Sashe 266
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai dawo gidan ba sai karfe shidda na yamma kuma tare da Nabil din suka dawo a lokacin kuma suka zauna a wurin daddy ashe tare da kaninsa yasir suka fita. Case sukayi sosai a ranan kan daddyn nasu yaki saka Nabil a harkansa na kasuwanci shine suka sameshi a office dinsa sukai magana dashi ta fahinta. Ida daddy din ya dorawa Yasir din wasu dokoki daga nan kuma shi yasir din yai fushi yace an tauyeshi da yawa a cikin harkan. Saida kyat master ya samu ya lalashi mahaifin nasu inda daga shi har ita salima din aka samu inda aka sasu kamar yadda suka bukaci mahaifin nasu yayi masu tun baya yaki don sanin halinsu da yayi. Suna fitowa wurin yasir din daya kwasheshi sai gidan da hjy yabi take zaune ya kaisa inda ya samu harda yarta suna nan gidan da farko data ganoshi ta firgita da ganinsa tare da jin wani iri. Amma gaisuwa irin yadda ya gaida ita din sai jikinta ya fara sanyi dashi yace mummy jiya mun shigo na sauka a gida sai na samu baki gidan. Dana tambaya sai Abba ya nuna min bai son maganan na barsa ne banyi maganan ba a lokacin har sai nazo na ganki don inji ra,ayinki akan hakan . Don baidace ba ace yanzu kin bar gidan Abba duk dadewan da kukayi tare sai lokacin da hutu da samun natsuwa yazo maku lokacin da yara zasu dauki nauyi ace irin wanan matsalan ya fito a tsakanin ku har abu yakai ga barin gida haka ? Duk kokarinta naso ta yaba mai bakar magana bata samun fuskan hakan ba gareshi saboda wani irin kwarjini da yaron yayi mata gashi da gani komai ya zaunu gareshi ya waye fiye da tsamaninta zakace shi din ya dade a turai ba danta yasir ba a lokacin. Ba halin magana a yanzu gareta don hanyar komawa dakinta takeso ako wani hali saboda duniya gaba daya ta bata baya lokaci guda. Yaci gaba da fadin babu dadi azo gida a samu duk manyan yayan gida babu iyayyensu a gida sai gidan ya koma kamar wani tsohon filin yakin da akai shekaru da barinsa. Zaki koma dakinki kwanan nan mummy ba tare da an tsaya wani tone tonen abinda ya faru ba har ya kawo wanan matsalan mai karfi a tsakanin ku ba mu dai bukatan mu shine ki koma dakinki ki zauna ku rufawa junan ku asiri dake da daddy zai fi. Ya mike tare da gyara kwalan riganshi yace zan tafi mummy da fatan ba za a samu matsala daga bangarenki ba sai kin jini yayi masu sai anjima tare da saurin fita daga falon don baison kallon jan fuskokin su kada ya fasa aikin alherin da yake son yi a lokacin kansu. Don Allah ya gani a lokacin ba karamin dake zuciyar shi yayi ba har yakai ga yin hakan saboda abubuwan sherin da matar tayi mai aduniya. Amma yau kawai dayaga yayanta a cikin halin maraicin uwarsu sai jikinsa yayi sanyi don yasan irin kuncin hakan duk dasu suna tarema da mahaifinsu a lokacin shiko baya tare da kowama alokaci da hakan ya sameshi. Ita ko hjy yar hjy yabi kallon yar uwanta tayi tace Yabi kin gani ko kinga rokon Allah mu a inda ya fito muna ta hanyar da bamu zata ba wanan yaron nasan yasan komai boyewa yayi ya nuna baisan meke faruwa ba. Makirine kamar ubansa ya sani ya nuna bai sani ba koma meye ai ni dai bukatana naga na koma dakina yanzu shine kawai burina a yanzu don ina kwana a zaune ina tunanen yadda murja zata juya min yarana bana gidan. Ki duba gasu yasir na zaci hakan amma ban samu ba sai gashi wai wanda akai abin donsa shine ya dawo yake son mayar dani dakina a yanzu. Ni ai yaran nan sun ban mamaki sai kace ba a kansu nake wanan yakin ba shine da su master suka dawo gidan shine ya zauna da mahaifin nasa suka kara zance kan aikin yan uwan nasa dakyat ya samu mahaifin nasa ya yarda har shi Nabil din ma daya rakosa ya samu nasa a lokacin wurin. Washegari sammako mukayi na tafiya don akwai nisa tsakanin zamfara da abuja sosai muka dauki hanyan zuwa zamfara din cikin motan da nake zaton na daddy . Muna cikin jeep din yayin da hilux yake bayan mu dauke da kayan mu yaran da basu saba da irin wanan tafiyan ba mai nisa sunyi kuka har sun gaji sai shidda na yamma muka shiga zamfara. Shehu ya kira a waya ya fito hanya ya taremu shi yayi muna jagora zuwa sabon gidan daya gina a nan garin gidane na gani nashiga tsara a lokacin don ko parking space din gidan zai dauki mota goma sha. Ni dai duk ba wanan bane a gabana ba lokacin burina na kyala ido akan Abban mu dake asibiti kwance kuma inga mahaifiyata tare da yan uwana danayi shekaru bana tare dasu. Mun shiga gidan komai zamzam a cikin