← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 267 OF 286

Sashe 267

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tace gidan wani abokinsa ya sauka. Alwala tayi don magariba daya gabato a lokacin ta shiga daki ke nan don tayi sallah taji muryan inna tare da Asmau data daukowa inna kaya tana fadin wai wanan kamshin fa haka Aisha ? Sai da ta idar ta fito tana masu sannu da dawowa Asamau ke sake fadin Aisha ina kika samo wanan turare mai mugun kamshi dadi hakane walle daji turaren manyane wanan kam. Tace turare ni ban saka turare ba ai wallahi gidan ga tun shigowan mutum daga kofa kamshi zai tareka balle inka karaso cikin gidan. Tace kodai kamshin turaren yaya ne kikaji har yanzu bai fita ba tace yaya wani yaya kuma yaya da bai gari shekara nawa yayan mu da bai nan. Kafin tayi magana inna tace koda yake nan ma wani turare yaka sakawa shi banda shirmen ki yayan mu fa nace inna yazo yau yana garin nan bai dade da fita gidan nan ba don yazo bai sameki ba yace zai tafi saida safe ya dawo. Cikin dafe kirji inna din tace shin dan Dije kinkace yazo garin nan wai da gaskiya ko wasa kikai sai Aisha din race inna na taba irin wasan gana ? Ya taho shin to ina kikace mashi na tafi sai yarinyar tace kauye mana wurin tallan kayan ki na mata shi kuma yace tunda baki nan bari yai tahiya nai sai gobe zai dawowa. Dan dije ya taho shina bai sanarwa kowa da zuwan shi ba yanzu ina ya sauka nima walle inna ban tambayeshi ba inna baki ga yadda ya koma ba don ko ganeshi banyi ba murya nai dai nagane shina. Ashe yau muyi barcin mu hankali kwance tunda kudi sun taho Asmau ke fadi cikin jin dadi tace ai ya tambayeni keya nice mai kin hita. Bada mata tai ya taho ba ke nan ko balle umma shike nan su umma su suyi zaman turai bata dawowa wasu kuma su tai ? Gaskiya da gani shi kadaina ya taho yace ma wai asibiti yayi daga nan zaitai ya dubu mahaifin mata tai dake kwance asibitin. Ikon Allah yanzu da ya tsaya har in dawo gwama yatai dubiyan uban mata tai ko yaushe rabonai damu muganeshi sallon dan abinda ya taho dashi ya tai can ya zazage masu suwa. Aikema kinsan karamin aikinai na yanzu kam inna ai sai abinda munka samu garai, don walle sai ya basuwa dama yayi balle yanzu da aka gani nai mai kudina shiya. Uwar tayi shiru tana nazarin zancen Asmau din kafin tace ni indama zatai ya kwana kodai zaitai asibitin ne ya dubuso ya dawo nan ke ku tashi ku shere mai ko inda zai kwantana kafin ya dawo. A a inna ina zaya kwanta koke mata babu komai a dakin nasune yanzu barshi inma ya dawo din ai zai gani da idonai basu bar mashi komai a dakin ba sai yasan dabara da zaiyi. Balle yace min sai da safe zai dawowa ina yaka iya kwana cikin gidan ga yanzu baki ganai bane fa inna ya zama dan binni wayaye ko tufafin jikinai abin kallo na. Shikan daga asibiti can ma sunce basu ganeshi ba don ya samu su baba Adone kawai da ummah tare da Abba din don ummah ta tafi yin sallah don haka basu shedashi ba. Jikin na Abban mu da dan dama saidai ya rame sosai duk jikin nan nasa ya zube ga farin geme dana kai daya dan tara yanzu alaman wahala da tsufa dakuma ciwo a tare dashi. Ya dan dade akan Abba din wanda yai karfin halin tashi a lokacin suna gaisawa yana tambayanshi mu yace muna gida yanzun nan muka iso shine yace shi bari ya fara zuwa ya dubashi kafin mu natsa mu yace su dai huta zuwa safe in Allah ya kaimu ai sai su shigo. Lokacin ne ummah ta shigo ta samesu take mashi sannu da zuwa ya tsuguna har kasa ya gaida ita kamar yadda ya gaida sauran ya tambayeta ya mai jiki da kanne na. Sun dan jima a nan har yake tambayan