← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 285 OF 286

Sashe 285

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba a rayuwan zaman mu don zahra bata rageni da komai ba a zaman mu na duniya. Duk abinda da ake nema wajen mace inna kinsan zahra tana dashi tome zan nema a wurin wata da har na rashi a zahra aida na zama butulun namiji a duniyan nan. Lokacin Asmau dake labe cikin daki ta kasa hakkuri ta fito don dama bashin itace taje ta ciwo take gudun matar jin muryanshi ya shigo kuma yasa ta labewa don kada ya gane bata bar gidan ba dayace tayi din. Ganin Asmau ta leko yaba inna kwarin gwiwan fadin rufa min baki sallamame banda farin meke rudin ka a cikin ta yace inna a naki zaton ke nan. Duk na miji da mutumin kwarai zaiso zahra ta kasance uwar yayanshi tavkuma zama mashi adon gidan shi saboda idab tarbiya ake nema zahra tana dashi ilimi asali natsuwa kyau uwa uba haduwa duk zahra tana dashi kin sani. Shin inna ba zaki tayani son zahra ba kamar yadda ita yan uwanta suke sona tsakani da Allah inna kowa na zahra yasan baki sonta a gidan nan ban dauka gaskiya bace sai yau din nan da kike son tarwatsa muna zaman lafiya da matata inna ? Sherin kuma zaka kullamin yanzu don kawai nace ka auri yar uwarka dake mutuwan sonka tun kurciya idan tana sona ni bansonta inna don ko banza Suwaiba ba irin macen da nakeso bane a rayuwana ba. Don haka kada a kara min wanan zancen don Allah don gaskiya idan an kara rayukane zasu baci sosai a lokacin ya dogo ya kalli Asmau kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya fice daga gidan kai tsaye. Amma inna lalai yaya ya daukeki tallaka don yaga baki boko ba baki da kudi kuma yasa yake nuna baki isa da sh, , , , Shiru tayi tana kallon kofan shigowan shine a tsaye don ya manta bai rufowa dije kofan daya budeba wanda yanzun kayan Aishane a dakin da sauran tarkacen dije. Ya tuno yasan kuma idan ya barshi a bude banu mai rufo mata shi hakan yasa ya dawo gidan ya mayar da kujeran a dakin ya rufo mata dakin nata. Shine kuma ya samu kanwar tasa tana magana a kansa yanzu ya tsaya yana sauraren abinda take fadi baiyi magana ba dakin dije ya shiga ya mayar da kujeran ya fito. Kara kallon Asmau yayi ya fice gidan kai tsaye yau ko na shiga uku Asmau ta fada me zai maki ai ba zaice komai ba tunda yasan ba zan barshi ba. Saidaya gama abinda ya fita yi ya dawo gida bai jima da shigowa gidan ba akayi masa sallama ana fadin ga masu nama nan sun kawo ya fita . Ya samesu ya kasa yadda za ayi da naman yasa aka shigo muna da sauran a ciki yake fada min ga namanan ya turawa inna nata ya kuma sa ankai gidan mu amma anyi kulli biyu na mama daban yace aba Tani na ummah ta gyara masu. Aiko angode wanan dawainiyar baiyi yawa ba kuwa har yajuya zai tafi sai ya juyo don jin abindana fada a lokacin cikin mamakin kalamin nawa yake fadin . Zahra ni wani dawainiya nayi haka da har kike ganin yayi yawa ga mutanen da suka dauki yarsu suka ban a matsayin abokiyar rayuwa . Wanda nake alfahari da kasancewa hakan a yanzu zahra duk wanda yace min bakeba nima zance bashi ba kowaye kuwa yayi gangancin fada min hakan a yanzu sai inda karfina ya kare a wurin yakar maishi. Ke daya aka kawo gidana gashi yau ta sanadin ki mun koma mu hudu gana biyar nan din mu nan ubangiji yana shirin kawo muna in Allah ya yarda. Lumshe idona nayi ina maijin dadi ga irin maganganunshi gareni da kullun yake nuna min shi ba butulu bane a cikin maza yasan anyi masa an kuma kyautata masa a lokacin da baida shi da ya kamata ace munyi masa. Inna na gida zaune da yamma su baffa sukayi sallama taji mamakin ganin yan uwan mahaifinsu suku gaba dayansu lokaci guda haka dole tasan wani abune ya kawosu gidan a lokacin. Shimfida tayi musa take suka gaisa tambayansu tayi ko lafiya babban nasu yace ai tunda kika ganmu balafiya ba don yaron nan Amadine ya samemu gida da wani zance mara dadi akanki da yarki. Allah ya baki da dan albarka da kowa ke fatan haihuwan irinsa a duniya amma kina son ki halakashi da bakinki don wanan yar taki mara hankali tana zugaki. To munzone mu fada mata idan mun isa dake ko tayi aure hakana ko kuma ta kwashe kayanta ta koma gidan ubanta tunda baku da hankali daga ke har ita. Kuka inna ta fara tana fadin maganganu ya kara fadin saiki matsa kiwa kanki baki a kan wanan yar taki don kina takaman kin haifeshi. Sukai mata kaca kaca don bai boye masu komai ba hankalinta ya tashi jin yace dama saboda ita muke zaune a nan idan ta matsa mashi zai