← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 286

Sashe 195

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Don Allah ayi hakkuri abubuwane sukayi yawa dole na dakatar da rubutun na kwana biyu yasa bakwa samuna kamar yadda muka saba kuyi min afuwa hakan ba yin kaina bane yan uwa.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Abinda ya baka tsoro wata rana sai ya baka tausayi don kuwa wanan karon kuwa ta juyewa hjy Yabi matuka a gidan fafir Alh ya kafe akan sai ta bar masa gida tunda ya furta hakan .
Gashi sai faman kiran duk wanda tasan abaya yana jin nauyinsu tana roko da a bashi hakkuri amma amsa dayane don Allah wani ka gafarceni .
Banaki bin zancen ka bane amma dole sai yabi tabar gidan na na wata daya ko hakan zaisa ta koyi hankali nan gaba ire iren bayanan dake yawan zuwa mata ke na a bakunan mutanen data tura su bashi hakkuri.
Don sam bata taba tsammani da cewa akwai wani ranan da irin haka zai zo mata a rayuwa ba sanin cewa tsaye take kyam a gidan da kuma kan al,amarin mijin nata ba irin jinin da bata bayar ba akan sha,anin mijin nata.
Yau sai gashi tun bata kaiga ganin cikar burinta ba abubuwa suna son juya mata baya a cikin dan kankani lokaci haka gaba daya abubuwa sun rikicewa rayuwanta.
Bata da zabi dole ta sauke komai da takeji ta zubar da makaman yakinta ta kwatawa makiyanta ta samu tayi amfani dasu duk da cewa suna cikin lissafin mutanen da bata kauna a duniya ta gansu kusa da mijjnta kuwa.
Alh jabbo dole su zata kira don sune mutane na karshe daya rage ta jeraba sa,anta garesu ta gani ko za ai sa,a yaji maganan su a matsayinsu na abokan,nan sa kuma aminansa tunna zamanin kurciya da har yanzu suna dan biyewa junansu din.
Duk da ita din a yanzu tayi wani kokari da zatayi na ganin cewa ta raba alakan dake tsakanin shi dasu don ganin cewa a yanzu shi din ba ajinsu bane .
Abin kunyane a gareta dashi mijin nata a dinga ganinsu tare dashi a matsayin da a yanzu Allah ya kaishi din nan na zama fitacen dan kasuwa mai fada aji a cikin gwaunatin zamanin.
Don haka tayi duk wani kokarin ganin cewa ta raba tsakaninsu din su hudun ta fitar dashi daban a cikin su tayi kuma nasaran yin hakan yanzu sam ya daina ko zancen su arayuwan shi a yanzu.
Sai gashi yau ita da kantace mai bukatan taimako a garesu don gaba daya duk wani dabara nata ya kare don barin ta gidan kamar yadda ya umurceta dayi wani gazawane a gareta yanzu duniya zasu gane halinda take ciki dashi a lokacin.
Dole uwar naki tabi shawaran yar uwanta data samo mata layin wayan shi Jabbo ya dauka tare da tambayan waye don jin muryan mace da yayi a lokacin.
Da kyar ta iya amsawa cikin isa da takama da izza tana fadin kana magana da Yabice daga Abuja sunan ya fara maimaitawa a bakim shi kafin yace bai san wata mai wanan sunan ba gaskiya.
Ta fahinci iya gaskiyan shi kuma yana kokarin kashe waya yana fadin wrong number tace daga gidan dan gaske nake magana dakai ta juya harshe cikin filatanci yadda zai fahince ta.
Yace yabi dai yabi matar dan gaske ko watace dai take kwaikwayon ta a yanzu tace ita dince sai taji yace dewa,ya, i.
To hjy yabi badai wani laifin nayi ba har kike nemana a yanzu duk da kauyancin shi ya isheta a lokacin amma haka ta daure tabiyewa wautanshi din take fadin a a ha wallahi nice dai ma nayi maku laifi ai kasan halinmu na mata da rashin tunane .
Na taba abokin kune yake fushi dani nace barin nemoku ku tayani bashi hakkuri don Allah don nasan yana jin shawaran ku idan kun bashi hakkuri din in yasa daga baya zamu magana daku musan abinyi a karshe zakuji sakona insha Allahu.
Jam jam meyasa ku masu kudi kuke tunanen cewa saboda kudi duk wani tallaka zai maku komai sai ku manta da zumunci da alaka irin ta addine akan zama tare.
Duk da ke matar tsohon abokinane kuma dan uwa a gareni, haka kuma aminina acan baya, duk da nasan irin abubuwan da kikeyi na ganin kin raba tsakanin shi da mu a tinanen ki shiya wuce ajin mu kamar yadda kika sha fada mana a baya din.
Tun bamu gane mai magananki ke nufi ba har mukazo muka gane gaskiyan zancen ki garemu muka kuma tsaya a matsayin da Allah ubangiji ya ajemu don musan dangaske ba finmu yayi ba a wurin Allah shi kadai yasan wanda yafi a wurinsa.
