← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 286

Sashe 104

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sai kamshin turare ke tashi jikinshi saita ta zube a wurin shima ya karaso yanawa mutumin sallama dago kan da mutumin zaiyi sai yaga wani dattijo farine. Mai son kamani dashi saidai wanan ba yaro bane shi kuma babban mutum ne a yadda ya ganshi zaune din da kuma kalar shiganshi da kujeran da yake zaune a kai. Ji yayi kamar an dukeshi ya tashi daga barcin sai gashi kawai ya bude idanun shi ya ganshi kwance cikin dakin nan na gidan tsohon da suka bashi ya zauna a ciki. Duk da yanayin sanyin dake garin hakan bai hanashi zufa ba dako har rufa yayi don sanyin daya kama mai jiki kafin barcin ya daukeshi bin dakin yayi da kallo na dan lokaci kafin mafarkin da yayi din ya dawo mashi sabo a ranshi. Daki daki yake tuno da abinda ya gani a cikin mafarkin nasa hakan yasa ya mike zaune yana kokarin sako kafafuwan shi kasan gadon karan . Kukan dabbobin tsohon yake ji daga waje wanda hakan yasa hankalin shi ya dauku a lokacin ya maida hankalin shi ga sauraren su. Kuka sosai sukeyi wanda ke nuna cewa wani abu yana faruwa da dabbobin a lokacin kusan tare suka bude kofa da tsohon daya fito a gigice shima yana fadin miko min fitilan mai haske shattu. Shima Ahmed din komawa yayi ya lalubo tashi fitilan suka cice daga gidan da sauri shida tsohon lokaci guda suka nufi wurin dabbobin da sauri suna haska fitila. Tun daga nisa suka hango babban bajimin saniyar tsohon a kwance yana shure shure hankali tashi suka nufi wajen tsohon duk a rude yake yana kiran innalillahi shi kawai yake ambatowa a lokacin. Baba kuna da tumfafiya a unguwar nan Ahmed ya jefo mai wanan tabayan shima a rude lokaci guda tsohon yace akwaishi can barin kadan yace ta ina ya nuna mai ya juya da sauri zai nufi wajen. Dakata muje tare da sauran dare ayanzu babu komai baba insha Allahu ya sheka guje tsohon bai yarda ba ya biyoshi a baya gudun kar wani abu ya sameshi. Suna zuwa da addua a bakin Ahmed din yakai hannu ya karo wani reshe na tumfafiyan ya juyo da sauri suka hade da tsohon tare suka juya Ahmed din yana sauri tun a hanya ya kara wasu ganye yake murzawa a hannun shi. Tsohon yana biye dashi ya rike saura ganyen da suka fadi a hannun shi yana zuwa gaban bajimin san dake kwace ya nemi hancin saniyan ya murza mai wanan tumfafiyan a hancin shi. Ya kara kallo wani ganyen ya murza yabi fuskan saniyan dashi duka har zuwa kahon zuciyar shi tsohon dai yana tsaye yana kallon ikon Allah don shi bai taba sanin wanan ismin ba a rayuwan shi. Zuwa lokacin kuma har wasu makwabta dake jiyosu sun fito daga gidajen su sunzo inda abin yake faruwa suna mamakin hakan. Bin gadon bayan saniyan yayi yana dan murza mata sauran ganyen a hankali yayin da saniyan kuma ta rage karfin shure shuren da rakeyi da farko din da alama abin dake damunta din yana gushewa a hankali gareta lokacin sun koma gefe daya suna kallon ikon Allah. Wai mamaki lokaci guda saiga saniyan ta fara atishawa irin ta dabbobi din nan da karfi zakace murane takeyi sosai a lokacin take fitar da wanan majinan a hancinta. Suna nan wajen aka kira sallah asuba don haka aka soma watsewa don haraman sallah sai tsohon nan dashi Ahmed din aka bari wanda har lokacin yana saman saniyan dake kwance tana samun natsuwa a jikinta. Tsohon ne ya iya fadin lokacin sallah na shigewa muje muyi sallah a barwa Allah ikonshi duk da yaga sauki ga saniyan don haka Ahmed din ya mike yabi bayan tsohon suka shiga gida tare. Bayan an fito daga sallah yawanci mutane suka nufo wajen don su jajantawa tsohon abinda ya faru dashi a tsaye suka samu saniyan yana halbin iska. Kowa a wurin yana mamaki zagayawa Ahmed din yayi yana kallon dabbobin dake tsaye cirko cirko suma da abinda ke damun su a lokacin. Baba ana samun rushin garwashi yanzu a kawo ai masu hayakinai kowa dake wurin ya kallo Ahmed din da mamakin jin hausan shi na yan sokoto a cikin su. Yarona meka fada nan ya kara maimaitawa basu gane me yake fadi ba saida yace garwashin wuta a kawo mashi aiwa dabbobin hayaki dashi san nan suka gane hausan shi. Tsohon ya juya ya shiga gida shi kuma Ahmed din ya nufi wanan wajen da suka debo tumfafiya a cikin dare kamar da mutane a wurin yake fadin sallamu alaikum tumfafiya jiya na maki laifi na dibeki kina barci ku gafarceni don Allah. Kaduwa da damuwa ya sani hakan ku gafarceni dan Allah yanzun ma nazo na dab debikine don Allah ya danyi shiru na dan lokaci kafin ya kai hannunshi ya mika ya fara kakaban bawan iccen tumfafiyan daya bushe a jikin iccen nasa saida ya tara da dan yawa yace ya gode ya juya ya wuce . Dawowanshi yayi daidai da da zuwan garwashin wutan ya zuba a cikin wutan ya aje tsakiya hayakin na bugun duka dabbobin wurin. Ina sam bankai ido ga kayab mutum ba wani yayi kadan ya saka min ido ga abina bana bakin ciki ko kyashi gun abin mutum dan wanda Allah ya bani yanzun kuma za a halaka min su. Haka ba zai taba yuyuba saidai muje tare da mutum idan yace zai saka abina a idon shi don ba zan yafe zalunci ba irin haka da rana tsaka. Baban ne mai saukin Ahmed din ke fadin haka kamar ya zare sai hakkuri da ban baki mutane ke masa suna fadin yayi sa,a ai wanan karon da har saniyan ya tashi bai mutu mushe irin wancan karon ba. Ya juyo yana fadin Allah yaga abinda ya gani ya turomin yaron nan a rayuwana shiyasa alheri yake da dadi don baka san a inda za a rama makaba. Yinin ranan dai sunyishi babu dadi a unguwar don shi da dattijon sun wuni cikin garke suna kula da lafiyan dabbobin nasu ne ana faman saka masu hayaki da dumi suna ji. Wanan ya shafar da Ahmed din zancen mafalkin shi abu daya ya iya tunawa shine cewa tumfafiyan nan da zaiyi amfani dashi ya gani a mafalkin shi a daren jiya din ke nan. Jin abu na tabashi daidai wurin mafalkin nasa har yana danjin zafin wurin ya juya don yaga ko menene yai karo dashi a lokacin.
Chapter 104 · 0% Book details