Sashe 211
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka akuyan ta karayi a cikin wani irin sauti mai ban tsoro zakace wani kosasashen dabba ke kukan kafin yan uwan suma su dauka a lokaci daya . Zakice sunga wani abune ko wanine yazo wurinsu yadda suke kukan gaba dayansu dan kokarin yunkurawa naji yanayi zai dago daga kwancen da yake din. Jin hakan yasa na dan daga daga jikinshi din ya samu yakai zaune lokaci daya yana fadin Allah sarki nasan muryana sukaji suke wanan kukan gashi dare yayi balle na zagaya wurin su. Aiko dabba yasan mai kyautata mashi dole suyi kuka don basu samun irin kulawan da kake basu idan suna Dijece mai kula dasu kuma ba kafa ke garetaba sosai. Kingani ko wallahi ina can ina tunanen su nima don nasan ba zasu samu kulawan daya dace ba dama har mafalki dasu nakeyi wani lokacin idan na kwanta. Jin hakan yasa na dan kalleshi kafin ya fadi wani abinda zai daga min hankali ya hanani barci da dare nace dashi. Dare yayi kan nima kwantawa zanyi kada in Makara don gobe muna dashiga school affa nafa shafa zaki fita goben ai ya fada sai kuma naga ya dukar da kanshi kamar mai tunane a hakan na sulale na shige dakin. Bandaki na shiga na kara gyara kaina kodana fito na sameshi ya shigo yana cire rigan dake jikinsa yana fadin zafi yakeji duk da sanyin da yai yawa a lokacin. Azoto na yadda ya gaji din nan ba zai nemeni ba a ranan son gajiyan dake tare dashi tunda yace min a ranan suka sauka Nigeria ya shigo jirgi karfe hudu zuwa sokoto a nan kuma ya dauko mota haya ya karaso dashi gusau. Don haka na dauka gajiya bai bari mu kasance tare a ranan sai gashi ina kwanciya naji muryanshi a bayana yana fadin Zahra kinsan fa nayi missing dinki sosai duk da banga hakan a gareki ba. Master agajiye kakefa kaima ka sani yanzu me zaka iyayi bayan wanan gajiyan dake tare dakai oho haka kikace yarinya aini ba raggo bane irin ki bari ki gani yanzun nan in nuna maki hakan. Koda gari ya waye na tashi duk jikina yayi tsami kuma ga shiga school ga hada breakfast da zanyi muna dolene tunda master yana garin duk da rashin kuzarina haka na daure nayi aikin dake gabana a lokacin yana kwance yana barcin gajiya kilama baisan na tashi bani . Abinda bai taba yi min ba kenan don tare mukan tashi idan ina aikin safen ya taimaka min dasu shara da wanke wake da gyaran daki amma a ranan ban samu hakan ba duk ni nayi aikin da kaina ni kadai. A gurguje nayi wanka nakai masa nasa ruwan dumin don huturun da akeyi sosai a wurin mu din wanka saida ruwan zafi ga mutum. Ina dauko kayan da zan saka ya falka a gajiye ya bude idanunshi yana fadin har kin tashine ashe na dan juyo nace eh . Yanzuma school zan wuce saboda na dan makara nasan yau yana da wuya na samu shiga darasin safe yadda na makara din nan ya akayi kika makara naji ya fada abinda yasa na juyo ke nan ina masa kallon mamaki don duk lokacin nan da muke magana fuskana yana kallon cikin wardrobe dinane. Kwane yake ya dunkule saman gado ya dora kanshi a filo ya lefe yana kallona murmushin danagani a fuskanshi yasa na gane zolayata yakeyi da hakan . A dan marairaice nace haba master kaifa ka hanani barci daren jiya kuma yanzu na tashi nayi aiyukan safe ace tsakani da Allah amma baka tausaya min ba ? Yana fadin ayya sorry yarinya shine baki tasheni in tayaki ba, dan zo nan na dan karasa don ban kwankwasa kofan da mukajine da karfi daga wajen part din mu ya hanashi karasa maganan da zai fada din naji yaja tsuki da karfi yana kokarin saukowa daga kan gadon . Sai kuma ya koma ya zauna ya kalleni yace yanzun haka innace fita kice mata ban tashi ba daga barci ba har yanzu. Kalloshi nayi ya kafin nayi magana muka kara jin dukan kofan da karfi wanan karon hakan yasa ya dago a hasale ya nufi kofan da kanshi yana fadin wai waye don Allah zai balla min kofa hakane. Mune yaya Inna ce tace mu dibo ko kun tashi taga baku fito ba wai muryan Asmau ke fadin hakan yace shine tace kizo ki dinga dukan kofa haka cikin daga hankali kice in mun tashi ai zamu shigo ciki mu gaidasu da kwana kada ki kara gigin zuwa nan kice kinzo tayar damu don ranki zai baci. Ya mayar da kofan falon daya bude da karfi ya buga din bai bude na shigowa part din ba a lokacin ranan ne karo mm a farko da hakan yai min zafi har nake tambayan kaina wai me inna take nufi da hakan da takanyi munane. Inma har tana tunanen wani abune ai mun riga mun more junan mu da dareko don ba zata hanamu kwana tare ba na fada a kasan zuciyana duk dana