Sashe 257
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zance komai Alhamdullahi a yanzu shekaran mu uku master ya zamo babban mutum don kwarewanshi ga aiki da kwazo yasa ya samu daukaka a wurin manyansu suka sandashi. Hakan ya jawo mai farin jini garesu sosai inda brother Bisi shine ubangidanshi yanzu ko ya samu wasu amma dai suna tare yana bashi girmansa dai har goben kuma bai abu ba tare dashi ba. Don haka alakansu take da karfi kamar yan uwa na jini ya daukeshi goes father din shi a can shi kuma ya rikemu as a kannensa na jini saidai har lokacin mahaifiyarshi bata da wanan labarin. Don data sani da ta fadawa mama, mama kuma ta samu abin gori ga ummah ko ta dinga fadan abinda bashi ba ta yadawa a gari ga wanda baisan gaskiya. Duk da kota sani din a yanzun babu wani abinda zata iyayi saidai sherin kawai bayan shi bata isa tayi wani abinda zaisa aikin mu ya soke ba shi kuma boda Bisi abinda baiso ke nan uwar taji ya zamo muna matsala ana muna gori yasa ya gargademu da kada mu fadawa kowa zancen. A karshe shike fadawa mahaifiyarsu ashe zahra tana nan tare da mijinta don na gansu a wani shagali da akayi na karin girma cikinsu ko harda mijinta. Yadda mahaifiyar nasa ta rude tun a wayan yasan ba a kwana bata fadawa mama wanan labarin ba sai ya godewa Allah da bai taba fada mata shiya samowa master aiki ba. Aikuwa a ranan takira mama take labarta mata labarin dataji daga danta cewa ai yaga Zahra da mijinta ashe da gaske a nan yake aiki kuwa. Sun dan taba maganganu a tsakaninsu kafin suyi sallama tun lokacin mama ta kara tsananta tsanarta akaina yayinda bangare ummah take yawan yi muna sadaka da sauran abubuwan da addini ya yarda dashi. Ina can auren hannatu ya taso nayi bakin ciki da bani kasan a lokacin don haka nakira ummah mukai shawara da ita kan taje dakina duk abinda da take so ta dauka na bata shi saboda Allah don hannatu mutum ce a wurina gata kuma marainiyace gaba da bayanta. Ummah bataki shawarana ba don haka ta kira hannatun tace ta karbi makulin dake hannunta taje ta bude dakin ta dauki duk abinda take bukata injini. Kuka ta dinga yiwa ummah tana fada mata irin yadda yan uwa suka bata baya yanzu da auren nata ya taso sai hakkuri ummah kawai ta bata tareda yan shawarwari. Lokacin da hannatu taje don ta bude daki cewa inna tayi bazata bude dakin ba don ba,a shawarceta ba ai da za ace azo daukan kaya itama ai akwai kayan danta a ciki kada a hada mai dasu. Ta kyaleta ta fito ranan bata samu daukan komai ba sai daga baya taje ta fadawa ummah shine ummah ta kirani tana fada min nayi mamakin hakan har nake fadawa Dije. Itama Dijen mamaki tayi take fadin ikon Allah amma Rashida tana da karfin hali kodaya yadawo itace ke fada mashi ranshi ya baci sosai da jin hakan. Shine ya kira inna din a cikin fushi yace inna wai meyasa kike hakane ai kinsam banda komai a dakin nan komai na zahra ne idan ba tufafina ba don me zaki hanasu daukan abinsu tunda suke da abinsu. To yanzu ka kiranine kayi min fada ko me yace fada kuma inna ni kawai na kirakine ki bari su dauki kayansu tunkan rayuka su kai ga baci don Allah tunda bani na saya mata suba. Duk muna zaune a lokacin muna sauraren yadda suke kwasa da ita a karshe dai ta fafada mashi bakar magana ta kashe wayan nata rai bace ya kalli dije yace wanan yasa nace zahra ta bayar da key din gidansu don gudun matsala ashe ba a tsira ba. Shine daga baya nacewa ummah hannatu ta diba har gadon ta kwashe a kwashe komai wanda bata so ummah ta mayar wurinta hakan ko akayi. Sun samu bata gida don haka hannatu ta tatara komai ta fita dashi daga gidan su Asmau na kallo duk gulma ya isheta a lokacin. Hannatu kan Allah ya kashe ya bata don master da kansa yace ta hada da gadon da komai ta dauka don ko mun dawo ba a gidan zamu sauka ba saboda yana gina a can . Wanda sai lokacin muka san da zancen ginan da yakeyi din a nan gusau wanda wani aminsa da shehun ummah suke kula mai dasu don ya mayar da ummah kamar mahaifiyar cikin saboda hankalinshi yafi kwanci da ita yasa duk wani shawara da ita yakeyi yanzu. Lokacin da aka kawo kayan nawa gida an samu mama na waje nan suka saka ido suna kallo tare da sake sake a zuciyarta saidata fadawa diyan ta sukace mu muka sani dai ai koma meyasa aka dawo dasu gida din. Muna can kuma har wayau bayan anyi wanan an lafa labari ya samemu cewa an kama ya musa wai ashe wai suna smogal ne shine sunan shi ya fito. Sai da kyar aka samu aka