Sashe 15
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari ummah na tana kitchen tana hada breakfast na sameta a tana tsaye tana fere arish daga bayanta nake fadin ina kwana ummah ? Da sauri ta dan juyo zuwa inda nake a kofan tana fadin fuska ba walwala a cikinsa maamah kin tashi yaya kan da sauki ta fada tana kallon yanayi na a lokacin. Nace eh ummah ina kwana yau kece ke girkin da kanki kafin Tani tazo tace nice kinsan Alh na gari dan anjima nan kadan jama,a basu barin ya zauna karshe ma ya fita. Abba ya dawone na tambaya a cikin mamaki jin haka yasa ta juyo dakyau tana fuskantana tare da fadin yadawo mana jiya ai har nan yake wurin ki shida malam bawa ai. Cikin mamaki na dago kai na kalleta nace malam bawa waye haka ummah tace wanan malamin dake kasan layin nan shi ya dauko a cikin dare yazo ya ganki. Jikinane yayi sanyi na karasa inda take ina karban yunkan data dauka a hannunta tana shirin fere dankali don ta nufi inda dankali yake na tako ina mika hannu zan karba. Baki da lafiya ki koma ki zauna ta fada ummah naji sauki zan iya na fada ki barshi ai ba wani abin mai yawa zanyi ba dankalin nan ne kawai da kwai zan soya sai ruwa tea gaya na dora a kattile. Hakan baisa na fasa amsan yukan a hannunta ba ta miko min kafin ta juya ta duka tana debo min adadin dankalin da zan fere din a lokacin. Tsaye nake ina fira naji muryan ummah tana fadin waini Maamah ina kika hadu da iskane haka har suka shafeki ? Wani irin juyowa nayi wanda ya fitgita ummah har ta kalli yukan dake hannuna danayi setin inda take dashi da sauri na sauke hannuna kasa tare da fadin iska kuma ummah ? Aiba shiganki sukayi ba shafanki kawai sukayi malam yace ki kula da addu,a maamah ko banza kinsan yadda muke a cikin mutanen nan bawai sun daukemu da daraja bane. Don gani suke har gobe mu bamu cancanci rabar Alh ba matsayin mu baikai ace muna cikin ahalin Alh ba a yanzu don kasancewar iyayyena tallakawa ko don na zama bare a cikin su yasa har ku suke kallon ku a matsayin da bankai ga tantanceshi a zuciyana ba. Kallon Ummah nake cikin mamakin zancenta gareni wanda ban gama na iskan data fada sun shefeni ba ga wani zance ta dauko min a yanzun kuma wanda na kasa tantance inda zancen nata ya dosa a lokacin. Taci gaba da fadin sai jiya na kara fahintan cewa har yanzu maman ku bata dauke mu da muhinmanci ba a gidan nan don irin maganganun data fada min a jiya kan kawai wai Alh ya dawo gidan nan a ranan girkina ta rufe ido ta fada min magana na kaskanci lokaci guda. Nayi duk kokarin da zanyi wajen tausan zuciyana a zauna lafiya amma a kwanakin nan tun dawowan mu garin nan yanzu ina ganin wasu halaiyan da hjy maimuna take tsiro min dasu na daban dake nuna ni banda daraja ko kima a wurin Alh da kowa. Ummah meta fada maki haka haka har kika kasa hakuri dashi ranki ya baci haka don nasan a zaman ku kece mai hakkuri da kawar da ido akan komai da akeyi a cikin gidan nan. Nishin ciki ummah tayi lokaci guda tana fadin yi sauri muyi aikin nan kada mu makara rana ya fito bamu gama ba naci gaba da fere dankalin gabana a hankali zuciyana tab da tunane. Allah ya taimaka anyi angama har ankai falo an jera duk lokacin ba wannda ya fito ummah ta koma tayi wanka ta shirya cikin wasu simple lace masu taushi dinkin zani da riga sai turare mai taushe data goga a jikinta. Part din Abba ta nufa sai ta samu mama a cikjn zaune tare dashi suna magana da ace can bayane fita zatayi daga dakin da sauri amma wanan karon ga mamakin mama sai taga tayi sallama ta shigo. Abbah tafara gaidawa tayi mai ya gajiyan hanya kafin ta juyo inda mama take tana fadin hjy antashi lafiya ya kwanan su Aisha dacewa yan matan dakin mama din a yanzu su biyu. Ciki ciki mama ta amsata ba yabo ba fallasa ta mike daga inda take zaune zuwa bandakin Abba din ta hada mai ruwan zafi ta kara gyara wurin ta fito. Lokacin ne Abba ke fadin mamana ta tashi kuwa ko har yanzu bai sake ta ba tace tashi tare ma mukai aikin breakfast da ita ai. Ya jikin nata yanzu ummah tace Alhamdullahi don ta dan watsake masha Allah ya fada barin yi wanka na lekota sai wayanshi dake gefe ya dauki kara lokaci guda ya kalli wayan kafin yace jiya saidai muka dauko malam bawa wa mamana lokacin kin rufe part dinki. Umm, ummmm ta fada kawai tana mikewa tsaye tare da fadin yanzu ni ai uwarta ta nuna bani na haifeta ba don ta nuna min hakan kaima gashi kuma ka fada yanzu da bakinka