Sashe 227
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
biye dakai masu karfi donsu ke hana jifan ya sameka yadda suke so. Duk yana wanan bayanin ne yana kulla magani a cikin wani jakkar fatan dabban daji daya fito dashi daga cikin gidan nasa wanda babu komai a ciki sai tarin magani irin na gargajiya kala kala a cikin jakkar fatan. Idan kayi amfani da wanan daga ranan su kansu zasusan komai ya kare garesu don abin zai koma garesu ga baki daya duk yadda sukaso samun ka ba zasu taba cinma ba da yardan ubangiji. Saidai kaidin kada ka yarda kaiwa wani sheri koda ta zuciyane don wanan maganin da zan baka bana rama mugunta bane ga maishi saidai ka barwa Allah ikonshi kawai akan mutum. Wanan mutumin ne ya kawo nono a cikon kwarya sabon tatsa ya karba yana mai godiya ya nan ya bude ya barbada wani garin magani ya rike kwaryan yana wasu maganganu kafin ya mikowa Amadin yana fadin duka zaka shanye yanzun nan ka bani kwaryan . Amadin ya karba da bissimillah a zuciyar shi kafin yakai a bakinshi ya kurba ya fara zuka yana jin dumin nonon saidai sam maganin baida daci ko bauri haka ya sha ba tare da yaji komai alokacin ba. Ya mikawa tsohon kwaryan ya karkadeshi ya kara miko mashi ya jawo kullin da yayi yanawa wanan mutumin bayani kadin ya mike ya karbi kwaryan yayi tako kamar biyar daga inda suke ya tarwatse wanan kwaryan ya bi kasa a ruguje don ba karamin bugashi a kasan yayi ba lokaci daya ya tarwarse a wajen. Humm mai karatu kowaye ba asiri a duniya bata sameshi bane wallahi kedai kawai kara rike Allah don shine mai jin kan bayinsa dakuma tsare bawa daga duk wani sheri. A daidai lokacin Amadin yaji kamar wani abu ya fita a kanshi yabi ta kunnuwan shi ya fita har yana jin tashin abin sama sai kuma ga guwaguwa ta hade a wurin ta nausa tayi yamma da inda suke zaune din. Kuna da Tumfafiya a gida ko yaji mutumin ya tambayeshi wanda ke masa fassara din sai kuma tsohon yace akwaita kuma ya tsare dokokinta sosai bashi ba har matan shi tasan fa,idan wanan iccen yanzu itama. Itama kusan laluran ku daya da ita saidai dan bambamcin kadan ne don ita nasu kawai suga rashin cigabansune kuma a zatonsu sun gani din don haka sun fita zancen saidai hassada da bakin ciki da zai biyo baya nan gaba kadan. Karbi wanan ka kai mata zata sha wanan din a cikin dare yayin da kafa ya dauke wanan kuma sai ta turara kada tai magana da kowa sai da safe har kwana uku. Shi wanan din wanan tsohuwar akuyan ta gidan ku mai bidilwan nan igiyan daureta zaka zuba akara dakawa duk wani mugu idan kunyi amfani dashi zaiji tsoron tunkaranka a lokacin Haka kuma matarka itama ta dage kuna da kokarin addua sosai kuna kula da addinin ku shiyasa basu taba nasara akanku kai mata wanan din. Idan tayi zata sha mamaki bani ba kadai har yan uwata da mahaifiyan mu yabawa wani magani akawo muna shi kuma Amadin aka dafashi sosai karfe biyun rana suka dawo kasuwan kamar yadda tsohon ya fada hakan suka sama ana lodin kayan da suka saya sai kuma abin mamaki kayan Amadi din ya fi yawa a cikin kayan sai abin ya daure masa kai sosai. Duk da tun cikin motan kanshi ya fara daurewa na farko dai abokan tafiyan nasa da suka fara nuna mai hassada da zargi a fili saidai wanan sirin shine don haka bai kulasu ba. Sai kuma jikinshi da yake ji kamar ba nasa ba lokacin guda kasala ya rufeshi nan ya fara zagin kansa da yarda da wanan tsohon basaraken da bai taba sani ba duk daya kawo masa Allah kusa. A dadafe ya iso gida saidai ya samu a hakanan da yake ya wakilta wanda zai loda masa kayansa a store dinsu shi kuma ya hau mashin zuwa gida. Ina tsaka da gyaran daki don ranan ya kasance asabar sai ganin shi nayi ya fado mkn dakin daga yanayin yadda yake magana na gane ba lafiya gareshi lokacin. Gaisawa mukayi kawai naga ya shige uwardaka na dauka bandaki ya shiga a lokacin don haka ban matsa sai na shiga dakin ba sai kawai naci gaba da aikina. Kayan dana wanke naje in kai dakin sai ganin mutum ya lulube da bargo yana rawan sanyi nan na rafka salati na nufi wajen shi da sauri ina tambayan shi bai iya nan amsa ba. Ganin haka yasa na fita da sauri zuwa kiran mutanen gida da nake jiyo dariyan su a lokacin ina fada masu abinda ke varies hankali tashe. Gaba dayansu suka taso zuwa dakin don su ganewa idon su abindake faruwa dashi yana kwance yarda na barshi Dijece ke kwala mai kira da Amadi lafiya ka dawo haka ? Da kyat ya iya budan baki yana fadin banda lafiyane dije sai yayi shiru kowa ido ya zuba mai kafin inna ta kawar da kallon ta ga dan nata tana bin uwar dakin nawa da kallo kamar tana neman wani abu a cikin dakin lokacin. Kasha maganine na fada hannu ya dago yai min alaman a,a can nace ko asibiti zamune haba dai kudai baku raina zancen asibiti daga ciwo kadan kuce aje asibiti. Watakila fa gajiyan tafiyane ya kamashi tunda ba yau ai ya fara tafiya irin haka ba inna din ke duk wanan maganan lokacin. Kafin kuma tace dani daya dawo din nan kodai kin bashi wani abu yacine hakan ya sameshi yanzu lokaci guds naji wani irin bazatan tambayan da tayi min din. Nace idan na bashi mike nan hakan ke nufi inna ke nan inason kasheshi ke nan kome ai da zan kasheshi da ban aureshi na zauna dashi ba har wanan lokacin. Hannu ya daga alaman ya isa hakana don Allah ganin hakan da yayi yasa nayi shiru ina mai zuba masa idanu ina kallon yadda yake fama a saman gadon lokacin. Dijece tace su fita su barshi iya abinda ta iya fada kawai ke nan a lokacin ta bar jikan nata cikin wani yanayi gidan malam tanimu ta nufa bayan taga fitan kowa daga part din namu tajawo kofan ta rufe.