← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 286

Sashe 52

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labarin nan bai shafi yan jahan zamfara ba ko kadan muyi amfanine kawai da sunan gari da title din don bada labarin ba,ayi don wani ko wata daya fito a zamfara ba. Munyishine don yan zamfara dake fadin ba a labari da muna a cikin rayuwan mu sai bawa ya hade ya shanye ya dawo tankar bashi abubuwa suka faru a kanshi ba Allah yasa mu dace da rahamomin sa amin. Abinda yasa nace hakan yanzu an fita zancen ummah mu din duk da itama ana dan waiwayanta tunda ansancewa dai tana tare da Abban mu taki fita gidan shi duk irin ukuban da ake gwada bata tun farko. Don haka ake jefa mata makarun durkushewa a ko yaushe tako wani hanya don kawai tayi baki ta dandani wahalan duniya da sunan kishi. Yanzun kuma dana taso ni yarta a kaina mama ta mayar da akalan aikin ta gareni badon komai ba sai don tagana durkushe a rayuwana. Na zamo ban dago ba bankai diyanta daraja ko kima ba a idon jama,a da har za a sanda ni a cikin diyan Abban mu a gari saidai nata diyan kawai take bukatan su daga. Wanan shine abinda mama ta saka a gabanta take kuma kanyi a yanzu tun bayan sayan motar da Abba ya canza min ya zamo mama masifa abinda ya zo ya tsaya mata a zuciya yanzu, Sai ta mayar da hankalinta a kaina sosai fiye da farko da take min tsana na iya zuciya kawai yanzu tsanan bai tsaya a zuciyarta ba har fili take nuna min hakan. Wanan tafiyan Lagos da sukayi na batan Dele wanda ashe tafiyan shi yayi ranan da suka isa a ranan shi kuma ya daga zuwa Canada yabar Nigeria. Bayan sun nasu sun huta kafin mama ta dawo gida sun ziyarci bokan su na lagos din ta kuma bada sunana ai mata aiki a kaina. Bokan ya danyi dube duben shi na fara aiki ya danyi ihu yana cewa wanan tana da abin mamaki sosai a tare da ita. Jin haka nan hankalin mama ya tashi ta nemi sanin meye abin mamakin nata da har yasa boka yadan razana yana sake ihu tare da ja da baya kandan yana gyara zama. Yace wanan din ita tauraruwa ce mai witsiya ko ina tana kada jelanta kuma zai zami mata alheri idan ta kada bazan boye maki ba ita din jinin ta nada karfi da wuya wani sheri yayi saurin kaiwa a jikinta. Idan dai bayi mata gagatumin aiki an kife ta ra baya yadda abubuwan zasu zo mata ta birkice shine kawai mafita a kanta yanzu amma yarinyar nada baiwa tare da masu tsaronta. Budan bakin mama tambayanshi tayi da cewa kana nufin cewa ita din zatafi duk yayana dana haifa kome ta kafeshi da idanunta tana son jin amsar da zai bata a lokacin, gabanta sai faduwa yakeyi cikin tashin hankali. Dagowa yayi daga shi sai dan walkin fata da yayi bante dashi a jikin shi sai wani digo digo dake jikin nasa zuwa samanshi wuyan shi na rataye da farin kudi couriers irin na da can baya ga dakin da duhu sai haske kadan ake gani. Kwarya ya jawo daga gefen shi yayi saddabaru a ciki kafin ya ya fara wani irin surukulen magana makin fuskana ya fito sai fuskan akuya ya gani Orrishi ririshi ya fada yana ja baya tare da fadin kai taba yarinyar nan fa fitinane a wurin ki. Nan maman Dele hjy Rafat ke fadin koma meye ayi a dakusheta kada ta haska zamu kifeta na lokaci don yaranki su samu su haska mu saka mata bakin jini ga kowa ta rasa wanda zata raba taji sanyi. Saidai fa amma idan zata bullo duk zata dakushe hasken yaran ki ga baki daya lokaci guda saidai akwai lokaci mai tsawo gareta kafin hakan ya faru da ita idan hakan yayi maki zan maki aiki kan hakan yanzu. Ayi duk abinda za aimata ta dakushe a wurin kowa ta koma abin kyama a wuri kowa yamana ba inda zata dafa taji sanyi daga ita har uwarta ta zauna a cikin ukuba mai wahala yace angama saidai idan na hada ina son kada aikin ya wuce kwana biyu yakai jikinta . Ma,ana zakusan dabaran da kukayi kika shafa mata shi a jikinta bukatan mu dai kawai shine ya samu taba jikinta suka kalli junan su mama ta bude baki tace angama. A daidai lokscin ummah ta idar da sallah nafila hanayenta a sama tana roka muna Allah tsari daga duk wani sherin mutum ko aljan ko wani daba daga dukkan abin cutarwa ta shafa. Addu,n iyayye nada tasiri matuka don koda mukaddarine sai abin yazo a cikin sauki ga bawa matuka uwa tana tsaye a ksn danta da addua da ya waita sadaka. Bayan ta gamane ta fito zuwa kitchen tani na tuka tuwo suka gaisa ta gaida ita da aiki harta juya zata tafi take fadin Tani idan zaki tafi gida don Allah ga kudin nan ki karba ki mun sadaka ki sayi tankwa ki bawa