← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 243 OF 286

Sashe 243

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da kake dashi kuma zaka bata rawanka da tsale yanzu gaba daya suka kalloshi cikin mamakin jin abinda ya fada daga shi Ahmed din har Nabil da mahaifiyanshi dake tsaye daga kofan fitowa. Yace kwarai ina kunyi da mahaifin ka ya baka umurnin cewa ba zaka tafi ba yau din nan yanzu ina office aka kirani da bakon lamba na dauka ashe mahaifinkane ya kirani. Duk da bai fada min komai ba amma ya rokeni da kada in barka ka tafi hakan yasa na dawo yanzu a gagauce don in cika masa alkawarin dana dauka kan hakan kayi hakkuri don Allah badon ni ba ka tsaya ka saurari mahaifin naka. A hankali ya dago kai yace ba komai daddy zan tsaya zuwa goben insha Allahu ya fada nan daddy din ya shiga saka mashi albarka ashe abinda basu sani ba Abban nasu yasaka anbiyoshi anga gidan da sunan maigidan har nombanshi shine ya kirashi. Dakin Nabil din ya koma ya aje kayanshi ya ciro wayanshi ya bugo min ina tsaka da gyaran kitchen din in dora girki tunda zai dawo ranan komai dare yace saiga kiran wayanshi ya shigo. Na san shine saboda ringing din dana sakawa sunan na Assalamu alaikum ya bahbah dake tashe a lokacin na dauka da sallama ina fadin zaka taso ke nan ko ? Yace wallahi na fasa saidai in Allah ya dawo dani lafiya zakiji ko menene ki fadawa Dije don kada ta damu kanta da leken kofa bazan dawo ba yau nace Allah ya kaimu a sanyayye. Allah ya tsare hanya amma baka samu zuwa gidan Abba din ba da cewa Abban mu yace wani Abban wai nace Abban mu mana mahaifina yace Zahra kinsan na fada maki gaskiya ba zan iya zuwa ba ina jin nauyin hakan wallahi amma tunda ina shigowa yanzu watarana zanje ai insha Allahu. Amma kasan yasan da zancen zuwanka ai koya sani zahra nayi mai alkawarin zuwa wurin shine ya tambayeni ina jin hakan nasan ranshi a bace yake nace Allah ya kaimu gobe lafiya na kashe wayana. Girkin da banyi ba ke nan na koma daki na kwanta ina charting hakan ya dauke min hankalina ga komai saidai banji dadin rashin zuwa gidan Abban mu din da baiyi ba gaskiya ko banza zai duba muna jikin nasa ai a nawa tunanen. Karfe biyar daidai Nabil ya sameshi a dakin yace ana masa sallama a waje haka ya taso ya fito yadda yake inda ya samu mahaifin Nabil ya fito masu da fararen kujeru a haraban gidan. Ya iso yana masu sallama suka amsa nan Dady nabil din ya shiga yabon kirkinshi yana fadawa mahaifin nasa shiko sai murmushin yake yake masa. Ya mike ya barsu a wajen nan ya kara gaisawa da mahaifin nasa da yanzun yanayinsa ya canza sosai ba kamar dazun da rana daya sameshi a massalacin ba. Dan shirune ya biyo baya kafin yaji muryan mahaifin nasa yana fadin nagode daka yarda ka tsaya don ni na dauka ba zakai min wanan alfarman dana nema ba ai. Sai alokacin yaji kunyar kansa yadda mahaifin nasa yake masa godiya akan abinda shi yakamata ace yayi mai a lokacin watau biyayya a gareshi ke nan aa zuciya ya kasa hanashi ya tsaya yai masa hakan. Watau a game da zancen Dala kuma da kaimun gaskiya har yanzu zuciyana ta kasa gaskanta hakan don wanan bawan Allah akalla zaikai shekara arbain zuwa hamsin yanzu rabonshi damu. Dukiyar mahaifitace a wurin shi masu yawa daya gudu dasu tun lokacin kuma ba a kara jin duriyanshi ba sai yau din nan da kazo min da labarinsa da bakinka. Da ace wanine ya fada min da zan karyatashi don ba inda hardo mai sunanka baisa anyi mai cigiyarsa ba har kira anyi mai na asiri akan ya dawo amma hakan ya gagara. Ba zai dawo ba Abba don kun kirashi