← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 286

Sashe 148

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fadin. Tani kece da yamman nan ta karaso ciki tana fadin wallahi uwar dakina yau dai nace barin lekoki muji lafiyan ki kwana biyu shiru koda yake hjy tace min ai kuna gaisa. Tani ai nayi fushi rabon ki da gidan nan har na manta na dauka kema ke manta dani ai yanzu takai zaune inda taga alaman nake nufin ta zauna don ganin na cire filon dake wajen . Uwardakina aure kan ya karbe ki kinga yadda kika koma kinyi kiba hasken ki ya karu ai kan zaijewa hjy dake cikin damuwa akanki da wanan labarin mai dadi wallahi. Kin kyauta da kika rufawa kanki da mahaifiyar ki asiri inyi hakan ne garuku dan a cutawa rayuwan ku kekan alheri wanan aure ya zama maki yanzu. Ba irin auren yan uwanki ba da yanzu ya komawa iyayyen ciki kullun ana gida tare da uwa shiyasa nake fadawa hjy cewa hakan yafi maku in anyi da sunan kuntata maku yanzu ya zama alheri a wajem ku. Don ga zahiri na gani nikan walle hjy zataji dadin labarin nan nawa dama damuwanta shine ba komai kike iyaci ba a rayuwanki. Banda matsalan abinci ko abunsha don gaskiya ina samu iya karfin shi Tani ba laifi yana iya kokarinshi dani alaman jin dadin hakan dana fada ya baiyana a fuskanta dkn bakin danaga ta kara washewa lokaci daya tana fadin. Haka akeso ka godewa Allah da mai maka idan har yana maka ko da kadan ne watarana idan ya samu zai maka wanda yafi hakan ai. Ki kara hakkuri sosai sama da wanda kikeyi din yanzu insha Allahu zuciyana tana bani cewa kinyi dace da miji nagari wanda kowa keson samun irinsa nan gaba. Don nasan baki sani ba duk jumma,a yanzu zaije gidan ku ya kwashi kannen ki yaje masalaci dasu idan zasu dawo kuma ya hadosu da tarkacen makulashe ya dawo dasu. Haka duk ranan talata yakan zo ya gaida mahaifiyar ki har yayi kokarin masu alheri hjy taso hana hakan amma nayi mata magana ta daina kinga kuwa ko hakan abin alfaharine gareta yanzu. Aiko kinga bai taba nuna min yana zuwa gidan mu ba fa koda wasa bai nuna min hakan ba yakan dai kira waya ya bani mu gaisa idan yana gida wanan kawai nasani ni. Na fada maki hakan ne don ki kara rike mijin ki da zuciya daya kamar yadda shima ya rikeki har cikin ranshi. Muka dan taba hira wanda taso ta fada min halin da Aisha da Rukkaiya ke ciki a gidajen auren su nayi saurin tarewa da fadin Allah ya kyauta yasa su gane gaskiya su rikesu amana ta amsa da Amin. Da zata tafi na hado mata clean da sabulun wanka da yan tarkace harda soyayyen nama tana ta godiya muka fito na rakata ta gaidasu Dije munyi sa,a inna ta dawo har ita suka gaisa tana ta kallon ledan dana rikowa Tani din tana son tantace abinda ke cikin ledan lokacin. Bayan na dawo daga rakiyanta din zan koma part din mu naji muryan Dije tana kirana da yaki nan amarya nazo take fadin. Nace matar nan ya kuke da itane wai na dan sake murmushi ina fadin mai aikin muce ita keyiwa mamata aiki ai. Bana fada maki basuda alaka ba dama wanan yar garita sosai yar unguwan tudun wadace ai shinagani haka kawai mace ta mayar da kanta baya taje tanawa wata katuwa aiki kamarta. Uwar Ahmed ta fada hakan yasa na dan daga kai na kalli gefen da take take naji raina ya baci har yanayina ya canza taci gaba da fasin baki fini ba don kwadai kina kwance da yayan ki ni ina maki wahala. Muryan Dije naji tana bata amsa da fadin yafi mata alheri don hakan yafi mata yawon tallan gida gida wai kayan mata ana daukan ta yar iska mara kamun kai . Inno tallan nawa shine na kika kira da iskanci ta fada cikin tashin hankali sai tsohuwar tace aikin nemam na kai da rufin asiri ma an zageshi mai zai hana masu yawon talla kica kica suna gogaiya da maza ba a zagesu ba. Nan ta soma cewa ni dai waga sana,an bari nai nikai gara inyi zama hakan tunda ya zama illa garan yanzu kuma . Nidai na wuce da mamakin su a raina ina mai jin zafin irin yadda uwar mijin nawa takan jefeni da kalamai haka masu zafi kai tsaye. Ban taba fadawa Ahmed ba saidai idan shi yaji ko yagani idan yana gari ya dauki matakin hakan don yakan dan debi kwanaki yana school zaria inda yake hada masters din shi yanzu. Yayin da ni kuma nake nan gusau ina hada nawa digree din wanda a lissafina saura shekara daya da yan watani na hada karatun nawa lokacin. Tani kuwa ta koma da labari mai dadi wurin ummah wanda hakan yasa ummah farin ciki tayiwa Allah godiya don ko tani bata raga komai da