gidan a falo muka zube don kafin mu iso har an tayar da injin din gidan ya dauki haske tako ina zama mukayi a nan don mu huta kafin su shigo da shehu ciki. Muka gaisa yana wani kara ban girma kamar yagga wata babban mace irin yadda akewa mama a da can baya hakan ya fado min a zuciyana lokaci guda. Nace a shehu ya muka sameku ya kuma kokari wallahi lafiya hjy na dan kalloshi Master yayi muna murmushi yana dukar da kai ban gane manufarsa ba a lokacin nayin hakan. Mun samu abinci a wurin munci donshi da yara da dije sukaci sosai ga kuma mai aiki da wata yar matashiyar yarinya su biyu wai ummah ce ta dauko mun su daga can garin su da zamuzo din nan don su rika taimaka min da aiki. Ai kuwa dai nasan akwai aiki don baya yarda da hakan nima kuma dai nafi da son nayi aikin abinda zanci da kaina don inada yawan tsanda ba girkin kowa nake iya ciba ni kaina shi kuma har yafini wanan halin tsanda din. Sallolin dake kanmu muka rama kafin na dago ina kallonshi a inda nake nace amma yau zamu shiga wurinsu ko muga mai jikin yace naso hakan amma yanzu dare yayi ku zauna a gida sai gobe da safe na kaiku. Zan tafi sani da shehu mu fara duba jikinasa mu gani don yanzun nan muka gama waya da Abba yake tambayana jikin nace ban karasa can ba tukun. Ba a dade ba shehun ya dawo gidan dauke da katon katon na abubuwan sha dana sauran bukatun mu suka fita tare dashi zuwa asibitin kakace bacan din ma zasu ba a lokacin don ni haushi ya hanani yin magana. Mama mama na kwala mata kira ta amsa tazo wanan matar da aka kawo min don bansan ya suke da mahaifiyata tunda ta haifi wanda ma ya girmeni don haka ban rage ba ai. Mama a dauke kayan abincin nan aje aci idan kun koshi kuma a duba wani gida nan kusa don Allah a basu don abincin yayi yawa kada ya lalace a banza. Tana godiya suka dauka nace ta turo wanan yarinyar ta tayamu saka kaya a daki na tashi sai lokacin na leka dakunan komai na gidan da gani kasa odan su akayo daga can masu kyau da tsada. Kowani daki ba laifi an gyarashi tsab an saka komai a cikin dakunan kwanan saidai nawa da nasa sunfi tsaruwa dakin da yace shine nawa an yimai ado da kayan cikinsa yafi kowane tsada a gidan. Komai na dakin nawa white and purple gwanin ban sha,awa hakan ya karawa dakin kyau da daukan ido a magariba aka kira yasa na shige daki tare da yarana dije kuma tana dakin daya kai kayanta ya nuna nan ne masaukinta. Wai ashe duk abin nan inna bata san mun shigoma Nigeria ba sai ganinshi sukayi kwatsam kamar daga sama ya shigo gidan yana sallama. Aishace kadaice a gida lokacin inna ta fita Asmau kuma bazawarinta yazo wai ta fita don aurenta da shekara daya ya mutu kuma da ciki lokacin Allah ya rufa mata asiri wurin haihuwa diyar batazo da rai ba shine yanzu take sabon zawarci don taki karatu ko secondary taki ta karasa wai ita aure take son yi tace. Don haka kowa ya zuba mata ido ana kallonta don dama bata da kunya shi kadai take tsoro yanzu kuma bai kasan tare dasu sai abinda taso takeyi. Da farko Aisha wai bata ganeshi ba saida yace Aisha ke kadaice a gidan wai ina sauran mutanen gidan ko inna har yanzun bata dawo bane wai ? Yayan mu wai kaine dama ban gane kaba wallahi muryanka yasa na ganeka yanzu tana kallon bayanshi ko zata ganmu tare dashi mun shigo gidan muma. Ina su Dije da anty yaya yace ba zaki gaidani ba nida kika fara gani suna can na barsu to ya fada yana bin gidan da kallo ko ina don gaba daya gidan ya sauya mashi kamar ba mutane a cikinsa. Dakin Dije da yanzu Aisha din ke zama a cikinsa ta shiga da sauri ta fito da kujerun roba farare guda biyu hade tana fadin inna sai dare kila ko kuma anjima kadan ni kadai ta a gidan yanzu. Ta aje kujerun yace tunda bata nan ba zan zauna ba amma kice mata nazo gobe zamu dawo yaya har zaka tafi ko ruwa baka sha ba fa yace sauri nakeyi zanje asibitine na subo mahaifin zahra . Subbahanallahi yana asibitine kuma yaya yace eh ance yana asibitin kwance ba lafiya walle ban sani ba aida naje na subashi kwanaki dai naje nagaida ummah da sallah. Kin kyauta ai ina ita Asmau din ya fada yana kallonta hummm ta fita bansan inda taje ba na daiga tayi wanka ta fita dazun saidai ka dawo yaya mun zauna ai. Har kofan gida ta rakoshi ya shiga mota tare da shehu yaja ita kuma ta koma cikin gidan cike da mamakin ganin bazatan da tayiwa yayan nasu haka kwatsan gashi kuma ba a gidan ya sauka ba ko ina ya sauka oho don dai tasan shi ba mai yawan abokai bane balle