Sashe 191
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
tsaye dakai ancinwa manufa yanzun sai dai sun koma zargin wace bataji bata gani ba kamar yadda abubuwa ke faruwa a gidan sarakan ka a yanzu da nan gaba zasu kokawa hakan. Jeka a dunkule na baka bayani da sannu kanka zai hasaka ka gane inda zancena ka yanuf dan maganganun a yanzu suna dunkule yasa hannu a aljihu yana ciro kudin don ya bawa dattijon . Ya ciro kudi masu dan yawa yana kokarin bashi ya dakatar dashi da fadin ko kusa kai ai jikanane yanzu dole in maka nayiwa banza balle irin ku kadai kula da kanka ka hada kuma da hakkuri da duniya . Allah ya aauke ka lafiya ka gaida min da ita salamatun kace ta dai dage da yawan addua kamar yadda ta saba da hakan duk da hakan sai da Ahmed din ya kasa wucewa bai basa komai ba sai ya zaro leda daga aljihun shi yace ta malam ga wanan gorone ka karba ya kalli ledan kafin ya mika hannu ya karbi ledan a hannunshi. Sukai sallama ya mike ya fita bai tsaya ko ina ba sai inda zai samu mota nan ya juyo zuwa gusau zuciyar shi cike da tunanen sarkakiyar maganan tsohon da yai mai.