don shima hatsabibin kansane sosai a kewayen kaf yana da girma da kima a idon mutane bai dogara da kiwo ba a yanzu da aikin gona ya dagora nake gani. Don amfanin gonan da nake sayowa na sayar ya kaini wanan kasan arnakun har na hadu dashi saidai yaba kowa mamaki yadda yai min a wurin donshi ya nuna yasan ni yasan kuma koni waye. Nan dai ya fada mashi komai daya faru dasu a garin har zuwa maganin daya bashi bayan ya gaiyace shi gidanshi din duk ya sanarwa mahaifin nasa. Kafin dattijun mahaifin nasa ya danyi murmushi yace dama shi masanine don suna da gadon hakan amma sunan magajiya daya fada shine ya daure min kai a yanzu. Shin kasan ko wacece wanan magajiyan da yake nufi sai Ahmed din ya girgiza kansa alaman a, a koda yake zaka sani nan gaba idan ka kawo kanka gidan amma koda kazo din kayi hankali da kowansu don zasu nunama a fuska sunfi kowa kaunan ka a cikin zurian mu saidai abin ba haka yake ba a zuciyarsu. Sun danyi magana ta fahinta kafin suyi sallama mahaifin nasa yayi mamaki lokacin daya taya mai mota da zaisa a kaishi gida amma bai nasa mussun hakan ba kamar yadda yai tsamani zaiki hakan. Shima ya rasa dalilin hakan din don haka kawai yaji tun lokacin zuciyarshi ta karaya akan mahaifin nasa tsusayinsa ya koma ji maimakin tsanar dayake ji nasa a baya wanan zaman ya kawo sauyawan komai a rayuwan su kuma. Washegari da wuri ya karya don sammakon da zaiyi sai kuma yawan godiyan da mahaifin nabil da mahaifiyan shi suke masa yayi yawa don shi ya kamata ace ya gode masu kan dawainiyar da sukai masa na zama a gidansu sai gasu suke faman gode mai. Mota har gida malam Bala driver mahaifinshi ya kawo shi tunda suka dauki hanya labarin hjy yabi da yaranta yake ba Ahmed din da zaman hjy murja yanzu a cikinsu. Wanan yasa ya dansan wani abu a game dasu kafin su hadu din don ba dadi kashiga mutane baka san irin halaiyansu ba don hakan ake son bincike saboda hakan Ahmed ya ke shiryawa haduwansu din. Yau tunda gari ya waye ina gida ban fita ba sam banyi tsamanin ganinshi a wanan lokacin ba sai jin sallaman shi nayi Dije na masa sannu da zuwa. Thank god don a gaskiya ba ai mun girshi indai a wurin gyaran muhallinane don komai tsab a lokacin ba ga kuma abinci nayi na gama na aje don Warmer's dina masu kyau da tsadane suna aje zafi har wani lokaci. Nayi mamaki kwarai ganin irin tsaraban daya dawo muna dashi wanan karon ga muryan inna har makwabta dama irin hakan take son gani ga dan nata ta dafa yadda take so ta faki idon dije tayi kyauta ta kuma sayar idan kudi ya kakare mata na kashi. Yayiwa driver nan bazata don yayi mai goma shatara da zai tafi shima yanata godiya sukai sallama ya tafi har lokacin ba wanda yasan waya kawoshi gida sai bayan tafiyansune yake fadawa Dije ai driver mahaifinshi ne ya kawo shi har gida. Amadi kaga Bukar din ne a can yace eh dije muna tare dashi jiya shine ya bayar da mota wai a kawoni gida iko sai Allah sanyin hali irin na mutumin nan gaskiya sai shi. Ya kamata dai kaiwa kanka fada hakana ku shirya ko uwarkama kuji saukin zama don gani takeyi laifin duk nakane yanzu nasani Dije haka inna take tunane bata tunanen irin abinda zan sama a can. Allah dai ya kyauta tsohuwar ta fada har takai kofa ta juyo tana fadin ai na manta in fada maka uwar garke bata gidan nan tun jiya da rana mun nemeta mun rasa kaf shiyan nan . Kafin yai magana nina farayi don da karfi na furta bata gidan nan ta bata ko yau ina bude kofa na ganta a nan kofan kwance har ina mamakin yadda aka saketa tana yawo ba a daure ta ba.
Chapter 243 · 0% Book details