taji ko tagani ba a ziyaran data kai min din harma da kari. Ba abinda yaiwa ummah dadi a cikin labarin sai jin da tayi nayi kyau daki sosai a bakin mutane ga kuma karatuna yana tafiya daidai haka kuma ina zaune lafiya da kowa a gidan. Dama damuwanta ke nan dani idan ta tuna cewa bana son yawan mu,amula da mutane sosai a rayuwana gashi kuma Allah ya jefani gidan yawa yanzu. Satin shi biyu a can zaria din ya dawo ya dubamu ya samemu lafiya saidai ya samu wai kayan abincin su ya kare dole ranan ya fada kasuwa yayo masu sayayya ya kawo masu dan ledan semo da kubewa danye ya riko muna jin karan ledan yasa uwar kyala idonta akan roban tana son sanin meya dauko a ciki a zaton ta wani abin dadine ya sayo min. Aisha ki dauki ledan nan ki kaiwa Zahra ta tuka muna shi don naga nata ya kare ya fada don kawar da wani zargi a zuciyar mahaifiyar nasa lokacin. Da sauri yarinyar ta dauko ledan zuwa part dina ta sameni a dan kitchen dina na dora ruwa don ranan nasan yana gari zan girka muna abincin dare ke nan ranan. Don in baya nan saidai nasha tea ko complain in kwanta ban damu da girka komai ba tunda ni kadaine kuma abincin bai dameni ba ni . Amarya yayan mu yace in kawo maki ki girka ta fada tana miko min ledan dake hannunta din na juyo ina kallon ledan kafin nace me kuma ya kawo yanzu har na dora ruwan zafi zan zuba shimkafa a wuta ? A gaban ta na bude komai ta gani tace na bata kubewan taje ta gyara min sai hakan yai min dadi sosai don dama shine abu mai wuya ga aikin nake gani gashi kuma ta taimaka min da gyaran shi. Don haka na hada na wanke da kyau na miko mata tare da abinda zata gurje min shi ta tafi wurin su dashi ni kuma naci gaba da aikina. Duk daba saurin aikin nake dashi ba amma ina kwantar da hankalina na girkashi da kyau yayi dadi saida saurin aikin da bandashi kawai ne matsalana. Sai gani nayi Aishan ta dawo min da kubewan data fara gurza ranta kuma bace tana fadin anty kiyi hakkuri ban kai ga gamawa ba innan tace in dora girkin mu. Na mika hannu na karba ina fadin aiba komai ko hakanma nagode ai saura kadan ki gama min ba zan dade ba zan gyara shi yanzu. Tace bari dai in tsaya nan in karasa maki kafin na koma ita innan mu bansan abinda ke damunta ba haka wallahi dan wanan zatace din me na karbo maki aiki in tayaki bayan ga namu nan har na dora tukawa kawai zanyi yanzu ida na gama. Muna magana tana gurza da sauri tana kallon hanyan shigowa part din namu saura kwara uku ta kare nina juya ina kokarin yin talgi mukaji muryan mahaifiyar nasu a bayan mu tana fadin. Kekan anyi mara wayau da rashin sanin ciwon kai na rasama me zan kiraki dashi naji sanyi yanzu kece don rashin sanin ciwon kai zaki dawo nan kina kamawa wata aiki kin bar na uwarki can yana konewa ? Kiyi hakkuri mama don Allah na fada daga inda nake tsaye nasha jinin jikina don banson wani abu ya hadani da matar nan ko kadan don ban hango kaunata ba a zuciyar ta. Don Allah ki rufa min baki idan ba lalaci ba wanan dan girkin ne za ace sai an kama makishi ko me ko idan kin dafa damu zakuci ? Naga yar nata ta kallota da sauri tace ke kuma munafuka kallon me kike min don na fadi gaskiya tasan ba zata iya kula dashi ba tayi auren ko an fada mata yar aikina haifa matane tunda sun saba kwanciya ana girka masu suna ci ko ? Ke Aisha fito ki koma cikin gida ki daina zuwa kama mata aiki tunda tana iyawa inma bata iyawa ai gani saiki fada min abinda zan kama maki kiyi ba sai anje ga haka ba. Daga dan tsakar wurin mu ya tsaya yanawa kanwar tashi magana a fakaice ta aje abin kubewan ta juya ta fita sai naji uwar tayi kwaba tana binshi da kallo ta juya ta tafi. Jikinane yayi sanyi saiga hawaye na silalo min a fuskana ya karaso ciki bayan fitan ta yana fadin kema princess meyasa zaki basu aiki bayan kinsan halin inna ? Dago kai nayi da niyar in fada mai yadda zancen yake sai na kasa sai hawayen dake bin fuskana ya dauki roban ya daga yaga saura kwara uku a ciki wanda bata goge ba yace aima ta gama ashe akwai wani abinda zan kama makine dashi ? Na girgiza kai na samu na bude baki da kyar nace komai na hada sai wanan din ya rage min dama kuma Aisha din ta gyara min shi ai. Ya danyi shiru yana kallon yanayina kafin ya juya zuwa ciki ya koma ya kwanta yana duban laptop din shi da yanzu yake aiki a cikinsa har na gama girki ana gab da magariba na wuce shi na fada bandaki nayi wanka tare da dauro alwala.
Chapter 148 · 0% Book details