ai. Da inada muhinmanci ko iko da ita aikona rufe kofa zaku tayar dani mudai zuba daku inga iya gudunku inda zaku da wanan sallon da kuka dauko min a yanzu. Dukkan su kallon mamaki sukai mata lokaci guda ta juya ta fice daga dakin ta gaban ummah tayi saurin jada baya da sauri kada su kai ga hada jiki abinda ba a so ke nan kishiya da kishiya su hada jikin su yana jawo tsiya a gida koga mijinsu inji manya. Na rasa meye matsalan maimuna a kwanakin nan murmushi ummah tayi ba tare datace mashi komai ba tabarmashi dakin itama ya bita da kallo yana gyada kai. Mikewa yayi ya shiga wanka ya fito ya ya shirya bai zauna cin abinci ba ya nufi part din ummah tana zaune da kannena a falo su uku ya shigo part din. Gaidashi suka farayi ta hanyar tasowa daga inda suke zaune suna mashi sannu da zuwa tana amsa masu tare da tambayan su karatunsu a lokacin naji muryan shi a falon mu yasa na nufo falo da sauri. Daga kofa da zaka fito daga dakunan kwanan mu nace Abba you are welcome ya dago inda yake yana kallona fuskanshi cike da murmushi yake fadin mama kece nan haka yau ya fada a cikin kulawa. Karasowa nayi zuwa tsakiyan falon namu na sameshi kasa nakai yadda muka saba gaidashi ina fadin ina kwana Abba ka dawo lafiya yace Alhamdullahi mama yaya jikin naki da sauki dai yanzu ko ? Kan ya daina ciwo ko jiya nazo mun dade dake baki san lokacin da haka ya faru ba dake hankalina ya tashi jiyan sosai yadda na ganki din sai nake tunanen ina kika hadu da iska haka. Da sauri na dago kai na kalleshi kafin nayi kasa da kaina da sauri ba tare dana bashi amsa ba ganin hakan yasa yace to ki kula don Allah mama don malam ya fada muna gamo dasu kikayi a wani wajen. Nan ma na sake dago kai a cikin mamaki sosai ina ksllon su Abba din nace dasu Abba ban hadu da kowa ba hakani bansan zancen kaba Abba. Kallon ummah yayi kafin ya juyo inda nake gurfane yana fadin ki kula da kanki watarana inyi lfahari dake uwata yawan jin kida da kallace kallace a cikin dare ko shiga bandaki kai tsaye ba tare da yadda musulunci ya koyar damu ba duk ki daina uwara don tsaron lafiyan ki. Na amsa da toh Abba nagode ina mikewa hannu yasa ga aljihun riganshi ya ciro kudi masu ya miko min lokacin har na juya zan tafi tafi kanena daya ke fadin anty maamahb Abba yana mika maki ya nuna min Abban da hannu. Juwowa nayi inda Abban ya ya zaune ya rike kanin mu karami a jikinshi wanan sallon na Abban namu mun dade rabon mu da muga irinsa a garemu tun dowowan mu garin zamfara Abban ya daina bamu irin kulawan da muka taso yana bamu. Lokacin da muke zaune Abuja kula muke samu wanda duk wani uba zaibawa iyalanshi irin wanda ke kawo shakuwa ga iyali amma muna dawowa sai sallon rayuwan ya canza a wurin mu gaba daya har Abban namu din a yanzu. Don ko bu za a bamu saidai mama ce zata sayo ita Abba zaibawa kudi ko kuma ta saya idan yazo ta karbi kudinta a hannunshi. Irin abubuwan da dai ke tauyewa dan adam hakkinsa da rashin yanci a gida shi muke gani a zamam mu nan zamfaradin daga mu har mahaifiyar mu muna a tauyene muna zama na rashin gata a cikin mama da yaranta wanda muke ganin su suna komai nasu a cikin gata da walwala na jin dadin nuna halin akwashi a gidan mu din. Don ko motan da nake hawa yanzu wanda anty Aisha tayi amfani dashine mama tace ta barmin shi a ka sayo mata wani na mata mai kyau na yayi ni kuma don zuwa school aka ban wanan din don shima baiji jiki ba. Gyara akai ta kara komawa sabuwa nake hawa har mutane na ganin aimu a cikin gata da jin dadi muke koda yaushe don basu gane gaskiya idan ba wa yanda suka zamo na jikin mu ba sunsan komai. Kaina girgizawa Abba din alaman ya barshi murmushi naga ya sake a fuskanshi yana fadin uwata idan ban bakiba wa zai baki ki karba karbi ki aje a wuri ki. Hannu bibiyu na mika na karba ina godiya kafin na tashi na mike na bar falon saida ya dan jima da yaran kafin ya fito yal nufi part din mama data riga ta samu labarin cewa Abbn yana part din mu kusan minti ashirin a ciki tare da mu. Don haka yana shigo tana zaune ta hakince saman kujera sai commad da take bayarwa daga inda take zaune din don ita mama tana da yan aiki har uku part dinta. Bayan diyan yan uwa maza da mata dake zaune tare da ita don har yan aikinta biyu a nan suke kwana a gidan namu don aikin mama. Abba ya shigo da sallaman shi fuska mama ta hade mai nan wanda suke falon suka shiga gaida Abba din yana amsawa ya kai zaune a