← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 286

Sashe 172

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

fadin lah kaine kana ina haka duk dadewan nan bamu kara jin kaba kuma ? Yace ba kun koreni Naija ba kedasu Mum nace kizo mu gudu muyi aure kinki bina lokacin da sauri na tareshi da fadin haba dai brother in ace ciki daya muka fito dakai nayi haka yaya zakaji ? Yace to meye tunda kinbi masoyinkine bazanji komai ba saidai in maku fatan alheri a duk inda kuke nace yare hoo a zuciyana wani yaren duk da musuluncinsu sai sin hada da al,ada mai kama da kafirci. Amma kasan addinin mu da yaren mu bai yarda da hakan ba garemu don me ni zan ba iyayyena da yan uwana kunya a garin mu saboda namiji ? Yace hakan dana sani yasa nabarki ai badon naso ba don lokacin inada hanyoyin da zan iya saceki cikinsu din amma sai kwanan nan mummy ke fada min wai kunyi aure keda sisters dinki. Ke kin auri wani tallaka bawa Allah kika zaba akaina sam baji dadin yadda take fada min yanayin da kike ciki ba tana jin dadin hakan. Wanan abin ya bata min rai sosai wallahi don nasan yadda kike da step mother din ki Alajah komai zata iya akanki don hakane yanzu na kiraki naji wani taimako zan iyayiw rayuwan ki a yanzu. Ke zan taimaka ko mijinki zan taimakawa ya samu abin rikeki yanzu ke nake saurare naji amsan da zaki bani da fatan kuma shi mijin naki yayi karatun gaba da secondary ? Shiru nayi ina sauraren shi don na rasa amsan da zan bashi saida yace kina tare dani kuwa nace ina jinka duk a cikin harshen turanci muke magana dashi lokacin. Yace wa kika zaba a cikkn ku nace idan zaka taimaka min ka taimaki mijina don ya fini bukata yanzu yace good nima tunanen da nayi ke nan da farko amma kuma sai nazo nayi tunanen kanku hausawa don mazan ku basu da rikon amana ko kadan . Yana iya cewa zai rabu dake wata rana idan ya samu wata kinga ya kwaremu a nan ke nan don haka naga gara ke ki samu din don daman mutum daya nake dashi yanzu kuma na tambaya ance har yanzu karatu kikeyi ke. No ka bashi banda matsala ga hakan idan ya samu kamar nice na samu ai don zai tallafa min yadda ya kama daidai gwargwado don ko yanzu yana kokarin shi dani ai. Ok alama dai ya nuna kina matukar son mijin nan naki ba laifi zan turo maki da yadda zaku turo da takardunku saidai bana son wani ya taba sanin cewa nine na taimaka maku da wanan aikin understand nace nagode sai naji ya kashe wayanshi a lokacin bai kara fadin wani magana ba kuma. Kallon wayan nayi na runtse idanuna gabana sai faduwa yakeyi sosai ina kuma tunanen wani irin aiki bisi din ya samu yanzu da har yake ikirarin taimakawa wani dashi. Sai kuma na koma fadin ni yanzu ta yaya zan fitowa Master da wanan zancen me zan fada mashi alakata da Bisi idan zancen hakan ya taso a tsakanjn gashi kuma damace muka samu a hakan kada ya wuce mu duk da bansan ko wani irin aiki bane dai. Amma zan gwada mai magana don haka na fara dan tsara yadda zan shirya mai zancen ko kadan banzan taba furta mashi zancen cewa Bisi din yaso aurena ba a cikin maganan. Zan dai nuna mashi cewa dan abokin Abbane da muke mutunci dasu yaji labarin baya aiki yake son ya taimaka muna haka dai na zauna na tsara yadda zan fada mai koda yayi min tambaya mai zurfi kafin na dawo ga tunanen mommy Bisi data fada mai tana jin dadi. Watau hakan ya nuna mama tana jin dadin halin danike ciki ke nan to ai ba wani zunubi na aikata ba da har Allah ya jarabeni da auren master din na tambayi kaina. Ina cikin wanan tunanen ne kiran master din ya shigo a waya na dauka muka gaisa nayi mai ya hanya yace Alhamdullahi ya isa lafiya har sun fito daga lacturen ranan