← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 286

Sashe 178

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

mashi sallama ya amsa na dora da ina wuni ya amsa da lafiya lau kun fito break ke nan ? Nace eh amma yanzu gida zan tafi don ba zamu zauna karatun yamma ba yau yace test zamuyi OK idan kika koma don Allah kada ki kula duk wani abinda inna zatayi maki don Allah nasan har yanzu tana jin zafin zancen daya faru da safe tsakanin Ku. Kai Waya fadama hakan sai naji yayi murmushi kafin yace au had kin manta na kiraki a ways lokacin kika bar wayan kunne da sunan zaki gaisa da Dije a lokacin don haka ban kashe wayan ba ai lokacin. Naji koma naji duk abinda ya faru had amsa da kika bata dan haka banson wani zance kuma ya kara tasowa son run dazun nake son kiranki nasan kina class lokacin. Ni ya wuce ai a wuri dama kawai don ta gane na bata amsa ai kuma shike nan ai yace na sani don Allah ki bar tankawa daga yau don tana sane take komai ai. Kayi hakkuri idan hakan ya bata min yayi murmushi yace is OK mashin zaku hau yanzu ke nan ko nace eh don yau Nabila bata shigo ba nake gani motarta baya nan. OK ki kulamin da kanki nace nagode harga Allah banji dadin da yaji wanan zance ba don ba komai nake son ya dinga jiba tsakanin mu muna gama waya dashi na mayar ke nan a jakka sai naji wani kiran ya shigo again Na dauka shine kuma a lokacin ya sake kira said naji ummahce ashe dana dauko na dauka da sallama ta amsa ina kokarin gaida ita naji tana fadin. Kina school din be had yanzu nace eh ummah amma yanzu make son in koma gida min tashi ke nan race to ki kira Aisha da mamaku kiyi masu gaisuwa . Don yarinyar nan jaririyar ta koma dazun aka kaita da sauri na furta innalillahi was inna alaihim raji,in yanzu yar nan ta rasu ummah ashe ? Have eh wallahi kamar dama jira take ayi suna taiwan uwarta bara yadda aka fada son jiyama basu kwana a gida ba saida suka koma asibiti da ita a can ta cika. Nayi mata adduan dacewa da Rahaman Allah ga musulmi nacewa ummah yanzu zan kira Aishan insha Allahu mukayi sallama ta kashe wayan nata. Jikina yayi sanyi sosai ina dago kai hannatu na fadin yar Aisha ce ta koma ko nace wallahi a cikin wani irin yanayi murya a raunane . Dama ai yana da wuya ta rayu irin hakan sai in yaro rabone zai zauna bayan ansha wahala karshe kuma ya taso a wahalce da ciwarwuta iri iri a jikinshi. A hankali muke takowa data cikin school din muna maganan sai ga motar motana na gani ta gitta muna nabi motan da kallon mamaki. Hannatuce ta rigani magana da fadin ikon Allah wancan kamar motarki zahra nace itace wallahi waye ke janta ciki nace naga kamar sanusi ne dan yayan mama dama dan dakintane shi sosai zakace shidin ma Dan gidan mune shi. Kai wanan mama din gaskiya ba mutumiyar arziki bace yanzun mortar naki zata dauka ta ba dan uwanta bayan kowa yasan nakice dama taje su hau hannatu meye duniya baki dayanshi ma balls mota da zai lalace. Wallahi ummah ta riga da tace koda andawo da motan ma bazan haushi ba ko hakan zai zama sanadin aurenta da Abba kuwa to kinga me zai dameni no yanzu da ita duk mai hawa ya hauta ba abinda ya dameni a yanzu. Shiru tayi kafin can kuma tace dani amma wuri ta samu ina ji a gari ana fadin ko wanan amaryan Abba din yanzu hjy mama ta shiga gabanta amma fa yadda mutane ke fadine fa. Murmushi nayi bance komai to waike zahra irin matan nan basu tuna cewa zasu mutu su koma ga Allahne wai mutum ya rungumi duniya yasa a gaba irin wanan halin me zataje ta fadawa Allah akan hakan ne wai ? Kofa bata mutu ba zata iya tsufa ko ta nakasa kinga duk abinda tayi din nan ya tashi a banza yanzu ai gara mu biya ta gida muyi masu gaisuwa ko ta fada jin tana ta magana ban bata amsa ba lokacin. Bari to na kira master in fada mashi na fada ina kokarin zaro wayana daga cikin jakata lokacin wanan Sanusin ya kara fitowa daga cikin makaranta ya kwaso wasu yan mata yan UG two a motan suna tafe suna shan kida sukazo suka wuce mu kamar farko. Ina jin hannatu tace wallahi Allah ya isa dan iska dakai da uwar dakin naka sai kunyi kunya tun a nan duniya in Allah ya yarda wani irin dariya ta bani lokaci guda har ya dauki wayan ban sani ba ina karawa naji yana fadin a ina kike kike wanan dariyan kamar an maki bushara ? Wallahi hannatuce take zagan min mama da sauri naji yace subbahanallahi wace maman naki ciki nace wallahi mama da mama ta gidan mu wai kawai don taga wanan sanusi din dan yayanta a cikin motana yana ja ya kwaso yan mata keja masu Allah ya isa. Sai naji yayi murmushi yace kai hannatu bata rabuwa da shirme wallahi ta bari idan nayi kudi in saya maku motar daba me karbe muna saidai Allah. Balle har wani gardi ya hauta wanan tamu dukane yanzu tunda na Abbane kowa yana da right din da zai hauta yanzu namu nan zuwa da yarda ubangiji. Murmushi nayi tare da fadin Allah ya nufa saidai kada ai kudin sayen motan aje a dauko min wace zata hanani zaman lafiya dakai kuma. What ya fada da karfi nayi murmushi tare da fadin nawa akayi muna gani dama tunanen ki ke nan zahra a kaina bari anji mu karasa mun samu dan mashin yanzu zamu shiga na bashi amsa na kashe wayan ina murmushi.
Chapter 178 · 0% Book details