← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 286

Sashe 150

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda jikina yayi sanyi haka shima na kulla jikinshi yayi sanyi sosai tun lokacin da abin ya faru har zuwa bayan isha,i bamuyi magana dashi ba. Ya dawo baya ya shigo ya dauki abu ya sake fita ya dan jima a wajen ya dawo ya sameni zaune ina waya da Hannatu a lokacin ya samu wuri gefena ya zauna yana sauraren mu don a zaton shi muna magana ne kan abinda ya faru tsakanin mu da mahaifiyar nasa yadda wasu mata sukeyi idan matsala ya faru dasu. Sai yaji magana mukeyi kan test din mu har dai zuwa lokacin da muka gama wayan na kashe ina gyara zama tare da lumshe idona naji muryan shi yana fadin. Zahra na yanke shawara zan nemi wuri mu koma can nidake don irin wanan matsalan da inna take yawan maki koda yaushe. Bana jin dadin ganin yadda akan sister dina inna take rufe ido tana fada maki maganan duk daya zo mata a ranta kandan matsala kadan tsakanin ku raina yana baci da hakan sosai wallahi. Jin abinda yake fada din yasa na dan sakw runtse idanuwa don na kasa fahintar ko ya fara ganin laifinane kan matsalan mahaifiyar nasa yanzu dani. Da kyat na daure na iya fadan magana daya da cewa yin hakan kuma shi zai kara haifar da babban matsala a tsakanin mu dasu. Don zasu dauka nice na baka shawaran ka barsu ka tafi can nisa dasu mu zauna mu kadai ba tare dasu ba din don nayi yadda raina keso ke nan yadda take zato ina yi a yanzu. Koma me zat fada ta dade bata fada ba don ba zan yarda da irin hakan yana faruwa ba ko yaushe tsakanin ku. Gaskiya niba zan tafi ba ni dai takewa hakan a kanka kuma zan daure duk wani kiyayyan da take nuna min a yanzu har zuwa lokacin da zata gane cewa ni din ba haka nake ba a yadda ta daukeni din. Shiru yayi ba tare daya fadi komai ba sai zuwa can naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin don Allah ki kara hakkuri bisa wanda kikeyi a yanzu nasan ba a kyauta maki ga hakan kiyi hakkuri don ni naja maki hakan. Ba zakaci abinci bane sai yayi sanyi na tambayeshi don mu kawar da wanan zancen ya nisa tare da fadin zanci amma tare dake don nasa baki ciba har yanzu. Bana jin cin komai ne yanzu amma muje in zuba zanci na fada ina mikewa ya jawoni nayo baya zuwa jikin shi na fada ba shiri. Rufoni yayi da hannayensa yana neman fuskana ya hada da nasa yake fadin princess nasan kina daure komai ne a kaina don kada naga kasawan ki. Kiyi hakkuri don Allah zahra hakan yana min ciwo matuka a rayuwana ba komai don Allah wata kila nidin ce nakeyin abu ba daidai ba wani lokacin . Ji nayi yace hmmm kin dai fadi hakan ne yanzu amma nasan abin kema yana damun ki nace toko ya dameni yaya zanyi tunda matsayin uwancikina take a gareni nasan zata bari wata rana insha Allahu. Sai naji ya kara rungumeni yana sauke ajiyan zuciya kamar wani zai kwanceni gareshi a lolacin yadda yake min din. Da kyat na samu nayi mai dabara ya daga mukaje cin abinci ba laifi na dan daure na danci don hankalinshi ya kara kwanci don hakan ya kwantar mai da hankalin shi . Zaune yake yana tunanen irin mafalkin dayayi a daren yana son tunawa amma kuma ya kasa gano komai a kwakwalwan shi. Yana yawan ganin matashin a yan kwanakin a mafalkin shi bai masa magana amma yana ganin matashin kamar yana cikin damuwa sosai game da wani abu saidai ya kasa fahintar damuwan matashin me zuwa mai da siffan danshi yasir daya haifa. Da farko ya zata yasir din ne yake cikin wani hali amma yana kiran wayan matashin dan nasa yaji yanayinshi yana cikin kwanciyan hankali sosai lokaci. Don haka suka dan taba hira kafin suyi sallama ya kashe wayan nasa din a lokacin yaci gaba da nazarin mafalkin da karo na uku ke nan yana yinsa a dan lokaci nan da yake ciki. Gyara zama ya danyi yana fadi a zuciyar shi shin kodai wanine daga cikin danginshi yake cikin wani damuwa irin haka alakar jini yake bibiyan shi a yanzu. Yasan a yanzu yana da rauni da sakaci zuwa ga yan uwan nasa da bai kulasu yadda ya dace din saidai shima yasan cewa haka kawai yaji baya son kula kowa nasa a yanzu. Dan daman shi daya shine alherin sa ga mutanen unguwa da mutanen gari bai kaiga ya fasa dan basu ihisanin daya kan dan raba garesu ba idan yazo garin duk da yasan bai masu komai ba a cikin irin tarin arzikin da Allah ya nufeshi dasu a rayuwa. Duk da yasan maidakin shi ma,ana uwargidan shi Yabi da yanzu kusan itace ke juya komai a yadda takeson ya kasance a rayuwan ta. Duk da hjy tayi kwatance da kokarin rabashi da kowa kamar yadda tayi nasaran rabashi da