Kuyi hakkuri don Allah kuskurene amma ba wai haka nake nufi bani son Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru ta kara fada a karshe.
Bakomai don daga mijin ki har ke bamu taba daukan ku da wani manufa ba a yazuciyar mu har yanzu a matsayin yan uwan juna muke kallon ku a idanun mu.
Nagode dama nasani shiyasa yanzun ma na kiraka don nasan ku kadai zaku iya shawo kan Allah ya janye maganan da yayi a kaina don Allah.
Ikon Allah harmu dinnan mun isa mu shiga tsakanin ku da Alh saidai mu dan gyara idan muga da bukatan hakan a tsakanin ku.
Zuwa lokacin yakai mata iya rai tana jin haushin sa yadda yake jan maganan tana tsawo kamar ace yana kusa ta makeshi dai da wanan iya yin na samun waje da yake mata din.
Nan dai ta daure ta koro mashi komai daya faru tsakanin su akarshe ta nemi da ya roka mata shi kada ta fice daga gidan kamar yadda ya bukata da tayi bayan bata mashi rai da tayi kan girkin dare data lalata.
Ya nuna mata laifinta tare da mata alkawarin kiran abokin nasa akan zai masa magana tayi mai godiya ta kashe wayan tana tunanen lalai abu ya baci gareta wai yau itace don lalacewa har take neman taimako a wajen wa yan nan mutane.
Shiyasa manya ke fadin wayasan gobe banda Allah ko a cikin yan kwanaki tana ganin kantane a matsayin macen da tafi kowa iya kama miji ta kammalashi da asiri sai abinda tace zuwa gareshi zaiyi.
Saukan safe sukayiwa kasan amma duk da hakan a nan suka samu wanda sukazo taronsu tun a jirgi yaso ya gane cewa bashi kadai bane a wanan tafiyan sai dai ya saka ido yai shiru yana kallon ikon Allah.
Ga wanda yazo taron su din a nan ya gane don sunayen su dake jere a wuri daya lokacin har su biyar maza hudu mace daya.
Bayan gama binciken su suka nufo wajen fita a nan suka samu mutum biyu suna jiransu sukai masu jagora zuwa wajen motocinsu na suka shiga aka kara gaisawa.
Sai kallon kallon sukewa junan su don ganin nisan tafiyan da sukayi a tare bada sanin cewa wuri daya zasu je ba sai a wanan gaban suka san cewa ai duk tafiya nasu dayane a lokacin.
Wani babban gina suka nufa bayan sunsha dan tafiya zuwa cikin garin suna baza ido wurin kallon abubuwan mamaki da suke gani.
Shiru Ahmed yayi yana fama tunane tare da ganin wautanshi na yarda yayi wanan tafiyan gashi bai fadawa kowa abinda zai tafi yi ba a lokacin haka kuma ya dauko hanya yabar garin har kasan zuwa amsa kiran wanda bai taba sanin shiba da sunan taimako.
Ganin tafiyan nasu wuri dayane yasa suka fara sake jiki da junan su inka debe Ahmed wanda yafi kowa takura a cikin su don gani yakeyi shi tasa ta kare ke nan daga nan.
Komai na wajen kusan da fari da blue akayishi blue mai hasken sararin samaniya sai wani tambari dake jikin ko wani gina na unguwar .
Da alaman ansan da zuwan su don suna zuwa wani bature ya taso yana gaishesu tare da fadin Najeriya suka amsa mashi da eh yace su biyoshi nan ya jasu zuwa dakunan da zasu sauka din dakina da a gida sai sarki ko wani hamshaki kawai zai kwana a cikinsa .
Sai gashi nan an ba kowansu nan ne masaukinsu na tsawon kwanakin da zasuyi a kasan har tafiyansu shikan wanka yayi ya dauro alwala tareda fargaban ta ina zai duba a wajen sallah a kasan.
Allah da ikonsa sai ga taswiran nuna yanayi ya hango makale a dakin ba bata lokaci ya tada niya yayi sallalolin dake kanshi da baiyi ba.
Yana gamawa duk da yunwar da yake ji a lokacin hakan bai hana wani barci mai mauyi ya daukweshi ba sai karfe hudu da wani abu na yamma ya falka daga barcin nasa.
A dan razane ya falka daga barcin yake bin dakin da kallo kafin tunanen shi ya tuno mai inda yake a lokacin hakan yasashi saukowa saman gadon da sauri yana dan dube dube lokaci guda.
Wurin window din dakin ya nufa ya dan daga labulen yana kallon wajen wurin zuciyarshi cike da mamakin komai na wurin don zakace ba hannu bane yayi aikinsu haka komai sai ya burgeka idan ka kalleshi.
