tashi lokaci guda sai gabata ya dinga faduwa. Mikewa tayi tana fadin innahu sulaimana wa innahu bissimillahi rahamanin rahim Amadi nikan nayi nan idan ka gama ka sameni a daki ta fada ta wuce sa sauri zuwa dakin nata tana sake labulen kofan da sauri. Ranan abinda bai taba faruwa ga Dije ba shine ya faru don Dije ta kwana a wahalce tana mugun mafalki da tsoro a zuciyar ta har gari ya waye kiran sallah asalatu a kunnenta tafito tayi alwala ta koma daki don sai ya kasance tana jin tsoron gidan nata a ranan. Tana jin fitowa jikan nata dafa dakin shi sai dai batayi yunkurin ta sake fitowa ba a lokacin a inda tayi sallah ne barci ya dan dauke ta bata falkaba sai da gari ya haska ko ina rana ya fara fitowa lokacin take jin motsin mutum a cikin gidan. A hankali ta mike zuwa wajen bata yarda ta fito gaba daya daga dakin ba lekowa tayi daga ciki sai ta gango Amadi ne ke faman wanke kayan sana,anshi yana shanyawa a rana. Hakan yasa ta fito tana fadin a, a yau ba bokon ne ko ka daga kafan ga zuwane yau din yana buga kayan dake hannunshi don su mike yake fadin . Akwai Dije kawai na tsayane in wanke wa yan nan kayan daga nan sai in dan fita da wa yancan dana kulle amma lafiya kika kwanta haka har wanan lokacin. Kai dai bari saita daga ido ta kalli garken dabbonin ta kuri idon uwar garke a kanta hakan yasa tace munaga rasulu Annabi sidi farin gani mazon Allah. Shiru tayi har yaje yayi shanyi ya dawo yanayin da yaga Dije din acikine ya daga mai hankali yake tambayan ta wai kuwa yau lafiya kike Dije ? Lafiyata kalau barin dan je nan makwanbta tunda kana gida na samo muna dan kamu nazo in kashe muna kunu yau a gidan mu karya dashi. Idan da saura ki gyara kawai Dije ba sai kin wahalal da kanki ba ai kayyah yau ban jin cin tuwon kunun dai nafi son insha yau tana fadin hakan ya tura hannu cikin wandon dake jikin shi yana lalubo kudi ya dauko dari biyu ya mika mata. Tace barshi akwai canjin jiya daka ban suna nan banyi komai dashi ba zan sayo dasu ta fice da sauri daga gidan yaci gaba da wankin shi. Wandunan daya dauko zai tsoma a ruwa a daidai lokacin uwar garke ta aza wani kuka dayasa ya kallota inda take din ya tsame hannun shi ya nufi wuri su yana jaye masu igiyar da suka harde dashi ya kara masu abinci da ruwa duk lokaci guda ya juya ya koma wurin wankin nasa wandon ya kara dauko wa ta sake wanan kukan nata irin na farko. Zai aje wandon hannun shi yakai daidai aljihun wandon yaji abu da dan karfi a ciki ya tura hannu a cikin wallet irin na maza mai kyau ya zaro a cikin wandon . Cikin mamaki yake kallon wallet din kuka sosai uwar garken tayi ya juya ya kalleta sai yaga ta koma ta kwanta lokaci guda hankalin shi ya mayar kan wallet din ya dauraye hannayen shi ya fara budan wallet din. Kudine a ciki irin na kasan waje da sai a photo yake ganin su sune a hannun shi ya ciro da sauri yana duba kudine masu yawa sun kai guda goma a ciki sai dan katin sheda dake da rubutun wani address din kasan waje sunan maishi da lamban wayan maishi a cikin katin. Ya karanta wana address din yafi a kirga kafin ya aje wandon a gefe daya tare da mayar da kudin yadda ya gansu ciki yaci gaba da wanke sauran kayan yana dubawa.