← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 286

Sashe 234

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

asalima yau sun gane cewa itace na kwaso a kammani. Har suka fito suna zance akan yanayin gidan mu duk da sun gani a idon su hakan bai hana su aibanta uwata ba wanda innace keta zuba akai har suka hau mashin suka dawo gida wanda anan ma dai saida suka dan taba gulma kuma kan mama don yadda take watsa masu kallon banza a lokacin yaciwa abokan na inna rai sosai inda wasu ke fadin mu dai aiko yama uwar sarakuwarki take a gidan mu tafi muna wanan nakasassan matar uban nata dake wani jiji da kanta ga mutane. Don gaskiya ummah ta nuna su natane don ta basu kullawa sosai a dakin wando ko kallon arziki mama taki tai masu sai kallon su da ta dingayi a wullakance karshe ma kamar ta matso da su fice daga dakin don ta fara fadin anyi yawa a dakin lokacin yasa suka mike suna Allah ya sauwaka suka fito. Hakan ne mafarin fadin maganganun su har dayan ta tsaya tana fadin abinda idonta ya gano mata a cikin ahalin namu . Bai dawo gidaba sai bayan magariba inda yazo ya daukeni da abincin da nayi muka koma asibitin don duba jikin na Abban mu da a yanzu yaji sauki sosai saidai karfine da baidashi har yanzu din. Don a gaskiya matsalan shi da hjy karimace duk ya haifar masa da wanan matsalan don ba karamin barna hjy karima din tayiwa Abban sanadinsa ba a lokacin. Wanda har hakan a yanzu yake barazana a cikin arzikin Abba din saidai bai fadawa kowa hakan ba amma ita ummah ta riga data samu labarin komai ta hanyar aminiyarta dake can Abujan. Wanda itama tajine a wurin mijinta har take sanar da ummah din halinda mijin nata yake ciki ita kuma taja bakinta tayi shiru bata yarda ta fadawa kowa ba balle ace a bakinta akaji. Sai gashi hakan ya tabbata don yadda Abba din ya dawowa iyalan nasa abin yabawa kowa tsoro a lokacin amma sai suka dauka cewa ciwone ya kaishi ga hakan daya zama a yanzu din. Bamu dade a wurinsu ba don ummah zasu tafi gida a lokacin su hamza ne da mamah zasu kwana dashi saboda mamace da girki yamma a ranan ta fake ga hakan don alaman hakan data nuna har ummah din ta gane me take nufi. Amma sai ji nayi master yace ummah don Allah zan samu a sauke min zahra a gida don zan tsaya har a sakawa Abba wanan ruwan daya rage kafin na koma gida. Ikon Allah mu meye amfanin mu a nan din da har saika tsaya a nan din No ki barshi tunda hakan ya tsara ai ba a hana mutum aikata alheri ko banza yana debe min kewan su musa da basa nan a yanzu don yadda yake nunawan nan gareni. Dadafa dama nasan za a rina tunda naga hakan yana gudana amma su musa da jafar kasan sunfi wanan din matsayi dai a hakan donshi surikine kawai yarka yake aure ko ? Hjy Maimuna wanan maganan da kikeyi a gaban yaron nan bana jin dadinsa ko kadan don kawai ya nuna kulawanshi a matsayin yaya na uban matarsa shine laifinsa a yanzu ? Donshi bai dauka a yadda kike zato ba da zuciya daya yake komai da yakeyi a nan din kuma iya kulawan da zai nuna ke nan asan yana da tarbiya ai da nuna kulawansa. Gwaggo shaface take wanan maganan tana kokarin saka hijabinta a wuyanta jin abinda ta fada din ya sosawa mama da yaranta rai daga can baba haruna yakarbe da fadin nima hakan dai naso gani . Don yaron gaskiya ba laifi yarone ko banza mai mutunci da sanin girman manya shi bawai yana hakan bane gaskiya don wani abuba shidai halinsa ne kawai hakana. A wurin mama taso ta rufe idanu taci masu mutunci yadda ta saba yi amma sai Abba din ya dakatar da ita ga hakan yace a, a fa hjy maimuna. Meye illan yaron nan yanzu ina ke kika karfafa aurenshi da maahmah lokacin dana hana nisai na dauka yanzu ai ashe kirkin nan nasa da kikagani yasa kika matsa na bata shi