ai. Ya tambayi lafiyan iyayyen shi nace kowa lafiya sai Dijece bayan tafiyan ka take fama da zazzabi yanzun ma nake shirin zuwa in gaida ita in tambaye abinda zataci in girka muna. Da sauri naji ya tambaya badai sosai bane jikin ko nace da sauki gaskiya don har ta fito dazun da rana yanzun daine ban kara lekata ba yanzun nake shirin zuwa to idan kinje son Allah ki min flashing zanyi magana da ita. Nace to naji ya kashe wayan lokaci guda ba tare da munkai ga yin maganan ba saidai kuma zancen ya tsaya min a raina sosai ina tunane har yanzu kan in fada ko kuma in kyalene. Ya samu abokan nasa su uku dama wasu abokan arziki nasa duk sunzo tariyanshi a lokacin ba bata lokaci suka dauki hanyar mambila suna isa garin hjy yabi wace yarta ta bata shawara kan . A yanzu kuka ko bacin rai ba nata bane ta sake jiki ta nuna mashi cewa tayi kuskure a baya ta nuna ba komai don haka ta daga waya ta kira layinshi. Baiki dauka ba ya dauka take fadin kana ina ne haka ko abinci bakaci ba kafita ba bai tsaya jin komai ba shima ya bata amsa kalar makircinta da fadin ina mambila yanzu. Baki sake take fadi a rude mambila Alh mambila ka tafi banda labari nan hankalinta ya kara tashi don gani take idan yaje mambila ba tare da itaba dayan kishiyar nata zata samu dama a gareta ke nan. Asalima itace ke shirya masu tafiya duk lokcin da bukatan zuwa ya taso masu garin nasu sai gashi yau shida kanshi ya tafi ba tare daya sanar mata bama. Nan hankalinta ya tashi maimakon lalashin data kirashi tayi mai kamar yadda yarta ta bata shawara sai gata tana kokarin fada mai bakar magana a lokacin. Rabu da irin matan nan da suke mulki da gadara da isa idan abu ya kwace masu suna shitin zama powerles a wurin miji lokaci daya sukeyi kamar sun zare kan miji. Hakane yazu yake shirin faruwa da ita don gaba daya sai take ganin kamar duniya ta kita a lokacin ita kadai ta manta irin mulkin da isan da take shimfidawa a baya gareshi. Yanzu Allah ya fara kwato shi ya fara samun walwala daga daurin boyen datayi mai wanda dama baya tabba ga bawa idan ba rai ya kare ba gareshi. Daga bangareshi kuwa amsa ya bata da fadin banda niyar saikin sanda zanzo yau don na fara gano me kike nufi dani yanzu ya kashe wayan ya barta a cikin mamakinshi lokacin. Ranan kan zarewa tayi gaba daya sai fama kiraye kirayen waya takeyi hankali tashe duk wanda ta kira sai hannkuri suke bata kan tabishi sannu in ma asiri akai mai ba inda zaikai. Wasu kuma don daukan alhaki sai su danganta abinda fadin mariyace kishiyarta tayi wani aiki a kansu yanzu da yaci don itama aiba zata zauna ta zuba maki ido ba dama. Jin irin hakan ya kara tayar mata da hankali sosai lokaci guda duk ta fita hankalinta har zazzabi mai karfi ya rufeta nan yarta babban ta fara fada da ita tana fadin . Akan daddy mummy kike son halaka kanki ki manta dashi mana yadda shima ya nuna kodake koba ke a yanzu zaiyi rayuwa . Jin hakan yasa ta dago kai tana fadin kina da hankali kuwa daddy zakice mu kyale duk wani abinda muke takama dashi da karfin wa muke duk abinda mukeyi a garin nan yanzu. Don suwa nake wanan haukan haka ba duk a kanku bane nake wanan wahalan kina ganin idan ya dauko wanan shege dan nashi ba zai mayar da hankalinshi bane a kansa ya kyale mu. Ko kuma yayi kokarin yaga ya mayar dashi wani abu yanzu kamar ku duk komai ma zai iya faruwane akai wanan ne damuwana don ko banza kinsa yana yawan complain cewa yasir baya jin maganan shi. Shiru yar nata tayi tana saurarenta tare da nazarin abinda uwar nata ke fadi kafin ta bude baki tace duk da haka mummy ki nuna masa rashin damuwan ki da hakan zaifi sauki.
Chapter 172 · 0% Book details