Sashe 175
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
na mike zuwa part dina na kwanta ina fadin in sun gama su tayar dani in rufe kofa Asmauce tayi saurin fadin ni a nan zan kwana barin tashi in rufe gida dayani. Inna nada baki a cikin gida na fada tace zan fada mata ta rufe don yaya yaja muna kunne sosai kan rufe gida wai barayi ke yawo a unguwa. Ta mike zuwa cikin gida bata dade ba ta dawo tana guna guni ta fadin wai inna kada mu kwana nan yau don dama idan baya gari a yan kwanakin nan da muka fara shiri dasu sukan kwana a part dina saboda kallo. Ai basu koma a nan din suka kwana dukkan mu falo muka kwana tare dasu nayi sammakon tashi zuwa school inda daga can gidan mu zan tafi in duba maijego sai dana shirya na shiga sallaman su nake fada masu sai da yamma zan dawo zan tafi gidan mu daga can in duba mai haihuwa . Asmau tace dani aida daga nan zaki tafi da mun tafi tare ina son zuwa gidan ku wallahi mutum baj fitowa ba a bashi wani abin karuwa ba gashi kuma kaci ka koshi farat inna tace to yar mayunwata fada mata gidab ku gidan tallakawane. Ji inna meye yanzu matar yaya bata sani ba game damu saidai idan mutanen gidansune basu sani basu ni dai na fita na barsu da shirmen su. Ina mamakin yadda Ahmed ya fito cikin cikin wanan matar haka halinshi ya fito daban shi kodan bai tashi tare da ita bane oho don dana biye mata ko da safe da mun kwasa tana fada da yaranra kan sun kwana part dina tana fadin wai ana dauke masu hankali da kallon banza da zai lalata masu tarbiya Kai haba inna wani irin bata tarbiya mutanen dako yarensu bamuji kuma ba irin tufafin mu suke sakawa ba don Allah ya horewa yaran nan ta baki basu da kwabo ko kadan. Shiru yayi yana sauraren abokin nasa har yakai karshen magana kafin ya dago ya kalli sauran dake saurarensu sukace kwarai kuwa don ko gaskiya Alh jauro ya fada. Duk yadda mukaso muzo kusa dakai a lokacin matarka dama kai kanka baka yarda da hakan saidai aimu bamu kika ba don ko yaushe muna tare dakai don munsan hakan bayin kanka bane. Duk abinda kake yi alama ya nuna muna ba a cikin hankalinka kake muna mun so mu share zancen ka mu zauna a inda Allah ya ajemu saidai a yadda muka taso dakai mun kasa hakan gareka. Badon komai ba sai sanin cewan da mukayi cutar dakai zasuyi a karshe don badon Allah suke tare dakai ba kuma gashi duk yan uwanka sun kawo ido suma sun saka maka duk da sunsan gaskiyan zancen suma sunyi fushi dakai a yanzu subar zancen ka. Idanunshine ya ciko da hawaye lokaci guda don jin zantuntukan da abokan nasa suke fada a yanzu yaushine mace ta mayar hakan a cikin yan uwasa da abokanan sa lokaci guda. Yanzun dai mu godewa Allah dayasa ka gane hakan da wuri tun lokaci bai kure maka ba don da ka mutu a cikin halin gaskiya akwai matsala babba. Aishi mutum mai alheri Allah baya barinsa haka dama don ko sun hanaka komai basu hanaka alheri ga mutanen makwabtanka ba. Wanan ma ya isa ya taimaka maka ka fito daga kanginsu don ba haka sukaso gani a gareka ba sunso suga sun rabaka da kowa a garin nan. Yanzun dai ba wanan ba yaya zancen da muka fara dakai a waya na yaron nan don ya kamata ace zuwa yanzu kasan matsayin da yaron nan yake ciki. Fuskanshi ya shafo don maganganun nasu sunyi masa yawa a kai duk da dama yasan dasu abaya amma yanzun da yake kara jin hakan a bakunan su sai yake jin zancen kamar sabo a gareshi. Sun dauki lokaci a tare dashi har zuwa magariba kafin zuwa sallah bayan sun fito kowa ya nufi wurin iyalinshi akan da safe zasu fito su rakashi zuwa wajen yan uwan nasa na haihu. A cikin gida kuma itama hjy mariya mamakin abubuwan dake faruwa sai take ganin abin yau kamar a falki yake zuwa mata ba gaskiya bane yau mijin nasune yazo gareta shi kadai ba tare da matarshi wani lokacin da yaransu da basu da kwabo ko kadan. Zasuzo su mayar da ita kamar yar aiki agidan sai sun tafi take samun sa,ida a rayuwanta don hakanema bata kaunan zuwan nasu saboda cin fuskan da ake mata din idan sunzo. Ya shigo gidan bata saba idan yazo ta sameshi ba kamar yadda ko wace mace ke samun freedom da mijinta idan yazo sai gashi ta kasa zuwa gareshi. Sai shi din ne daya fahinci hakan ya taso zuwa gareta sai taga abin wani irin bambarakwai a gareta don haka lokaci guda ta rude da ganin shi kai duniya.