Sashe 203
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban fahinci me kakeson fada min ba jabbo kana nufin duk ku nan kusan inda dana yake ko kuma mai kama dashi kuka gani kuna zaton cewa shi din danane ko haka kawai kuka kawo zancenshi tunda ina neman dana a yanzu ? Duk da rayuwan shi Alh jabbo din ya baci amma haka ya dake ya dan sake murmushu cikin takaici ya kalli abokin nasa yace. Nayi zaton zaka fadi hakan ka dauka munzo ma da tsigar yaudara ko cin amma na don muna ganin kana da kudi mu yaudare ka saidai ka tuna cewa abinda ya shafeka mun dauka ya shafemu muma. Duk da a yanzu munsan kai a wurinka ba haka bane abin yake kana ganin cewa zamu iya cuta maka mu yaudareka don kawai muci kudin ka saidai idan kayi wanan zaton a zuciyarka kayi babban kuskure dayin wanan tunanen. Don munsan dankane yasa mukaje mukayi tsaye akayi masa gata aka wankeshi daga zargin da mutanen gari suka fara mai suna kiranshi da sunan Shegene baida ubba ko yana da baida gata don baisan ubanshi ba. Wanan yasa wanan dattijon ya nememu muka tafi da motoci biya tare da sadaki da sauran abubuwan da duk ya kamata a samu a bangareka na uba muka rufawa kanmu asiri don munsan cewa dankane na cikin ka a lokacin. Sun kuma nemi sanin kai kana ina yanzu mun fada masu cewa baka kasan ne yasa mu mukazo a wanan lokacin muka wakilce ka a matsayin mu na yan uwa kuma aminai a can baya. Tunda Alh jabbo ya fara wanan bayanin ya dukar da kansa kasa bai dago ba don kunya irin na fulanin asali yana mai nadaman furcinshi na farko a garesu. Alh Jabbo din yaci gaba da bayani yana fadin wani aure na gaiya ko na rabo ya fada kan yaron a lokacin yasa mu kuma muna ji bamu tsaya yin sanya ba muka tafi a madadinka muka daura mai auren. Mun kuma boyema wanan zancen ne donshi bawan Allah nan daya bukaci muyi hakan gareka a lokacin don a wancan lokacin da abin ya faru idan ka sani a lokacin akwai matsala babba don haka muka rufe zancen a tsakanin mu. Sai yanzu daya gama shirin da yakeyi a garekane yace mu tunkare yanzu duk wani sihirin dake aiki a kanka ya kare insha Allahu shine ka ganmu a yau din nan munzo. Jin yayi shiru ga bayanin shi yasa Alh Habu din dago kai a sanyaye yana bin kowansu da kallo mai alaman wai haka akayi dama baku sanar dani ba tuntuni. Alh sai hakkuri malam musa ya fada daga inda yake zaune din yaci gaba da fadin alokacin koda mun sanar dakai wani abu fadin baida rana don mumunan abu zai iya faruwa tsakanin ku a lokacin don asiri yana aiki akanka. Amma yanzu insha Allahu komai yazo karshe da yardan ubangiji saidai fa ka kara dagewa wurin rokon Allah don har yanzu masu wanan makircin suna tare da kai. Wanan dalilin yasa nace su fadama kada ka rabu da matarka don idan kun rabu din abinda zatayi zaifi wanan da sukayi yanzu ka barta a dakin ta shine mafita koda tayi bai taba tasiri a gareku din. Tunda ya dukar da kanshi bai iya dagawa ba sai ja, jajir da idanuwan nasa sukayi don jin wanan labarin nan suka fara bashi baki tare da musalai akan kaidin dan adam a zamanin nan. Nan dai ya dago da kyar yana masu godiya kan wanan namijin kokarin da suka taka masa ba tare daya sani ba a can kasan zuciyar shi kuma yana cike da tunanen fam na yadda zai kalli dan nasa da a yanzu ya girma harda iyali gashi can ya barshi a uwar duniya shima da nasa tarin matsalan rayuwan daya fara fuskanta. Sun aje magana kan cewa zasu dunguma daga nan kafin su koma gida saboda yafi kusa suje garin wurin yaron don har lokacin akwai sauran kwankwanto a zuciyan shi dangaske din akan yaron kodai ba dan nasa bane wani sukaiwa wanan hidiman haka. Tun ina saka danuwa a raina har yakai na dan cire tun bayan wayan da mukayi dashi din yake fada min koda zasu dawo sai nan da wata daya don wasu course da sukeyi akan abinda sukajeyi din can. Na daina wahal da kaina da wani girki tunda Ahmed din bainan kafin na dawo gida nakan dan sayo abinda zanci a hanya tun bayan kwarewan da inna tayi da abincina take fadin wai ban bata da zuciya daya ba yasa hakan. Ranan bama fita ko ina don haka na tsefe kaina naje wajen kitso ban dade ba sosai na dawo don ban samu kowa a gidan kitson ba lokacin. Nan na samu sun dora girki sunayi sai faman fada inna kewa Aisha din nagaidasu na bude part dina na shiga ban dade da shigowa ba saiga Dije har kofana tana fadin . Ga dan fura da kankara ki dama ki diba min yanzu na amsoshi nan gidan mai hura ba zan iyacin wancan girkin nasu mai kazantar