Sashe 57
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
taji kamar an bangajeta ra dauka wani a bayanta mai karfi yayi mata wanan bangazan . Allah ya gyara bata kai kasa ba ta juyo taga uwargarke a tsaya tana ture ruwan cikin jarkan da kai hakan bai mata ba tasa kafa kamar mutum ta ture ruwan ya zube a wurin. Da sauri Dije taja baya a firgice don sai taga kamar ba akuya bace mutum ne ai gabanta don yadda uwar garken ta nuna hasala a fil sai hakan ya ba Dije tsoro ya koma dakinta ta shige sai lekowa takeyi daga cikin dakin tun safe ta kasa fitowa ta dan rage aiyukanta na gida kamar yadda tasaba yi. Gashi kamar hadin baki yau ba wanda yayi sallama a gidan ita kadaoce a cikin gidan sai dabbobin ta dake kiwonsu inka debe uwar garke dake tsaye tun lokacin bata kwanta ba ta kurawa kofan dakin Dije din ido babu kiftawa. A daidai lokacin da Dije din ke lekawan ne a yanzu uwargarke din ke kwantawa a makwancinta komawa Dije din tayi baya ta dafe kirjinta tana sauke ajiyan zuciya. Sai kuma raji shigowan mutum gidan yana sallama da mamaki a fuskanshi yake bin gidan da kallon ganin a yadda ya fita yabar gidan haka ya dawo ya samu gida kamar tun safe Dijen bata leko wajen ba. Dijeh ya fada da karfi kuma a razane yana sauri zuwa kofan dakinta sai gata ta leko a tsorace don ta sheda shi din ta gani ko wani sukai arba da juna a hakan. Amadi kaine ashe ta fada kamar a tsorace tana kokarin yunkurawa ta mike tsaye lokacin yace wai lafiya kike kuwa Dije ? Tace balau ba kan , kadai huta a san nayi a gidan don ga baki daya duk a firgice nake yau din nan. Me ke faruwa agidan ne Dije ya sake tambayanta a gagauce, Dije ta dubeshi tace huta dai mayi maganan daga baya barin dan fita in samo muna dan wani abu inciwa cikina ta fada tana jawo tsunman gyalenta daga kofa a rataye. Tasa kai da sauri ta fice gidan ko kallon inda dabbobin suke batayi ba ta fita da sauri ya bita da kallon mamaki don yadda take jan kafanta mai mata ciwo kamar na dole takeyi lokacin da sauri. Juyawa yayi wurin dabbobin yana kallon su kafin yabi ko ina na gidan da kallo yasan duk da tsohuwar nada ciwon kafa amma idan yai irin tafiyan nan na sammako ya fita bata barin gida haka da datti saita gyara shi. Cikin dan lokaci yayi tunane kardai yawan maganan akan uwargarke da tsohuwan keyi ya zamo gaskiya fa shi bai kula ba har wani abu yazo ya samu kakar nashi saidaga baya yayi daya sani akan hakan . Bin bayan Djje din yayi wace ya samu a tsaye kofan gidan nasu kamar tana tunane Dije ya ambata daga bayan ta cikin murya mai nuna yanayi. Ta juyo a firgice taga shine ya karsso dab da inda take tsaye yana fadin Dije meye damuwan kine wai ki fada min don naga kamar a firgice kike yau a gidan. Duban bayan shi tayi kamar tana duba idan wani na biye dashi lokacin kafin taja hannun shi su taka dan nisa kadan da gidan nasu kafin tace yau uwargarke taso kasheni Amadi. Kasheki Dije tace kwarai nan ta kwashe komai yadda ya faru ta labarta mashi tare da fadin don haka dole ka sayar da akuyan nan ko mu saketa tabi gari kawai taje duk inda zata. Dan shiru yayi yana kallon tsohuwar kafin yace baki ganin in muyi hakan munyi ganganci Dije akuya nan fa ba zamun takeyi a gidan nan ba yanzun. Tana zama na amanane a wurin mu yanzu yau idan mun saida ita maishi yazo muce dashi me ke nan ta dawo mun koreta ko ta dawo mun sayar da ita ? Kiyi hakkuri kizo mu shiga gida zan san abinyi kan hakan me zakayi ta tambayeshi