sakoshi har da mahaifin master saida ya sa baki kuma ya kashe kudi sosai saboda Abba yanzu baida zarahi. Kuma duk Abba yayiwa mama da ummah bayani bayan daya dawo gida da yaya musa din tarasu yake fada masu duk yadda abubuwa ya faru ga Aisha da Rukkaya a wurin. Bayan sun koma dakin sune Aisha ta fara magana wai hum, ummm for god sake saida mijin zahra ya saka hannu fa ki duba don Allah mama. Daga inda Rukky take zaune tayi tagumi tace ba ina fada maku sunyi karfi sosai ba yanzu nifa a wurin wanan kawar nata kawana kejin labarin su wallahi ance yayi kudi sosai a can yanzu. Kai ni kina ban mamaki wani kudi aida mun gani ko a nan wurin uwarta tunda su ba abin boyo bane da za a boyewa mutane. Sunyi tayin halin nasu kafin su dawo zancen dan uwansu dayaja masu abin magana badon Allah ya gyara ba da ba, a san yadda za akaya ba a karshe. Ban rasa komai ba a rayuwata don haka ba abinda na nema na rasa a duniya don master gaskiya mutum ne mai fitar da hakin iyalinsa dana iyayye. Gashi da sanin ya kama ina zaune ranan bai fita ba yana zaune a gida falo yake kwance da yarshi suna kwasan rikici irin na yara yana biye mata. Na taso na zauna ba tare da nayi magana ba ido kawai na kura masu daga inda nake zaunen ya dan dago kai ya kalleni yana fadin madam ya akayine na dan kallesu na gyara zama ina dan kwanciya tare da bata fuska don gaba daya banjin dadin jikina duk kwanakin. Ganin banyi magana ba yake fadin ko jikin ne har yanzu muje asibiti naji sauki kawai dai jikin ne banajin karfin shi yanzu. Kuma ga dai azumi ya gaba to Dije kuma ta nuna min gida take son zuwa yanzu don ta nuna ta gaji da nan din don zama wuri dayan ne nasan ya isheta. A hankali nace haka dinne gaskiya ta gaji da zama kasan nan tana dai daurewane kawai bata nunawa jiya ai muna waya da inna take fadin wai Asmau ta samu miji ttace aure zatayi ita bata karatu. Asmau da batako kare secondary school dinta bane take zancen aure a yanzu yace waya sanar mata ita ta sani don na kula inna ta daure mata. Aisha dai munyi magana da ita tace wai FCE zataje kuma ban hanata ba tayi kokari ai idan ta tsaya tayi karatun don nam gaba zai mata amfani. Muma gashi mun gama amma yanzu muna zaman gida shine ummah ke tambayana ranan tana min sheri wai ni dana tsaya nayi karatu yanzu kuma ban batun aiki . Idanu ya lumshe kafin can naji yace gaskiya zahra bana bukatan kiyi aiki a rayuwana indai ba kinga gazawa na bane a gareki gaskiya tunda Allah ya hore min ya kamata ke ki zauna ki huta a gida kiji da dawainiyar gida kuma. Amma idan kina ra,ayi ba zan hanaki aikin ki ba tunda ra,ayinkine dana iyayyen ki don da karatun ki na sameki don haka ba zan tauyeki ba a yamzu. Gaba dayan mu shiru mukayi lokaci guda dagani harshi din da yake maganan a lokacina na dan wani lokaci kafin yace ina ma son kin mun list na wanda zamu turawa kayan sallah da abin azumi. Saidai kada ki sa Abba da su inna dasu ummah da gwaggo shafa har da baba Ado dawa kuma can dai Mambila zan aikawa baba jauro da komai a can. Duk kana da kudin da zakai wanan dawainiyar duk yadda ka lissafa murmishi naga yayi tare da fadin zahra ke nan kefa yanzu ba matar fakiri bane kamar yadda hjy tsohuwa take fada maki. Wani kallo nayi mashi yace yes na sani zahra duk da baki taba fada min ba kina shanye bacin rai a zuciyar ki ke kadai ki sani bake kadai ke hadewa ba har dani abin yana taba min zuciyana . Kada kice duk bansan halin da kike ciki ba na bakin ciki ga yan uwanki a kaina zahra nasan komai dake faruwa a lokacin kawai dai naga baki damu da hakan bane yasa nake sharewa nima. Raina bata kafin nace ai ba don ka suke wanan maganan ba don ni da ummah ce kawai don su musguna muna suga mama taji dadi a rayuwanta shine kawai. A ganin ki ke nan zahra lokaci yayi insha Allahu da zan nuna masu kuskuren su na fadin wanan zancen ni din dan halas ne zahra ba shege nake ba yadda suke daukana. Shiyasa kikaga bana raina lamarin ummah da Abba don sun min komai a rayuwata don Abba yai min wani magana a lokacin daya tsaya min arai bayan ya gama min jawabi. Wanda har yau dashi nake kallon Abba din don wanan kalamin na ba a wani a banza saika jajirce zuciyan ka kazama jarumi ka wanke kanka daga fadin mutane a kanka. A lokacin nayi ta juya wanan kalamin a raina ina neman fassaranshi sai a yanzu nake kara gane me wanan zancen yake nufi a kaina zahra. Abba yayi amfani da hikimarshi a lokacin ya aura min kene don yana da hope akaina