tsiya ba haka. Na karba da niyar damuwa a daidai wanan lokacin wani yaro ya shigo yana fadin ace idan Amadi yana gida ana masa sallama wai daga mambila. Dije dake tsaye kofan dakina ta juya tana fadin wani Amadin za a gani gida yanzu koda yana gari wanan dan ujulan da bai iya zaman gida ko yaushe yana wurin neman kudi. Yana can yau rabonsa da garin nan ai ya kai sati biyu ke nan nake gani ta fada tana bin yaron daya juya zai fita daga gidan don jin da yayi ance wanda ake nema din baya gida a lokacin. Sai kuma ta juyo tana fadin waima yaushene mijin naki yace zai dawo don Allah ya gani ban faye son tafiyan nan nasa na aje a dade ba. Yace karatune yayi yawa sai nan da wata daya kila zai dawo amma Dije sai nake ganin kamar wani dan uwansa ne yazo daga can garinsu don naji ance daga mambila mai masa sallaman yake yanxu. Mambila inane kuma hakana ta fada tana kallona cikin tsigar tambayan nace garin mahaifinsa mana Dije aikinsa sunan garin ke nan dama mambila ai. Sai naga tayi wani irin juyawa da sauri ta nufi hanyan fita suka hade da wanan yaron daya shigo da farko yana fadin wai ance idan akwai wani babban yaro yazo don Allah. Yaron ya fada da dan karfin murya daga inda yake tsaye din can naji Asma,u na fadin kai ka damemu da sallama ance bayana nan ka kuma dawo . Shige mu tafi Dije ta fada tana bin yaron a baya shikuma ya nuya ya fara tafiya daga inda Aisha take tana fisgo hijabinta dake rataye tace Dije barin ga ko waye. Ina tsaye ina tunanen kukan bakar akuyan nan na gidan data soma tunkan yaron ya shigo gidan sai ssutin hakan data kara a yanzu din. Wanda hakan yasa nasha jinin jikina a lokacin don nariga dana yarda da camfin dana sawa kaina na gane alaman faruwan wani abu daga sautin kukan akuya duk lokacin da kaji kukanta wani abu ke shirin faruwa a gidan ke nan. A hankali can kasab zuciyana na furta muji alheri ga wanan kukan da kikeyi na juya zuwa falona don in zauna in dama huran da nake kayan riko a hannuna din tunda Dije ta mika min shi. Ina kaiwa zaune salatin Dije yasa na dago da sauri saidai bankai tsaye ba naji tana fadin ikon Allah bai karewa a duniya yau ga na manzon Allah a kofan gidan nan. Inna dake daki ta fito da sauri kai babu dankwali tana fadin wani na manzon Allah kuma umma tace na manzo dai mahaifin Amadi da kika sani Rashida tsohon mijin ki shine yazo garemu da kansa inji Allah. A lokacin har nakawo tsakar gidan kamar yadda kowa ya fito don jin me Dije ke fadi a lokacin inna ko kwasa tayi kamar zata kofan gidan kome ta tuna kuma sai taja ta tsaya wuri daya. Dije ta bita da kallo tana fadin yau naga shashancin banza makin ki tura akai masu abin zama ko nan icenyan malam Tanimu sai ki fara shirme irin naki da ina zaki da zaki fita ? Umma nace dake fita zanyi haka kawai dai zan dan leka nagani ko shi dinne da gaske ko kama kika gani kace hakan amma ni nasan ba zai taba zuwa nan garemu ba shi idan yasan kunya. Zaki fara haukan naki Rashida shi Na Manzon Allah din zai bace min ne koda yake shekaru sun ja yanzu don nima dai ban ganeshi ba gaskiya saida ya fada min ko shi waye . Ke Aisha maza ku debo tabarmin nan na dakina sabbi kuje kukai masu suna waje tsatsaye wajen motan su na barsu koda yake na aika a fadawa malam Tanimu zuwansu idan yana gida. Sallama malam tanimu din ne a gagauce yana fadin Dije akawo masu wurin zama su zauna abar manyan mutane haka tsatsaye a waje suna jira jn kuma shigowa zasuyi nan ciki aisai su shigo din malam tanimu din ya fada a cikin hanzari. A,a wallahi haram ina zasu shigo muna haka cikin gida bamu dako shiri a lokacinne Aisha ta fito da manyan tabarmi a hannunta guda biyu daga dakin Djje din kamar yadda ta umurce ta dayi. Shi kuma malam Tanimu bai fita ba sai cewa yake Djje kinga ikon Allah yau na manzon Allah ne yazo garin nan wurin danshi Allah buwayi gagara musali. Ni ai ganin abin nake kamar a mafalki yau ina Amadi gori dashagube yakare gareshi yau shima da yake kamar kowa a garin nan. Juyawa nayi zuwa part dinna don tsayin baida amfani kitchen na fada na jawo manyan jug dina na ruwa set ne harda cups dinsu da tire ban taba amfani dasu ba tun zuwana gidan na shiga daurayewa . Bayan nagamane na dauko kankaran nan biyu da Dije ta kawo min in dama fura na jefa cikin ko wani na koma daki na dauko kwalayen drinks irin wanda master kan sawo min din nan na aje don baki guda uku duk mm a jera a cikin ture din. Sanan na fito na kwalawa Aisha kira