mabukatan layin ku sadaka. Kiwa Allah ki tabbatar da kinnmun wanan sadaksn takwan don hankali bai kwanta da tafiyan mutanen nan ba sam saina dinga ji gabana yana faduwa lokaci lokaci haka kawai. In sha Allahu hjy za a saya ayi yanzun nan kuwa bari nayi sauri kada yamma yayi ban fita ba dare yayi ban samu badawa ba a yau din nan. Tani ta karbi dubu biyu ummah din ta kara miko mata wani dubu daya tace wanan kibawa yar jagoran makaho wanda mace ce ke masa jagora da sanda koda yarinyace ko babba indai har mace ce a bata. Hjy sarkinda akaiwa ya sani Allah ya tsare ya karba muna ummah ta amsa da amin tani ta juya ta koma cikin gida tani na gamawa ta yiwa ummah sallama ranan da wuri ta bar gidan namu yar kasuwa ta biya ta sayi tankwa na daidai kudin kulin dari dari tun a hanya ta fara rabawa wanda tagani da alaman bukata har zuwa gidajen shiyansu. Washegari kuma tunda safe ta taka zuwa gidan sarkin makafi ta kai masu don tasan da yaran shi mata yake yawon bara shi sai wani zubin ne zaka ganshi tare da diyanshi maza. Sai karfe tara ta shigo gidan mu ta fadawa ummah tayi duk yadda tace din lokacin ne ummah taji shakat a zuciyarta irin yadda take jin kunci a cikin ranta din nan. Hakan baisa tayi sakaci da ibadanta ba don tasan irin abin rashim imanin da akanyi don kawai kishi da rashin hankali gashi a jirace take da mama ta dawo daga lagos din tace zatayi mata magana kan case din Dele din. Sai gashi mama tadawo din munji shiru saida sabon halin da aka dawo dashi tun bayan dan rikemin hannun da tayi danaje gaishe ta ban kara ganin fuskan mama kuma a gidan mu. Haka abubuwan suke tafiya a garemu dadi da rashin dadi duk muna hakkuri muna shanye komai a cikin mu bisa jagorancin mahaifiya a garemu ummah . Wace ke hanamu yin wani abinda ba daidai ba kamar yadda yan gidan namu suke abubuwansu muna kallo komai yinsa sukeyi a gadarance don wani lokaci ko mota na parker zasu sa a kirani wai a nan suke son aje tasu motar na jayetawa. Ire iren hakand dai na nuna gadara da isa ga kowa yasa ummah kawar muna da idon mu kan komai a gidan namu yanzu muna komai cikin rashin issashen yanci muda gidan mahaifin mu din. Ya kasance weekend don haka tun dana shige dana dawo ban fito ba ina part din mu sallaman yan uwan Abban mu naji sun shigo suna gaida ummah. Hakan yasani fitowa daga daki don na gaidasu a daidai lokacin da gwaggo shafa ke fadin wai makulin wancan dayan part din naku yaya yace muzo ki dauko muna a dakin shi. Gwaggo ina kwana au mama kina ciki ashe suka fada na karaso ina gaidasu da kwana har kasa don basu girman su a matsayin iyayye a gareni suka amsa min cikin sakin fuska tare da tambayana karatu. Naji ummah tace dasu Toh key din part din nan kuma wani abin kuka samu ke nan kuma suka kwashe da dariya tare da fadin aikin sanmu ba raggaye muke ba mu. Ke zaki bamu don Allah bamu son dogon tone tone kizo ki saka muna hannu a kai kuma yanzu kima ihu suka kwashe da dariya ta mike ta shiga daki ta dauko key din part din Abba ta fita. Gwaggo sa,ade ta kalli sauran tace ai kunga haka yafi da wacan mukaje karba da yau sai mun raina kan mi gidan nan don gadara da isa da samun waje. Yanzun dai ai sai tabi wani sarkin kuma a sake sabon danmara tunda ga wata zata shigo wanan kan suna daidai da ita ai in tace ita goganyace yar kano ai ba wasa bace. Gabanane ya fadi dam lokacin guda don na fahinci Abba aure zai kara ke nan kuma abubuwan zasu taru suyi muna yawa ke nan yanzu don bamu san wace kala zai kwaso muna ba kuma. Mikewa nayi na koma ciki har suka tafi ina jin sunata raha da ummah din suna tafiya na fito ina fadin wai Abba aure zaiyi kuma ? Budan bakim ummah sai cewa tayi Allah yasa hakan shi yafi alheri Allah ya hau damu kan ko wacece ya karemu daga sherin dake cikin haka. Na amsa da amin a sanyayye shiru nayi ina tunane kafin na mike nashiga bayi don naiyi wanka daga cikin bayin ne na dinga jin murya na tashi dana saurara sai naji muryan mamane ashe. Har na fito na zauna na shirya mama nakan nakinta na fito falo na nemi abinci naci nidai banyi gigin fita ba lokacin don irin ashar din da mamake lailayowa a bakinta lokacin. Har tana fadin wai Abba da yake da irin mu a gida har uku shine yake zancen kara aure a yanzu ba zancen auren yaran shi bane a gaban shi ke nan. Ta koma fadin saime ba za a taba ganin bayanta ba dai inma anyi don ta saidai mutum ya karawa kanshi takaci ai don ita a shirye take da kowa a gidan nan.
Chapter 52 · 0% Book details