a dan tsorace tana kallon shi don jin me zai fada. Yace bari dai yanzu koma ciki bari na gangara na sayo maki abinda zakici kafin motan kayana ya iso nan da dan lokaci in zama busy ya fada yana kokarin wucewa. Ta jawo hannun shi ba zaka barni da wanan abin ba a gida ni kadai kai subbahanallahi ya fada kafin ya dan daga kai yana tunane a wurin na dan lokaci. Yanzun zo ki zauna ga wuri naje in dawo yanzun nan yana jan hannun ta zuwa wurin dan dutsen dake kofan gidansu a kafe inda wani lokaci suke zama ko masu tafiya su zauna asama su huta akai. Zama tayi kamar yadda yace din shi ya wuce can inda yan mata ke saida abinci ya sayo mata shimkafa da salad da miya da nama yanka hudu sai ruwa mai sanyi daya riko mata a leda lokacin tare da fantan kwalba. Ya dawo suka shiga gida tare ya kaita har dakinta ta zauna ya fito ya diban mata ruwan wanke hannu don yasan ba zata ci da cibi ba saida hannu. Saida ya tabbatar da ta fara cin abincin a galabaice ya mike ya fito sai wurin dabbobin nasu ya tsaya a gaban uwar garke daga daki inda dije take ta iya hangoshi wurin yana gyara masu wuri. Ya zubar da ruwan ya dauke roban ya wanke ya share wuri ya zuba masu abinci da ruwa duk a cikin zafin nama da alama yana saurine a lokacin. Haba uwargarke keda Dije ba hakan tsakani ku ai karki manta Dije itace farin ciki gidan nan dani daku duka baki dayan mu gidan ai Dijece gatan mu kin ture ta idan wani abu ya sameta yau duk ya samemu ke na ai. Ke kanki ina baki girman ki na babba cikin yan uwa duk wani laifi ko wani abu kece babba ke, ke dauka don haka kibar firgita min Djje don Allah ba lafiya ke ga tsohuwar ba kin sani. Haba uwar garke bai kamata haka ba tsakanin ki da Dije sai mutunci ai yanzu kibar mata abin dabo dabo tana firgita dake haka don Allah. Zaka ce da mutum dan uwanshi yake magana a lokacin yana taba uwargarke magana sai ta mike ta girgiza jikinta kafin ta dona kai a ruwan shan su tana sha . Bayan ya gama dasu ya dawo zuwa dakin dije daga kofa ya tsaya yana mata magana Dije zanje na duba na gani ko motar kayan mu ta iso na fake don nan nake son a kawo min su gida tunda banda shago a kasuwa yanzu. To kayi niyya Amadi Allah ya taimaka nima barim je gidan malam Tanimu harka dawo sai in dawo gidan ta fada tana yunkurin tashi tsaye ya dawo ya tsaya yana fadin . Dije kardai ki dauki wana zancen ki kaiwa makwabta shi suzo su fassara wanan magana da wani manufa kuma daga baya. Kinsan yadda mutane suke yanzu balle ana ganin na fara sana,an nan da kudin mutane sai su dauka ai wani hali na daban na farayi yanzu karshe ma sai a camfa gidan nan kiga anzo anki shiga daga karshe azo ana gudun gidan nan kuma. Hakane fa yanzu lokaci ya canza ai gara daka kwabeni don kan abinda nayi niyar zuwa fadamasu ke nan yanzu inda taimakon da zasuyi min su taimaka min dashi. Ba abinda zai sake faruwa in sha Allah har inma ta hurhurane Allaj zai muna maganin ta balle yanzu ina batun shigo da kayan nan kinje kin fadi hakan a take zasu camfa min ne kan kudin tsafi nake amfani dasu. Alhalin kudin mutane ne na aro na kara nake juyawa tace Amadi kudin wa ka anso yace naso maki wanan bayanin kuma sai naga baki cikin hankalin ki yanzu idan na dawo zan fada maki komai in sha Allah. Nan ya fice ya barta tana zancen zuci ita kadai a gidan har ta dan samu fitowa ta gyara gida saidai tanayi tana kallon inda dabbobin suke har taje ta sakamasu hayaki saboda sanyi a wurin garken nasu.