← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 286

Sashe 200

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kofan part dina da aka turone yasa dukkan mu muka kalli wurin Dijece ta shigo tana fadin ina amarya ki fito ku gaisa da mahaifin naku kuma kuzo ku gaisa dashi da cewa su Aisha. Jin hakan yasa na figo hijjabin sallahna muka fita tare lokaci guda suna da yawa a wurin ganin haka yasa naji kafana yana hardewa. Daga can bayan Dije na labe ina gaidasu da zuwa duk suka amsa muna lokaci guda suna kallon mu kafin wanan tsohon yace wanance sarakuwar tawa ko yana nuna ni. Dije ta bashi amsa yace jijiga kai tare da fadin Allahu akabar duk inda kake arzikinka saiya bika yarinya sannu da hakkuri ki dan kara saman wanda kikayi a baya alherin ku kamar yashigo hannune ko gareku. Watau Alh wanan yar da kake gani itace mabudin komai ga dana don itace silar komai dake faruwa a yanzu saidai ba za a gane hakan ba don hankali baikaiwa a gane komai. Anyi gaiya da zaton kuntatawa a garesu saidai gaiyan ta alherice ga kowa nan gaba kadan insha Allahu arzikin su dayane ya dago yana kallon inna dake zaune kofan dakinta a lokacin takure don ta raina kanta da ganin mahaifin master a yanzu yadda ya koma. Shi mai hakkuri baya taba tabewa a banza don haka yarinya ki kara hakkuri akan wanda kikeyi yanzu kada zancen wani ko wata ya daga maki hankali ko kadan komai na duniya mai zuwa ya wucene ga bawa. Allah ya dawo maki da mijin ki gida lafiya abinda yaje nema a sanadin ki Allah ya bashi ke ai alherice a wurinsa da kowa nasa insha Allahu. Kan kowa dake wurin ya daure yadda tsohon ke fitar da zance a dunkule ba tare da ya nuna ga inda zancen nasa ya dosa ba a lokacin dije ta karba mai da fadin kwarai hakkuri komai tsayinsa akwai alheri nan gaba don ni zan fadawa mutane hakan . Don ko akan Amadi naga hakan a baya haka yake dawo min da kuka an kirashi da shege ko an goranta mai rashin uba mara asali wanda ubansa ya gudu ya barshi haka zan shura takalmana naje fada wasu su ban hakkuri wasu kuma su sake goranta min a gabanshi. Yau gashi da rayuwana na fara ganin haske a gare shi bayan irin kunci da wahalan rayuwa da muka fuskanta abaya tun tasowan yaron nan inba malam Tanimu gashi nan da yakan dan tsaya masa wani lokaci tun bayan rasuwan ladan zance a cikon kunci da bakin ciki yaron nan yake rayuwa . Sai ko haduwan shi da yarinyar nan gata tun haduwan sune abubuwa suka fara walwarewa a garemu yake dan samun abinda zaiyi har muka fara girki a cikin gidan nan yanzu muce masha Allah. Don dai, , , , haba Dije wanan maganan ina ya fito haka a bakinki kuma yanzu ai adai godewa Allah tunda mahaifinsa ya dawo gateshi yanzu. Wani daga cikin yan uwan kakanshi masu nuna masa tsana a baya ya fada da sauri sai Alh jauro yace dashi ka bari ta fada munsan zafin da take ji a yanzu a zuciyan ta komai ta fada daidaine don an saba masu a rayuwansu ga hakan. Balle ita zance ai gaskiyace ko bata fada ba dolece ansan zata fuskaci wanan rayuwan tunda anyi ba sau daya ba muna gani sai dace da mutanen arziki ankan samu saukin zuciya idan irin hakan ya faru da mutum. Har lokacin mahaifin nasa baiyi magana ba yana zaune ya dukar da kanshi kasa zatin shi da kwarjinsa kawai ya haska wurin ta yadda ba mai iya fada mai zancen da bai dace ba. Haka ko duba ga yadda yan uwan suke girmamashi ya isa mutum ya gane shi din wani babban mutum ne a cikin al,umma a lokacin. A hankali ya dago kai ya juyo inda nake gurfane ya dan kalleni kafin muji muryanshi a karo na farko a zamansu wurin yana fadin yarinya waye mahaifinki garin nan ne ? Jin hakan yasa na dago da sauri na dan kalleshi farine sol karfafa dashi duk da girma ya fara kamashi lokacin da ganinsa kudi da mulki sun zauna a jikinshi sun zama jinin jikinshi a wanan lokacin. Don haka dole ya tambayene haka a cikin gadara da izza da isa amma sai nake ganin ai nima idan na fadi sunan nawa mahaifin zai ji izzansa ya gushe a lokacin don nima nawa mahaifin sanane sosai a wurin suna a kasan amma ganawa tunanen. Yarinya dake ake magana wani daga cikinsu ya fada don tunatar dani a inda nake lokacin don haka na dago kaina a hankali nace Mayanan Gusau. Kallon alaman bai fahinta ba yayi min na sake fadi ina dukar da kai kasa Alh Ali custom mai ritaya na garin nan ya juya ya kalli su malam tanimu dake zaune sun zuba ido da sauri Baba sani yace rankaidade ai wani mai kudine yana zaune a abujane yanzu iyalinshi suna nan garin