tunda ta nace akansa din lokacin. Amma kuma yanzu kina kokarin fadin abinda ba daidai ba akan yaron don an fadi gaskiya meye laifin yaron nan yanzu kuma gareki. Donni sai yanzu nakema alfahari dabawa zahra shi da kika saka nayi don yafi min wa yancan mazajen nasu Rukkaiya mutunci don shi ko wani zuwa nayi zai shigo ya gaishe balle mijin Aisha dako ganinsa ban ma taba yiba ni har wanan lokacin . Ai hakan abin alfaharine a gareki don kece kika bada goyon bayan na aurawa ita zahra shi ga kuma auren yayi amfani tunda ba a jin tsakanin su ai hakan abin alfaharine. Dakin yayi tsit lokacin da Abba ke wanan bayanin idon mama ya kara rufe lokaci daya taji wani bakin ciki ya tokare mata makoshi ta bude baki a zafafe ta fara fadin. Yanzun kuma zakace mijin zahra yafi na su Aisha kirki ko me don wanan shishigin daya fara yima a yanzu shine kirkin dayafi sauran ? Har ni zaka dorawa wanan alhakin kace nice nace ka daurawa zahra aure dashi saukin abin mara asaline daishi sai kabi a sannu don tsuntttaciyar mage bata taba zama magen kwarai. Har idon ka ya soma rufewa da dan wanan halaiyan da ake nunama dama nasan an kulla wani abin ne tundazun danaga yana wanan rawan kan na munafuci gareka ai. Su wa yan nan da kake kokarin ganin laifinsu a yanzu sune dai din sarakan naka na asali wanda kasan uwarsu da ubansu gari kuma ansani koda yakema tsayawa fadan hakan yanzu ai bata bakine don ita gaskiya gudace. Murmushi Abban yayi yace wai meke damunkine haka maimuna kan yar cikin ki yaya balle yaron nan ba shege bane da uban sa kilama kaida kake Abuja zaka iya sanin mahaifinsa ai. Wanan Alh Abubakar dangaske mai company oil and gas da kakeji shine mahaifinsa shine dana farko a wajensa wanan matsalan dai da suka samu da iyayyen ita mahaifin yaron shine kawai ya jawo matsala a garesu nakin yarda tabishi a lokacin da zai koma gida. Ummahce take fadan hakan cikin kunan rai ita da gwaggo shafa don cin fuskan da mama din keson tayiwa Ahmed din a wajen saboda in indon mama ya rufe kowa tana iyaciwa mutunci lokaci daya ita haka halinta yake saboda irin izzanta. Dakata Salma wai kina nufin dangaske mai kanfunan nan na Abuja dama shine mahaifin yaron nan tace kwarai kuwa Alh don yaron shine na farko daya haifa a nan. Nayi mamakin wanan bayanin da ummah take yin don ban taba tsayawa na fada mata komai daya shafi Ahmed din ba irin wanan saboda wauta irin nawa a lokacin. Shiru dakin yayi kafin mama tace wata sabuwa ke nan dansa ko dan dan uwansa ba balle wanan tazo mujitane kawai akeyi don gyaran zance kila dan dan uwasa nema ake fadan hakan. Kai Abba ya daga yana kallon Ahmed din da alokacin yana tsaye bakin kofa ba wanda ya farga da shigowanshi dakin sai Abban da fuskanshi yake kallon kofan dakin shi zaiga mai shigowa a lokacin. Hannu yayi alaman ya karaso yasa kowa ya juya yana kallon kofan a daidai lokacin wasu hawayen bakin ciki suka fara zubo min a idanuna. Kai din ashe dan babban mutum ne irin Alh Abubakar ka tsaya a haka ana barna maka suna a nan don me baka koma gun mahaifinka ba don asalinka ya gyaru. Tsayuwa ya gyara kafin yace hakan ra,ayinane Abba amma kwanan nan zamu koma can don zan bar nan din saboda na samu aiki a karkashin UNICEF don haka ba zan bar zahra a nan in koma kasan waje ba sai idan ta kammala karatunta zan dauketa mu tafi tare. Allahu akbar Allahu akbar dama haka yake a wurin Allah baba Ado ya fada daga inda yake tsaye din yana sauraron cin mutuncin mama da takewa surikin nasa a lokacin. Kafin ya juyo yana fadin to maimuna kinji kinji yanzu da kanki akan yarmu duk yake wanan batda sau din don irin ku masu mumunan fassara da akidan banza yanzu kinji gaskiyan koshi waye a bakinsa ko ?
Chapter 234 · 0% Book details