makara ban fita ba don yunwan da nakeji don haka na zauna na karya ni kadai a falo shi yana cikjn dakin ashe wanka ya shiga Ina gamawa ya fito yana fadin wani mashi din dai zanyi kokarin saye kafin in koma zaria in aje don zuwan ki school bakiga yadda bin achaban nan yake ci min raiba wallahi. Kawai dai banda yadda zanyine a yanzun din yasa na kyale hakan amma wanan abin yana damuna a rayuwa na dauki ruwan tean dake gabana ina kurbawa nace don kawai wasu mazan na daukana ko ? Haba dai ni bama wanan ba duk wanan fa zahra ta dalilina kika shiga wanan halin a yanzun don kawai kin aureni yasa aka kwace maki motanki a hannunki akabawa wani yana hawa ina gani. Shi kuma Abba kamar zai karbo duk da a lokacin wallahi ban ra,ayin a dawo maki dashi kamar yadda ummah ma bata son a dawo dashi tace. Tsohon magana ke nan ni yanzu ba motana ba komai da zai fito hannun Abba a yanzu irin haka bana so don na fahinci ba a bani sai ran ummah ya baci a lokacin kaga gara dai a zauna lafiya zaifi sauki na fita na dauraho cup din na aje a kitchen na dawo na dauki jakkata ina mashi saina dawo ya amsa min haka kawai naki shiga cikin gida in gaidasu na wuce a bina. Kamar yadda na zata na makara sosai haka din ne ranam don ban samu darasin safe ba ya wuceni a ranan don haka na jira saida malamin ya fita nashiga ajin. Kan hannatu na duke na aje jakata saman desk ina kawai zaune ta daga tana fadin Zahra har kin daga min hanlali wallahi lafiya yau kika kai wanan lokacin Lafiya kalau master ya dawo jiya cikin dare yasa na makara yau don ban shirya zuwanshi dole na tsaya hada mashi breakfast kafin in fito. Kai haba don Allah amma kinyi kokari ma da kika fito mutum yayi irin wanan tafiyam ya dawo kuma ki fito da kawai ki zauna gida abinki na kwana biyu. Zaune nake daga gefenta ina hararanta kafin nace idan na zauna gida shine zai min marking din pepper na ya bani A ko kece zaki maka min ki bani gara dashi ya gama ya huta yanzu. Niko karatuna da kike gani hannatu zakice nice na fara karatun boko a gidan mu don yanzu idon kowa a kaina yake tunda su har yanzu basuyi making ba duk da karatun da sukayi a lagos da illorin. Nafa sani nasan komai nima dai fadi nakeyi ai ina zaki zauna gida har na kwana biyu sai kace baki san ciwon kanki ba dai nace ai shiyasa kikaga na dake kodan na fitar da kaina da ummah kunyan hakan. Sai yanzu tunane yazo mai na rashin kyautawan da baiyi ba da bai tsaya ya tambayi Rashida ba a lokacin akala dai rabuwan arziki sukayi a lokacin don haka bai kamata ace yaje har gusau din ba bai tambayeta ba. Sai yanzune wanan tunanen ya tsaya mashi a zuciyarshi yake ganin rashin kyautawan don idonshi ya rufe da son ganin dan nasa a lokacin amma kuma ai bai kamata ace ya manta da ita ba gaskiya. Shigowan hjy Yabi dakin yasa shi katse tunanen da yakeyi din a lokacin ya bita da kallo har ta iso inda yake kwance takai zaune a bakin gadon tana kallonshi. Sun shirya tun bayan da yaransu suka shirya tsakaninsu suka lalashi mahaifin nasu akan kome matar nasa tayi masa suna rokonshi daya yafe mata don Allah sabodasu . Don basu jin dadin yadda abubuwa yake faruwa yanzu a tsakanin su gashi har abin yakai ga barin gida duk da basu san me yafaru ba daddy munsan kai mutum ne mai hakkuri don haka kayi hakkuri da mommy ku karasa saboda mu da rayuwan mu. Ire iren wana kalaman da diyan suke ta kirashi suna masu yasa dole taji kawai ya hakkura din da ita su zauna tare amma fa wanan abin ba wai zai fita ranshi bane. Don haka dole a yanzu takon zamansu ya canza sallo shi ya koma miji ita ta koma matsayinta na mata a gidan ki banza ai yanzu ba ita kadai bace a cikin gidan. Wanan ne dalilin sauyawan shi ya sauko suka fara shiri a tsakaninsu sama sama duk da hakan bata gamsu ba yanzuma tazo mai da korafine dalilin kwace bata kudin ma,aikatan gidan da yayi ga hannunta yake basushi direct ta wurinsa. Don haka ba karamin kara zubar mata da girma hakan yayi ba kawai dai tana dakewa kamar yadda yan uwanta da yayanta suke bata shawara ko yaushe gashi har yanzu ba zatace ita ga laifin da tasan tayi masaba. Kawai dai ta tsunci kansune a cikin wanan hakin da lokaci guda ya ricibe mata komai yana batun gagaranta a gidan kamar yadda ta saba yi a baya can. Bayan ya gama saurarenta ne ya dago yana dan murmushi kafin ya kalleta da kyau yace Yabi waiko kina tuna mutuwa a zuciyar ki Alh don me zaka tambayeni hakan kuma ? Yace yes dole in tambayeki hakan mana ace mace kullun ita