da zama su yace. A Abujan nan dai yake zaune yaya akayi ban taba jin hakan ba ko sunanshi a garin sai kawai naji ba dadi a raina lokacin don hakan kamar rainine gareni ai. Don jin hakan yasa na dago kai ina fadin yana zaune a maitama da zama shidin kuma yanzu business man ne a can yana kuma siyasa saboda ritayan da yayi. Masha Allah kice mahaifin naki duk mune ashe yan kasuwa hakan nada kyau sosai zan binkinta na nemeshi mu san juna idan mun koma Abujan don nima a can nafi zama idan ina kasan nan da iyalina. A raina nace tofa kaji manya sai idan ma yana kasan ke nan yake zama a Abujan da iyalinshi ke nan a waje ya faye zama ke nan zancen shi ke nufi sai naji ya katse min tunanena da fadin. Mijin naki zai dade a can ne ko ya kusa dawowa a yanzu na dan girgiza kai kafin nace nan dai da one month zai dawo kila yace idan sun gama course din nasu. Ok wani irin program ya tafi yi ke nan nace Abba bansan ko wani irin course bane yaje yi yadai ce an daukesu zuwa can din don yin course din . Sai naji yayi murmushi yace kai da kyau hakan yayi min dadin ji sosai wallahi Allah ya bada sa,an abinda akaje nema a can nace amin sai na dukar da kaina cikin ladabi don a takure nake a wurin don tambayoyin sun min yawa a lokacin. Amm,mm ko zan samu layinshi a wurinki wanda yake kiranki dashi a hankali na dago kai na amsa da ehh Abba akwai layin wayansa saidai ba a samun shi idan bashi ya kira mutum ba. Ok dama waje ya fitane ko kuwa sai nace ina ganin cikin kasanne suke kafin naci gaba yace ok dama hakane kinsan wata kila course din ba mai son damuwa bane sun zama special people ba ko yaushe bane yanzun za a samesu ba ke nan . Duk da haka ina dai son in samu layin nasane a wurina don nan gaba saboda kira sai ki ban wanda yake amfani dashi ko wani lokaci. To Abba na amsa na fada a hankali ina kokarin dagawa sai naji yace yanzu ke wani abin kikeyi a nan karatu kikeyi ko bakije gababa tukun saboda auren don shi a zaton shi ina matakin gama secondary ne kilama din yaga karantana a idonshi. Sai na dan duka ina fadin Abba ina matakin karshe ne a nan jami,an ta gusau nake karatu yanzu insha Allahu mune zamu karasa nan gaba. Sai ya dago ya sake kallona yana fadin kai dakyau ashe yaran nawa manyan gobene da mijin da matar Alh jabbo kaji wani ikon Allah a nan har yar nan kin kai wanan matakin na karasa jami,a a dan shekarun nan naki abin yai min dadi matuka a raina dolene na godewa Allah da iyayyen ki. Don yadda kike diyar mutunci da daraja suka dauki yarsu sukabawa wanda akewa tunanen baida asali da gata a tare dashi duk da na fahinci kalman malam musa kamar da gaiya suka aura maki shi a lokacin dama. Amma duk da hakan abin a gode masune a yanzu din gaskiya saboda namijin kokarin da mahaifin ki yayi wurin ingata rayuwanki haka da ilimi da kuma tarbiya don dan zaman nan namu na fahinci abubuwa a tare dake. Jeki ki kawo min layin nasa kada dare yai muna don yau din nan zamu koma da ace mun samesane a gida zamu iya kwana garin nan donshi ayanzu ko tunda bai gida don haka yau din nan zamu juya mu koma abuja insha Allahu sai nan gaba idan mun dawo. Sai dai ki sani da zaran ya dawo muka gana dashi zaman garin nan ya kare gareku ke nan don ni mutum ne meson ganin iyalina a kusa dani ko yaushe balle ku da kuka dade bama tare daku kinsan dole inso zaman ku a wajena yanzu don mu fahinci juna da ku kuma mama ta huta hakana itama yana kallon Dije. Dan murmushin yake na sake na mike kowa na kallon yadda muke maganan a cikin sake jiki dashi naje part dina na dauko wayata na fara fada masa numbers din yana dauka a wayanshi. Don koda na dawo daga dauko wayata na samu ya rabawa kowa dake wajen kudi don haka na dan ja na tsugunna ba tare da nayi wani motsi ba ina kallon yadda suke rawan jiki wurin amsan kudin daga hannunshi. Basu kwana ba kamar yadda yace sukaiwa har da makwabta da mutanen unguwa wanda rabonshi ya ratsa alheri suka tafi suka barmu cike da alheru a cikin gidan namu don koni ya ban kudin da bansan ko nawa bane a lokacin. Kuma kowa ya sa ido yaji ko ya gani na mayar da hannu a cikin hijjabina lokacin ga su Aisha na fadin wai inna kin taba rike kudi haka masu yawa a hannunki ko ? Ke ni ba wanan ba kudinsa na banza kalman daya fada zai dauke yaran nan daga nan shine ya tsaya mi Takaicine ke damun ta tun bayan dawowanta gidan da yan aminan mijinta sukaje bikonta suka dawo da ita dakinta taso ta saka tsauri ta nuna ita
Chapter 200 · 0% Book details