sayar da gidan ya koma wurin mahaifinsa da zama. Wanan yasa muka samu sauki akan inna tazo har gida ta taso Asmau ta bashi hakkuri itama din kuma taba nata mahaifiyar hakkuri akan ta daina irin halaiyanta. Allah da ikonsa Abba ya dawo saman kafansa da lafiyansa saidai babu karfin jikin sosai kawai za a ce Abba ya dawo yana sakawa master albarka dashi da yan uwanshi. Mun wuni a gida tare da ummah don munje taron Abba da dawowa ranan a can gida muka wuni ana nuna muna gata da zalla kauna. Ina can ne master ya bugo min waya yana sheda min zancen komawa da zaiyi washegari don aikin daya taso masu a lokacin dole zai barmu a nan din ya tafi don shima yasan bazan bishi haka a gagauce ba. Hakan yasa na dawo gida don tafiyan nasa na hada mashi kaya duk da hakan saida ya gwada cewa mu tafi a tare zaifi masa saukin amma kafin nayi magana Dije ta bashi amsa da haba Amadi . Ka barsu nan wanan karon ta haihu a gaban iyayyen ta da yan uwa inyaso daga baya sai kazo ka daukesu ku koma zaifi tunda yanzu kaga cikin nata ya tsufa sosai ai zata iya wahala a hanya. To dije yadda kikace hakan za ayi don nima ba dadewa zanyi a can ba in dawo don aikina nan kada ya tsaya ga kuma ginan gidan ki Dije naso ace angama kafin nayi tafiya ki koma ina nan . Washe gari bai tafi ba saida yaje yayi sallama da Abba dasu ummah yayi masu alheri mai yawa ta bajinta ya tafi hannatu kuma a ranan ta bugo min waya zata shigo garin don jos suke zama da mijinta inda yake aikin koyarwa a can jami,an jos din. Zuwanta yai min dadi sosai don ta debe min kewan wucewan master kwanata biyu a gidana bata fita ko ina ba saiga na ukune ta shirya ta tafi gidan yan uwanta. Ta kwana biyu kafin kuma ta wuce kauyen mijinta can ma tayi masu kwana biyar ta dawo kamar dawowanta nake jira a daren nakuda ya kamani mukaje asibiti da ita da dije banfi min goma sha ba Allah ya saukeni lafiya. Na haifo dana mai kama da ubansa sak kamarsu daya da Amir da gani kaga jinin fulanin usuli mun kwana can saboda dare yayi da safe aka sallamoni muka dawo gida. Sai bayan mun dawone muka bugawa ummah waya ina sanar dasu mamaki tayi don koda dare munyi waya lokacin na dan fara jin nakudan. Na samu barci a lokacin ya bugo min waya ganin shine hannatu ta tayar dani tana miko min wayan na karba shine yake kirana da vedio call. Na dauka abinda na fara nuna mashi fuskan yaron dake barci yana nade a cikin showel fari da karfi yace what zahra kin haihu ke nan ashe gaskiyan dije datace idan na wuto daku zaku wahala har nake ganin laifinta ta hana min matata. Kafin can yace me muka samu nace baby boy nima na samu babana yanzu yace Allah ya raya muna baba a cikin sunna na amsa da amin kafin ya koma tambayata bana jin komai ko a jikina ? Lafiya kalau nake gaskiya kuma ina shan magani ok a debo ganyen tumfafiya a dinga dan gawa yaron jikinshi dashi da mankadanya kindai san yadda mukewa yarashi a nan na amsa da eh Allah ya raya muna baba Ali custom akan tafarkin addinin islama na sake fadin amin. Washegari yan uwa da abokan arziki suka cika gida suna zuwa barka wanda hakan ya zamo min bakon abu don can bai mutum biyu ko uku dake shigo min ba idan na haihu. Sai nan na gane dadin haihuwa a gida din yadda yan uwa suke cika gida suna kuma aikawa jariri adduan fatan shiruwa da more rayuwa a gareshi. Sati ya kewayo aka rada wa yaro suna tare da yanka anci ansha yadda ake gudanarda shagalin suna bisa al,adan malam bahaushe inda yan uwan haihuwan master sukazo don halartan bukin sunan yaron nan da yawa suka sansu suka kuma san a yanzu master ya wuce raini a wurin kowa. Idan nace dake su Anty Aisha da Rukkaiya sai gwaggo shafa dake uwar buki sune a tsaye a sha anin kada kiyi mamaki balle iri didiman da sukaga anyi tun suna diba suna boyewa duk da ana fada min nace su kyale kowa na dan lokacine ai abin. Da zasu tafi kuma nabi kowan su da abin arziki aka kaisu gida duk immani ya kashesu don sunsan in sune ba zasu iya daure in shige masu gaba ba yadda su na barsu suna min komai a lokacin kuma yadda sukaga dama. Duk yadda master yayi kada a samu matsala da inna a lokacin sha,anin hakan bai yuyuba don saida inna ta aiko nan gidan wai a basu nasu naman da aka soya. Nasan yadda ya tsara abin don saida ya fada min komai ga yadda za ayi hakan dayace din kuma nasa akayi komai ankai gida mu ankai gidan inna amma saiga Asmau a cikin dare wai inna ta aikota ta karba. Nace bamu kasa komai da ita ba a nan don ankai maku naku
Chapter 285 · 0% Book details