yan uwanshi ta hanyar kakabesu kaf a rayuwansu . Sai ita da nata yan uwan da irin mutanen data yarda su zauna a kusa dasu lokacin amma kuma duk da hakan batayi nasaran rabashi da aminan saba na kurciya da hakkurin su kan irin wullakanci da suke fuskanta baisa sun gaji sun bar mijin nata da ita ba. Wanan abin yana matukar konawa hjy rai don ta tsanesu kamar yadda ta tsani mutuwarta a lokacin haka ta tsani ta bude ido ko kunnuwanta yaji mata yana ambatan sunayennsu ko zai masu wani alheri a rayuwan su. Hakama yanzu da zancen wanan matashin mai kama dashi daya fito yasa hankalin hjy din ya kara tashi sosai duk da bata sancewa shi wanan matashin wayeba gareshi. Tayi kokarin acikin siri nasa mutanen ta su binciko mata wayeshi amma anyi rashin sa,a har rana ita yau basu ma ji wani duriya daga gareshi ba balle ganin shi. Har tellansu isah da shima yaga matashin ta bincika a waya amma ya nuna mata shima ganin shi yayi kawai kuma yaga kaman nasu kamar yadda wasu da dama dake wurin ranan suka sheda hakan. Tun abin yana damunta a rai har ta dan fara sakewa don ba wani labarin da zai gamsar da ita akan matashin ta bar abin ga kamace kawai irin na dan Adam wani lokaci. Da wanan tunanen ta manta da zancen saidai bata bar wani kafa don daure mijin nata da takeyi a ko yaushe na ya zauna under control din ta kada ya tsalake duk wani abinda tace dashi a rayuwa. Ta kumaga nasaran yin hakan don ko banza shidin ya kasance ba mai hayaniya bane ga kuma asirin dake aiki sosai a kanshi ko yaushe cikin barbade yake a jefa a filon kwanan shi. A shafa a takalman sakawan shi a zuba mai inda zaibi duk akan duniya da zai iya bari itama zata iya barin shi ko wani lokaci amma ta manta da hakan duniya kawai aka saka a gaba lokacin da nema daga ita sai diyanta kwara hudu data haifa dashi biyu maza biyu mata. Saidai iya binciken ta ita da bokayen nata da malamai Allah ya batar masu da basiran cewa dan nashi yana raye ko yaushe sukayi mata duba sai suga ai baida wani da a duniya sai diyan ta. Don kamanin danta suke bata sak da wanda suke gani a duban nasu don hakane hankalinta ke kara kwanciya don tasan sungama da wanan babin a rayuwanshi ko. Bata san Allah ya riga daya tsago wanan hallitan a cikin jikinshi ba yana rayuwa a wani bangare na daban a cikin kasa kamar yadda suma suke nasu rayuwan cikin jin dadi a daulan mijin nata da Allah ya azurta shi dashi ba. Ba wani abu takewa hakan ba tun farko ita da kakanta data bar duniya a yanzu tareda yan uwanta dake taimaka mata wurin irin wanan halin nason su mallaki duk wani abin hannasushi tun farko. Don irin hakane yasa tun farko suka nisantashi da kowa nasa bayan sun gano barshin gida a lokacin bashine solution a garesu ba. Yasa suka karya asirin ya dawo gida saboda sunsan dukiyan ba zata ciyu garesu ba su kadai tunda ga yan uwanshi da suke uba daya sun mamaye komai bayan batan nasa. Yau gidan yana da jama,a sosai don mijin nasu dake gari don hakane duk wace ke girki bata da hutu idan mijin nasu yana gari. Irin hakane ya kasance ga ummah da girkin ya fado kanta a washegarin ranan da Abba yazo garin ke nan zata karbi girki hannun mama wace ita iya abincin dare dana rana zata girka dashi din. Suna kitchen suna aiki da Tani mai aikinta don tun karfe biyu suka dora girki a gidan suna tsaka ga aikine yan uwan Abban mu mata suka shigo don ganin Abba din a lokacin don ya kwana biyu bai leko garin ba. Tun bayan auren shi da hjy karima yanzu Abba din sai ya kwashe kwanaki mai tsawo bai leko Gusau ba suna can Abuja tare da amaryan shi . Ganin tana aikine basu tsaya a part din ba suka shiga wurin mama sun dan dade tare da mama din kadin Abban ya sallami wasu bakin da yake ganawa dasu lokacin yace su shigo gashi kafin wasu su shigo mashi ya tsayar dasu wurin son ganin su din. A wanan lokacin ummah ta shiga lokacin girkinta na ranan don haka ta shigo falon suna ciki da yan uwan nasa don ta dan rage wasu aiyukan daya shafi rayuwan Abba din da suke masa da kanau basai sun saka yan aikinsu ba sunyi. Gwaggo uwace ke fadin hjy salma naga fa sai wani sharning kike yi yanzu meye sirin hakanne yanzu sai gwaggo rabi tace meya dameta yanzu tunda ta aurar da yar mu ai dole hankali ya kwanta kafin wa yan nan su taso kuma don Amira kan ba yanzu ba kusa auren ta sai me rabon ganin hakan. Gwaggo uwale din ta kara fadin aiko naga mama da mijinta a mashin zasu makaranta wanan yaron akwai kokari wallahi haka zai daukota saman yar mashin dinshi ya kawota gaida mu har gidajen mu.
Chapter 150 · 0% Book details