Sashe 230
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masha Allahu nayi farin cikin jin wanan labarin mai dadin ji a yau din nan Amadi kasan turawa bako nan gida najeriya ba ma ? Wallahi inna ai nan gaba kadan dije sai makka zan kaiki insha Allahu dake da inna tunda ita zahra zuwan ta biyu gidan su kuma ta saba fita kasan wajen ita dama. Lah inna yaya kace arziki ya zo ke nan wayaga hjy inna ai lokacin wani fadi zai tashi ke tafi can don Allah in gaskiyane aikin kwaraine su samo mashi aiko nan cikin najeriya mana. Sallon a karasa jayeshi garemu ke nan yanzu yana nan ma tare damu yaya aka kwashe balle ya dauki matarshi sun fita aisai lokacin da muka ganshi kuma. Haba inna na dauka godiya zakiyi da murna ba wanan irin maganan ba ai a bakinki su jayeni zuwa ina su suka haifeni halan da zasu jayeni gareku. Kai nifa indai ta wanan yarinyar ne aiki zaizo ma ko wani abu ina bakin cikin hakan don gori yana nan wata rana yana jiran ka da zaran kace zaka kara aure nan gaba. Aure kuma inna ana zaune kalau ita wanan ta gidan laifin me tayi min da har zanje karin wani aurecen yanzu kuma a dai muna addua da fatan samun zuria masu albarka tare da ita. Kaji shasha wanan din da aka cunama ita halan nemanta kayi suka baka ita data kwaraice aba zasuko kalli tsayinka ba balle a baka ita din . In kanawa kanka karatun ta natsu kaiwa kanka fada kasan abinda kake ciki har kana murna wai sun baka aiki don rashin sanin ciwon kai. Kallon dije yayi irin kallon dake nuna tambaya ga mutum na kan inna daya kuwa take irin wanan maganan haka amma a fili baiyi magana ba mikewa yayi ya fice daga part din kawai. Ya zauna yayi Shiru yana tunane yaya mahaifiyanshi zata din ga yi mai hakane wai kuma itace ta haife shi ya samu alheri haka ta nuna bakin cikinta a fili. Sai gani na fito daga dakin muna waya da ummah yaji ina fada mata zancen samun aikin da brother bisi yayi mashi hanya yau sun kira suna sheda mashi ya samu aiki a wajensu. Masha Allah masha Allah kai wanan labarin da dadi yake Allah ubangiji yasa iyakar wahalan ke nan naku Allah ya kara daukaka rayuwan ku daku dana bayan ku ubangiji Allah yasa ya rike amana tare da taimakon musulmin Allah ina karbawa da Amin zanko kirashi in masa murna nace ai gashima zaune ya dawo yanzu. Tace bashi wayan har lokacin tana nuna farancikinta ga hakan ya karba tayi mai fatan alheri da dacewa da rahaman ubangiji sukai sallama kodaya miko min wayan ta kashe ko hakan yasa na dan kalleshi naga baiko bude ba balle ya diba hakan yasa na kalloshi. Hawayene naga yana zuba a idonshi da sauri nace kaiko master dai ko adduan ne bai maka ba maimakon ya ban amsa sai kara hawaye yakeyi innalillahi na ambata. Wai Master lafiya kuka haka lokaci guda dukar da kai yayi yana girgizawa kafin can ya dago ya kalloni inda nake ina zaune na kura masa ido ina kallon shi yace a cikin murya mai rauni. Ina bakin ciki da mamakine har bansan lokacin da kuka yazo min haka ba wai ace yau mutum ya samu aiki irin haka amma mahaifiyarshi ce farkon nuna bakin ciki ga hakan don wani dalili nata na daban da baida tushe just saboda kiyayya ko tsana ni ban sani ba zahra. Wai inna kake nufi dama tayi wani maganane kuma game da aikin naka yanzu na tambayeshi ina kallonshi yace yanzu naje ina fada masu azatona zatafi kowa murna. Amma inna sai cewa tayi don ku kara mallakenine a gidanku kuka samo min aiki badon komai ba aidake abin kwaraice da iyayyen ki basu daukeki sun bani ke ba . For god sake na rssa me kikayiwa inna haka raina ya baci don haka a ranan na labarta mashi komai da inna ke mun ina hadewa a gidan nasu ban kuma fadawa kowa. Tambayan farko da yai min shine kona sanarda ummah komai nace wallahi ban taba fada mata komai ba game da hakan amma aiko ban fada ba ummah mace ce zata gane hakan ko wurin maganata wata rana. Ki duba zahra yadda ummah take min fatan alheri da sakawa abin albarka amma wai ace mahaifiyata ita batayi farin ciki da lamarin ba yaya kike ganin zanji a raina don Allah. Watarana zata daina wanan wani abune can na daban amma nan gaba zata rage gaskiya mu daiyi hakkuri a gama dasu lafiya kowa da halinsa ake zama dashi dama. Yayi shiru kamar yana saurarena kafin ya nisa yace shike nan Allah yasa ta gane gaskiyan amma nina san hakan yana da wuya gaskiya ke kuma na gode da rufin asirin da kike min har kike danne zuciyan ki game da ita daba haka ba ban san ya abin zai kasance ba garemu gaskiya. Da kyar yaci