Kofan yaji yana kara hakan ya dawo da hankalinshi zuwa inda yake jin kukan na fitowa koface alaman akwai wani a kofan dakin a lokacin karan bani yayi yai amfani da abinda ya gani a rubuce jikin kofan ya bude kofan lokacin.
Wani mutum ne tsaye a kofan dan gajere ya dan fara manyanta yana tsaye dauke da kayan abinci yace Mr Yusuf ya amsa masa da kai yace abincin rana na kawo ma tun safe muna zuwa muna samun kana barci.
Bayan tafiyan mutumin ya bude abincin ya irin abincinsune nacan don haka ya dan taba kadan don babu dadi a bakinshi irin yadda ya saba cin namu.
Bayan gama cin abincin ya dan fito ya zaga saidai bai yarda yayi nisa sosai ba don kada ya bace ya kasa gane dakin nasa.
Hutun kwana biyu sukayi kafin a sanar masu da taron da zasuyi washegarin ranan don haka kowa ya kwana dashiri sunawa Ahmed din kallon bakauye wanda baisan komai ba.
Sai gashi ya barsu da mamaki kan tambayoyin daya amsa masu a wurin interview din ya bar kowa da mamakin hakan don yadda ya amsa masu tambayoyin nasu basu zaci hakan ba daga yan kasan nan.
Lafiya dai wanan kiran haka cikin wanan daren don ban taba zaton hakan daga gareka ba Jabbo .
Murmushi yaji yayi tare da fadin kiran ya kamane na kiraka a yanzun din idan ka duba da cewa ban taba ma kira a cikin dare ba haka ai.
Murmushi ya sauke kafin yace nasan dai duk kuna kusa da wayan ke nan tunda naga ka kirani a yanzu din kwarai kuwa kusan kowa na wurin nan in an debe kaida baka kusa damu.
Sai ya kwashe da wani irin dariya wanda ya dade baiyi irinsa ba don fadin hakan ya tuna mashi da wasu abubuwan kurciya da suka faru dasu a baya suna yara.
Ba wanan ba yanzun dai mun kirakane mu baka hakkuri da shawara ba tare dayin binciken komai kayi hakkuri da mai dakinka don Allah.
Au har can kuma takai karana lalai yabi tana da alaman tabin hankali tunda har ta iya rufe ido wai tana neman taimakon ku a yanzu ?
Yaushe idan ita mai hankaline har zata iya tunkaranku kan zancenta dani matan da da karfibda yaji ta rabani da kowa na kusa dani da aka sanni dasu tun farko.
Ba abinda yake ci mun rai a yanzu kamar zancen ysron nan dana baro zamfara a baya koda an gashi yanzu da wani ido zan kalli yaron nan shida iyayyensa har in yana raye.
Abinda ya wuce abar tunashi sai hakkuri da istigifari don neman yardan ubangiji ga bawa amma duk ake tuna irin wanan abin ba zai taba wucewa a zuciyar mutum ba ai.
Amma kasan ko komai ya wuce zancen yaron nan ba zai taba barin zuciyana ba don bansan da wani ido zanwa Allah bayani ba a kanshi.
Jabbo kasan ba karamin cutana yabi da yan uwanta sukayi ba yanzu gashi duk wanda na tura sai ya dawo yace min wai ba a gane komai ba game da yaron da iyayyensa ba.
Don haka yadda ta rabani da kowa nima a yanzun banson ganinta gidanan ta fice min daga gida ko zan samu sallama a rayuwata.
Zaka samu insha Allah kaidai ka kwantar da hankalinka yanzu idan ja yake hukunci a cikin fushi ai baka kaiga cinwa manufarka akanta ba ke nan idan Allah yayi yaron ka ya baiyana kaga bataji komai ba game da dawowan nasa.
Ga hjy murja data dawo yanzu shima ba wani zama sukayi tare da da zaisa ta fara nadaman abinda takewa mutane a baya ba don haka kayi hakkuri ta zauna dakinta don Allah.
Zata zauna amma wanan karon ina son ta fara dandana irin abinda naji a kanta itama don haka kona sati dayane sai ta bar gidan nan taji itama in hakan yana da dadi.
Zata bar gidan na kwana biyu kawai tunda kace hakan amma na sati daya gaakiya yayi yawa to shike nan ta bar min gidan nawa shine kawai saukin zuciyana a yanzu game da ita.
Dole hakan akayi saidai bata dawo gida ba nan ta zauna a Abujan a cikin wani gida nata data saye boye yana jin hakan yace ai idan ba gida garinsu ta koma ba akaje can akai magana ba zata taba dawo masa gida ba.
Gashi wanan tafiyan ya bashi daman tone wasu abubuwa data binne a gidan dama aikin da kowa baisan lokacin da tayi shi sai hakan ya kara sashi cikin sallama yake jin tankar ace hjy yabi din ta tafi ke nan daga rayuwan shi har Abada.
Chapter 195 · 0% Book details