Sashe 215
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ya yaye bargon daya rufa dashi yana kallon katon agogon bangon dake manne a bangon dakin mai hoton masalacin ka,aba a jikinshi. Uku da rabi na rana lokacin ya nuna masa abinda yasashi yin motsi ke nan yana zabura don lokacin sallah da yake ganin ya shige mai a lokacin. Motsa jikinshi dayayine yasa ya tuna zazzabin daya rufeshi tun a hanyan shigowa su Nigeria wurin dawowa daga tafiyan da sukayi hakan kuma yasashi kokarin tuno da abubuwan dasuka faru dashi din wayen wan garin ranan. Tabassa wani abin aljabi da ba zai iya fada ba ya faru dashi tun bayan shan maganin nan da tsohon nan daya hadu dashi a garin mutane da sukaje ya bashi don watau irin nasa kuma ya yarda yasha alhalin bai taba sanin wana mutumin ba a rayuwanshi. Ka tashi ya jikin naka muryan na ya katse mashi tunanen daya fara a lokacin jin hakan yasa ya gane bashi kadai bane a dakin ba lokacin sai yayi kokarin kallo inda yake jin muryan. Zaune nake saman sallayan dana idar da sallah ina kallon shi da tasbaha baka a hannuna ganin ya kalloni ne yasa na kara mashi sannu ina tambayanshi karfin jikin nasa tare da kokarin mikewa a inda nake zaune din. Na nufoshi ina fadin yanzu Dije ta tafi itama tun dazun ai tana nan ta sakaka a gaba yau maigida ba lafiya hankalin uwar gida ya tashi ainun sai yanzu data duba taga kayi zufa shine ta tafi ta dauko abin fitara ta dawo ta dauka zafi kakeji nasan. Dan murmushi ya sake kafin ya sauke kallonshi kan tasbahan da nake ja din yana lumshe idanuwan shi a hankali cikin hakan ne kuma yake fadin. Sallah nake son in sauka inyi zahra kuma banjin kamar kafata zata daukeni gaskiya don jin jikin nan nakeyi kamar banawa ya fada a dan marairaice cikin nuna har lokacin yana jin jikin nasa. Ina zuwa na fada na dora tasbahan saman gado na juya zuwa bandakin na kara tsabtace kafin na fito ina fadin muje na taimaka maka ka samu kayi alwalan a bandaki. Da taimakona na samu ya shiga bandakin ruwan dumi na tanadar masa yayi alwalan dasu na sake kamashi ya fito muka dawo dakin yayi sallah kafin ya idar naje na hado masa tea mai kauri na kawo mashi da kyat na samu yasha rabin kofin ya koma ya kwanta a kasa yai shiru. To ashe ya falka ina can na tsaya fada da yar banzan nan naje na samu tasha min rake a kofana taki kwashewa dole na tsaya na share na rufo kofan . Ganin tana magana hankalina yana kanshi yasa tace Amadi yayane wai kodai na fita in sake dubo malam Tanimu din ne hannu ya dago mata alaman a,a. Tace to ka zauna haka da ciwo a gida ba a san meke damunka ba nifa hankalina ya soma dagawa tunda ba wanda yasan garin daka fito hakan ma ? Yayi sallah yanzun daya tashi shine ya koma nan ya kwanta naga kamar ya rage jin sanyin da yake ji yanzu karfin jikin ne baiji ko yunwa zai iya haifar mai da kasala. Amma na hada masa shayi yasha shine ya kwanta a nan din sannu kedai yar albarka kinyi dabaran yin hakan gaskiya ko zai iya cin abinci sai a fita ayo cefanai ki dafa masa. Muna da abincin dana dafa dazun da safe ba wanda yaci a cikin mu aiko kema ki diba kici ku taru bakuci komai bane kuma harki fadi kema saboda yunwa ba mai kama wani kuma ? Zanci ai na fada jin hakan yasa ya kallo inda nake yana fadin zahra jekici abincin kada yunwa ya tayar maki da ulcer kuma mana ai naji sauki nace maki ba ciwon komai nakeyi ba sai gajiya da dajin da muka shiga ya jawo min hakan. Baka dai kara shiga irin wanan dajin gaskiya ka tsaya a cikin gari ka nemi kudinka duk abinda muka samu ya wadatar amma irin wanan wahalan haka meye ranan sa . Insha Allahu wahalan ya kusa karewama gareshi mu dai matsa da addua Allah yasa muji alheri nan da yan kwanaki duk inna na tsaye muke wanan maganan. Sai naji tace daga inda take tsaye din tana sauraren mu wani abin zai samu halan da kike fadan hakan ko wani dan uwankine zai samo mashi aikin yi tunda yaki ubansa ya tsaya yana hangen arzikin uban wasu da bai ishesu ba suma har kika fara fadin hakan. Ai inna ko wani da da sunan ubanshi yake amsawa in kin debe marasa godiyan Allah dake canzawa kansu suna zuwa sunan wani amma aishi master nan yafimu sanin abinda yake shiryawa akan mahaifinsa lokacin hakane kawai baiyi ba. To abinda aka kitsa mashi ke nan ashe to yajiera lokacin har zuwa lokacin da mahaifin nasa zai sake fushi ya juya mashi baya indai wanan bakin fulatinin uban nakune dan lokaci yake baku kawai yanzu. Wai yanzu meya kawo wanan zancen ana zancen lafiyan bawan Allah nan ni nakan rasa irin hankali naki Rashida a hakan kike fatan shiga cikin manya ki zauna hankali bai isheki ba ? Dawa niyi ina son shiga manya ni umma kinkan fara irin maganganun ki ke nan koma nace ina son komawa gidan na manzon Allah ai ba wani abin kunya bane garenu yanzu tunda kowa yasan irin rabuwan da mukayi dashi a baya. Dadin abin dai banu na kashe maki auren ba lokacin don ko wa yanda suka kashe maki auren yanzu naga baki ganin laifinsu sunema abokan shawaranki a yanzu don kunga abin duniya suna sonci ta dalilin ku yanzu ko. Haka kuma uban wasu din da kike fadi ai yayi muna komai wanda ya dauki danshi yaba naka ba don komai ba aiya gama maka komai inga tunane. Don haka nake zama a wurina don nasan danazo nayi magana nice mai laifin don ita gaskiya daci gareta daya hakkura ya karbi mahaifin shi yadda yazo mai aiduk wanan wahalan da yanzu baiyi shi ba. Gaskiyata daine ba a son a fadi tunda ana ganin zaifi mutane nan gaba shiyasa ake kulla mashi makirci shi kuma ya kasa gane hakan yafi bukatan ya labe a gidin mace yana cin arzikin su. To dama magana kecin zuciyarki ashe kike rikewa don wanan zancen ba zancen yazu duk ya kawoshi ba dama hanyan fadin abindake zuciyan ki kikeyi. Batayi magana ba a lokacin sai tashi fuuuu da tayi tabar dakin cikin bacin rai tana fadin babu yadda za ayi ace idan ba asiri ba wai da yaki mahaifinshi haka kawai don wani dalili da aka kulla mai a zuciya tunda yaza mijin tace ko. Duk binta mukayi da kallo harta fice kafin nace Allah ya gani idan da hannuna ko wani nawa a cikin wanan zancen amma yanzu ashe laifina ake gani cewa nina hana hakan gareshi. Ai nima idan ya yarda da hakan dadinane tunda ki gidan mu ina da yan adawa masu nuna min cewa ina auren mara gata wanda baida asali. Hannu master din ya daga alaman don Allah na bar zancen ya kalli tsohuwar yace Dije zan samu in karayin hayakin abin nan na dazun ?