ta kome Abba din keci yanzu tace to sun dai ce sugar ya shiga ciji yanzu ba komai yake ci ba sai abinda akayi da wake ko accha yake dan ci. Ummah aida an fada muna daga can sai mu sayo abincin irin masu laluran azo dashi amma yanzu bari shehu mu fita mu zaga manyan shaguna ko za a samu wani abu na daban sai a sayo ya dan canza launin abincin in babu zanyi waya da Abbana zuwa gobe sai a kawo muna. Na duba likitan inji kome ke nan ance ya fita zuwa gida sai dai zuwa safe mu ganshi sai asan abinyi don ina son mu wuce gaba dashi a kaishi kasan waje. Allahu akbar baba Ado ya fada daga bayansu don yana jin maganan da sukeyi din yace ance in baka mutu ba ba a gama halittanka ba yau yaron nan shine zai dauki dawai niyar Alh haka ? Gaskiya hakkuri bai bar komai ba don wanga abu wani babban isharace Allah ke nuna muna haka dan mutum dan baiwane ba abin raina bane idan ka ganshi ganin farko don baka san baiwan da Allah yayi mai ba gaba. Baba haruna yace ai kaji tsoron Allah in ya tashi nuna ikonsa a inda yaso kai dai kawai ka rike Allah da mazonsa ka dauki kowa da zuciya daya. Daga can gefen su Abba din suke wanan maganan shidai master yayi masu sallama akan zaije ya dawo suka fita bai dade ba kuwa suka dawo da abubuwa da Abban zai danci ya canza bakinsa akan waken da ake ta dankara masa a yanzu. Sun dan jima har yake tambayan mama da bai gani a wurin ba aka ce masa tana gida tunda rana ta koma mi zata tsaya yi yanzu tunda ba wani abinda zatawa handama baba haruna ya fada a dan hasale. Ko daya dawo gida karfe sha daya da rabi na dare lokacin duk su dije da yaran sunyi barci nice a zaune muna hira da hannatu fa charting ya shigo. Sannu da zuwa nayi mai ina mai tambayan jikin Abba din ya amsa yana fadin ashe baki barci ba nace wanan mai surutun ce hannatu muke charting da ita. Ya kwabe kayan jikinsa ya shiga bandaki ba tare daya ban amsa ba ruwa ya watsa a jikinsa ya fito yana goge jiki duk ina zaune yace gaskiya Abba yaji jiki sosai amma yanzu da sauki sosai . Don da kansa ya mike zaune amma ummah ta fada min cewa da sai an kwantar an tayar dashi amma a dan kwanakin nan gaskiya sunga sauki. Wani iri naji a raina nayi shiru ina tunanw kafin na nisa a hankali nace Allah dai ya bashi lafiya yasa hakan kaffarane gaskiya Abba ya bautu da ciwon nan a jikinsa don tun kan mu tafi fa yake dan fama a tsatsaye. Har yanzu yakai ga kayar dashi ina dai tsoron kada ya zama sai kuma nayi shiru don banson ma in furta wani abu amma duk da hakan saida ya gane menaso fada. Naji yace inda ciwo ko ba ciwo lokacin mutum yayi dole a tafi fatan mu dai mu cika da kyau da imanin ubangijin mu a zuciyar mu na amsa da Amin ya saka riga ya dawo bakin gadon ya zauna ya dan kalleni har lokacin ina cikin tunane yace. Shiyasa nace barin fara zuwa na dubashi shima Abban da kansa fa yace na barku har gobe kwazo ku dubashi akwai gajiya a jkkin ku kuma kinga ba ke kadai bace yanzu. Don haka ki cire duk wani damuwa insha Allahu da alaman sauki sosai a tare dashi don duk alaman sauki ya dan fara baiyana a jjkin nasa. Nama je gidan su inna daga can jin hakan yasa na dago kai na kalleshi kafin in tambaya yaya suke yace saida babu kowa a gidan sai Aisha kawai na sama itama ta dawo ke nan daga school lokacin. Inna kuma wai ta tafi kauye wurin talla bata gidan ma har yamman nan nace talla kuma yace talla mana shiyasa don in kamata ai ban fadawa kowansu zuwab mu ba gashi ko nagani da idona. For god sake zahra me inna ke nema a duniyan nan wanda ban mata ba ace wai sai inna ta fita yawon talla don Allah ?
Chapter 267 · 0% Book details