← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 286

Sashe 86

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

a baya yanzu laifin ku nake gani. Shiru tayi tana bin jikina nata da kallon mamaki kafin tace shiyasa kataho min da zancen shi kwanaki ko ai tun lokacin na fara zargin da akwai wani magana a kasa da kake son fito min dashi. To bari kaji garin nan kaf ba wanda naji ya taba zuwa garin da yace ya fito saidai naji sunan garin a gidan redio jefi jefi. Amma dai ai cikin kasan nan yake ko koma ba kasan nan bane ya zama dole yanzu inje neman mahaifina duk da yayi banza dani nan cikin duniya amma nasan dole ina ranshi idan yana raye. Wa hwada maka ga garin da yake da zama taka maimai ko nan daya taho ai a karkashin Alh Abu dan canji ya zauna shina ma yayi auwalin aurene har muka yarda muka bashi ita. Daga baya da tahiya tayi nisa yake fada muna shima bai san garin su ba ya dai yaba da hankali nena ya tsaya mashi akai auren. Gara ma tun wuri ka fitar da zancen shi a ranka don kila ma baya raye yanzu ni haka nafi sawa raina don gaskiya inda Auwalu na raye nasan daya taho nan ko don kai. Dije ko bai raye zanje yan uwanshi su san dani a a nika zama nan ana tsangwamata kan laifin da ban aikata ba gara naje nasan asalina da anka fara fadin bani dashiya. Aiki ko ja a gabanka zuwa wanan garin har uwar duniya don baka san iya kwanakin da zakayi a hanya kafin ka kai garin. Zuwa lokacin yagama hasala da kakar tasa don da ace Dijen tasan yadda zuciyar shi ke tafarfasa a lokacin da bata yi wanan zancen dashi ba a lokacin. Damace gareshi a yanzu don haka bai cewa Dije din komai sai shirin tafiya daya fara bayan ya tambayu kan yadda zai kai kanshi garin mahaifin shi na asali. Tare da samun karin bayanin yadda zai iya gano mahaifin nasa idan ya isa wurin wasu abokan hurdan mahaifin nasa a nan gusau da yai zaman mutunci dasu a garin. Sallah asuba nayi na zauna ina tulawa a wurin kafin gari ya kara haskawa na fara jin motsi a gidan na mutanen gidan dake kara kaina a tsakar gidan ina jin motsin duk abinda sukeyi saidai ban fito bane waje lokacin. Bayan na shafa na mike na shiga bandaki wanka nayi don nayi saboda hakan don zuwa school dana saba fita da safe dana gama azzakar saina mike na shiga wanka. Na fito na shirya cikin dinkin atampa da akai min buje da riga na fito yar shar dani na mike na fito zuwa falon gidan namu. Babu kowa a falon saidai abinci da yan aiki suka jera a saman dining wata kafira da dan bujene a jikinta ta fito daga kitchen dauke da wani katon dood warmer a hannun ta tanufi dining din ta aje ta juyo sai lokacin ta ganni a zaune. Ina kwana mah ta fada tana dan rage tsawonta kadan don ban girma a gareni na amsa ina kare mata kallo tare da kyaman yadda na ganta nasan ba musulma bace. Don mu a lokacin zaman mu gidan ummah bata taba yarda ta dauki yar aiki kafira ta jefa cikin mu saidai musulma yar uwan mu da zata bamu tarbiya a tarevta dauketa tankar yarta na cikinta. Idan zasu tafi kuma a rabu a cikin mutunci da dadin rai ana kewan juna kamar kada su tafi amma gashi yau arniyace a gidan take dan yawo da buje kuma cikin kazanta haka irin nasu ko don ina kyaman hakane a raina bansani ba ? Hjy nakawo maki abincin ki a nan ne ta tambayene cikin girmamawa nace no ki barshi idan na tashi ci zan nemeki tace yes mah ta nufi kitchen inda suke aiki. Daga kai nayi na kalli dakin ummah wanda a yanzu mallakin mommy ce wai sai naji zuwa Abujan nan ya zame min dana sani don abin bakin cikin da nake gani a gidan ga zuwana. Karan budan kofa naji yasa na dago kai mommyce tafito daga dakinta tana kokarin nufar dakin Abba dake rufe sai kuma ta juyo ta dawo zuwa dining da nufin duba abinda aka girka na breakfast. Kullan farko ta bude ta rufe ta fara kwalawa kiran sunan wata da Tabitha daga can kitchen mai sunan ta amsa sai gata da sauri hjy ta fara fadin banace idan kun gama ku fada min kafin ku kawo kitchen wai meyasa ku bakwa jin magana ne ko koyaushe sai na dinga nanata maku hakan ne ? Dauki kikai min daki idan na gama zan kiraki fito dashi sorry ma Janet naba ta kawo ashe nan ta aje ai ban manta da dokanki ba. Common dauki ki tafi kin tsaya kina surutu tana fadi ta juya ta shige daki matashiyar matan tabi bayan ta duk wanan abin bata kula da cewa ina falon zaune ba ta shige dakin. Gabana ne ya fadi me za a jeyi da Abincin kuma a dakin mommy tsam na mike daga inda nake zaune din na nufi dakina dana fito gado na haye na kwanta ina faman tunane. Barcine ya soma daukana a hakan naji an turo kofa na bude idona mommyce tashigo a cikin shirin ta na fita aiki ganina na shirya tsam kamar mai shirin fita ta saki murmushi a fuskanta tana fadin. A, a my daughter wanan kwalliyan haka rangas ko wani wurin zaki tafi dagowa nayi da dan murmushi a fuskana na zauna ina kokarin sauka daga gadon tare da fadin ina kwana mommy ? Lafiya kalau ya gajiyan hanya koda yake da alama kin sauke gajiyan ma ai tunda naga harkin shirya haka fita zakiyine ta sake tambayana. A, a mommy ba inda zani kawai dai haka na saba dashi damani na fada na koma saman gado na zauna tace to ai hakan yai min dadi sosai don dama ga abinci can an gama sai ki fito muci kafin Alh ya fita dama baku wani gaisa sosai ba jiya ya shige part dinshi. Mommy bana karyawa da safe haka sai dai in an jima zan fito nace wajajen karfe goma kice min yar tawa baturiyace kema kina irin tsarinsu ke nan dai ? A a mommy haka dai na saba daman ni to ki fito ku gaisa da Abbanki yana falo zaune zan fada masu kadasu kwashe kayan abincin sai idan kin karya din yanzu taso muje kafin ya fita. Zaune Abba yake yana waya tana fitowa yake fadin kinsan fa sauri nakeyi kin kuma je kin zauna abinki can sai gani na fito bayanta hakan yasa yai shiru a lokacin. Har kasa nakai ina fadin Abba ina kwana lafiya ya amsa min dashi yace ya gida ya kika barsu a can , ? Kowa lafiya suna gaida ku amma ban samu zuwa gidan hjy na sallameta ba don nasan zai tambayeni hakan. Ba laifi ya fada yaci gaba da cin abincin shi da mommy din ta zuba mai wanan din kuma datasa akai mata daki dazun. Ta juyo tana fadin daughter idan kinzo karyawa wanan ferfesune a cikin cooler zakiji dadim shi sosai ga Abban kinan ma zai sha kefa Abba ya fada naji tace ai kasan ban faye cin kifi haka da safe ba. Kofa aka bude wasu mata biyune suka fito a cikin shirinsu duk muka dago muna kallo su .
Chapter 86 · 0% Book details