abincin muka kwanta ranan baiko shiga yiwa dije saida safe ba yadda ya saba mata idan yana gari haka ya kwana yana tunanen halin uwar nasa dole dai a karshe ya hakkura barci ya daukeshi. Washe gari ko da fushi inna ta tashi ina sauri don banda niyar zuwa school ina son zuwa na diba jikin Abbane agidan mu ranan naji wayana yana ringing na dauka . Ummah ce muka gaisa daga muryanta na gane babu lafiya take fada min cewa gasu asibiti tun da asuba jikin Abban ya kiya dole sukazo asibiti dashi kuma kusan kowa na wajen ma. Jin hakan yasa na gagauta girkin na gama na zuba masu naje dashi don kazan da master ya sayo muna bacin rai ya hanna kowan mu cin kazan da dare don haka na juye amiyan gaba daya nagyara. Karfe goma da rabi na isa asibitin nida master saman yar mashin dinshi tun daga nisa nake hango yan family din mu suna sintiri a haraban nan hankalina ya kara tashi shi ya dauko kayan abincin ya biyo bayana dashi. Fuskokinsu babu dadi na karasa ina masu sallama muka gaisa sama sama yan gulma kuma duk da halinda ake ciki hakan bai hanasu muna kallon kwakwan ba a lokacin. Kofan dakin da Abba din yake ciki yana rufe yan uwa duk suna waje nan na tsaya nake tambaya gwaggo uwa yar dakin mama ta kasa ta tsare duk wanda yazo a nan suke dakatar da mutum wai ba a shiga. Muka karaso na gaidasu na tambaya yaya mai jikin suke fada min cewa da sauki na danyi shiru ina tunan shima master din ya gaidasu zuwa can dai naga shirun ba zai mun ba nace. Wai likitane ya hana shiga sai matar baba Ado tace min muma tunda mukazo ba a bari mun shiga ba amma aisu hjy dasu Aisha suna nan cikin dakin dukkansu. Gwaggo Uwa tayi saurin fadin hjy maimuna tace duk wanda yazo ko waye kada in bari ya shiga barci Alh keyi jin hakan na juyo na kalli master ina fadin mu shiga master. Yace ba an hana kowa shiga ba ban tsaya sauraren shi ba na kama kofan na murda ta bude duk suka bini da idanu lokaci guda. Suma na cikin dakin suka kallo mu nayi sallama nashigo ina gaidasu suka amsa harda hjy tsohuwa a wajen na dan matsa ina tambayan ya jikin nasa sai anty Aishace tace min da sauki yanzu kike tafe ? Eh na tsaya na karasa girki nazo dashine keko da tambaya kikekin sani ko an tsaya neman na mashin ne ko ana can ana dabara tunda ba abin hawa ke garesu ba hjy ta fada. Koma meke garemu aidai nazo na wuce zuwa wurin Abba inda mama da ummah suke saman gadon suma zaune nabi Abba din da kallo duk ya rame ya fada sosai ga farin gashi ya cika masa fuska sai ya koma min kamar ba Abba ba. Halan me kika dafo zahra zara hjy ta tambayeni nace dawisu da jimina na bata amsa ta mere bakinta tace da wanan mijin naki fakirin ai ko a makwabta baki jin kamshin su a wanan unguwar naku mai kazantar tsiya din nan. A lokacin yake sallama ya shigo da kayan abincin cikin daki yana sallama duk abinda ta fada kuma a kunnensa amma ya wayen ce yana gaidasu tare da tambayan mai jiki. A, a dama tare kuke ashe waiku ga irin masoyan birnin nan ko anyo tafiyan mata da miji din nan to yaya son ran naki ai nafiki tunda zamanin ki ko kofan gida mijinki bai yarda ya fita dake gwadawa tsara. Mai karatu kowa yasan dan hausa da fadin magana kai tsaye ta fada min na fada mata wai ashe hakan kuma laifine a wurin ta sai ta fara fadin . Ke ki fita a idona zahra don ke haka kike fadawa mutun duk kalman dayazo bakinki kai tsaye niko danayi aure ba macen da zata nuna min yatsa ban gwada mata ba. Ke har wani auren kikayi haka a jeme kike ganin kinkai kowa Allah ya gani ya hanawa jaki kaho da bamusan iya tafiyanshi ba. Maahmah kama min bakinki a wurin nan kada ki tayar da mahaifinku ummah ta fada don ganin zancen zai baci a lokacin hjy tace ki barta mara kunya ina daidai da ita ai. Yarinyar nan ina kula duk muka hadu sai wani dage kai takewa mutane kamar wani yasata zaman gidan mijinta haka ke kika mayarda kanki baya a cikin dangi ai ba wani ba. Idan na mayar ai bada wani na mayar din bako kaina na mayar hakan bake ba wai ba nace kiyi shiru ba ke baki da kunya ko maahmah ? Muryan Abba naji yana fadin wai meye hakane kafin wani yai magana Rukkaiya tayi saurin fadin Zahra ce da hjy suke musayan yawu daga zuwanta. Kingani kuntayar dashi kuma likita yace a barshi ya samu barci wai wama ya bari ana shigowane saida nacewa Uwa kada ta bar kowa ya shigo dakin nan fa. Harda ita maahmaah din naji ummah ta tambaya sai mama din tace ita daban ne da saura kodon su Rukkaiya na ciki zaune dole ke nan sai itama din ta shigo