← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 286

Sashe 62

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoki naja nayi wurgi da wayan ina dana sanin zuwa wanan gidan a ranan da banje ba da hakan bai sameni ba ai sai naji duk wani farin ciki da dan walwalan dana samu ya gushe a zuciyana sai zallah takaici da haushi tare da wani kunci daya tokare min zuciyana. Ban iso gida ba sai wajajen magariba ganin kofan gidan namu ba yawan jama,a yasa na gane cewa Abba ya tafi ke nan shi da Amaryan shi. Gwiwa mace haka na fito daga motan na rufe na rataya jakata zuwa cikin gidan namu da sallama na bude kofan part din mu da ake rufe tun shida kamar yadda musulunci ya koyar ayi. Ummah ne falon zaune da kanne na jin karan bude kofan yasata dago kai gareni tana fadin yau ina kika tsaya haka baki dawo da wuri ba ? Dan daburcewa nayi kafin na samu natsuwa ajikina nace mun tsaya summit din assignment ne ummah bana son wanan dadewan haka a waje kisani dai ke mace ce. Toh ummah na fada don a matse nake na isa dakina ina shiga jakka da yan takardun dana riko na wurga saman gado na fada ban daki fitsari nayi sosai kamar ba zai tsaya ba a lokacin yadda na zubashi. Sai lokacin na fara samun sa,ida a jiki na mike kayan jikina na kalla kafin nayi shawaran kwabesu cikin bandakin tare da wankan dana darji jikina da kyau da soso da sabulu masu kamshi na fito na saka doguwar rigana a daidai lokacin an fara kiran sallah. Don haka na tayar da sallah dama da alwala na fito daga bandiki din ban fito ba saidana sauke isha,i nayi addua na mike na fito don na samu abinda naciwa cikina. Dining na nufa na bude abinci ina diba kani dake bi mun yazo yana fadin anty zarah nima ki zuba min banyi magana ba amma ji nayi kamar ya dora min wani aiki mai nauyi akaina. Na jawo plate na zuba mai nasa sanin halinsu yasa na zubawa kowa nasa a lokacin bankai ga zama ba sauran suka fito wurin dan suci abinci basa wuce takwas zuwa tara basu barci ba sai ummah kadai muke bari tana tsabgoginta. Nan muka fara cin abinci sai karan cibi kakeji a wurin da dan surutun yaran dake tashi ummah ta budo kofa tafito daga daki zuwa falon . Ai ki basu abincin ne ashe yasa najisu shiru basu shigo damuna ba munan tare dasu tun dazun na bata amsa auta da kanki kikecin abincin ta kalli yar kanwar mu dake ci a wahalce. Kafin nayi magana kanin mu ke fadin ummah tace bata son anty ta batane karban spoon din tayi hannun yarinyar ta fara bata daga can kanina yace ummah yaushe Abba zai dawo ? Ummah wai sun tafine na tambaya ina kallon fuskan ummah din a inda take zaune, tace dazun da karfe hudu suka tafi take naji wani iri a raina lokaci guda. Don gaba daya na kula wanan zuwan na Abba iyayyen mu gaba dayansu basuji dadin zuwa nasa ba don sai shi da Amaryan shine da yanuwan dake sintiri a gidan namu da sunan zuwa ganin amarya don ace tana raba masu kyauta idan sunzo yasa sukai ta tururuwan zuwa ganin ta din. Lokacin na fahinci cewa da wata manufa sukayi hakan duba ga yadda a dasuke bin mama suna banza da ummah watau sai inda akalan Abban ya juya a nan suke suma ke nan don neman abin duniya. Magana ummah take min amma sai taga ba saurarenta nakeyi ba na shiga dogon tunaneni a lokacin wai me kike tunane haka wai ? A,a ummah na fada ina nisawa kafin naci gaba da cin abincin dake gabana ummah tacigaba da fadin ai gara da suka tafi yau din don zaman su zai iya jawo fitina a gidan nan tunda dan zuwan nan nasu Allah kadai yasan iya fitinan da hakan ya haifar a gidan nan. Yanzu zama yake sosai a cikin gidan nan tunda an hada hardani waini makirace tunda na girka abinci dasu kamar yadda yabada umurnin a girka masu har kwana nawa zatayi ta tafi inda tafito da zan tsaya yin kishi da ita. Ita bata gane cewa hakan yafi muna rufin asiriba da ace sai an dauko abinci daga gidan hjy an kawo nan mu muna kallo zaifi zafi da cin zuciya a garemu. Yanzu ba gashi sun tafi ba an dai rabu lafiya aurene baka da hujjan hana namiji yin abinsa idan ya tashi don me zan tsaya fadan kan abinda nasan bada maganin sa . Iyaka dai inyi fatan Allah ya hau dani saman kansu duk wani sheri ko mugun fata mutum ya nufeni dashi ya koma kansa ni kuma ubangiji Allah kada yabani ikon tunanen da zan cutar da wani a cikin su. Amin na fada ina lumshe idanuna lokaci guda kafin nace sai azumi ke nan Abba zai dawo yanzu bana ba zai fara azumi tare damu ba a nan ke nan ? Tunda yana da mata a can yanzu ba zaizo nan ba sai azumi ya raba tsakiya ke nan zaizo rabon sallah ga mutane yadai bada sakon ku nan ya bayar a baku yana hannuna. Mungode muka fara fada duk da Abban bai kusa damu a lokacin amma hakan bai hana munyi godiya gareshi ba yadda muka sabayi a gaban shi. Ummah mutanen nan dana kaiwa kaya dazun suna ta godiya sosai wallahi tundai tsohuwar nan dana kaiwa gidanta tayi tasa albarka sosai wallahi tana maku addua. Kallon mamaki ummah ke min a lokacin kafin tace dani wace tsohuwa ke nan kika kaiwa sadaka na dan natsu nace kakan wanan din Ahmed din na na school din mu wanda ya taba taimakona din nan har ya kawoni gida. Kinsan gidansu ne ta tambayeni nace eh mun taba zuwa da yawan mu gidan mu gaidashi don shike taimaka muna a school sosai sai muka hada kudi dubu bibiyu mukaje gidan gaidashi. Maamah kin fara yawo daga school ba tare da sanina ba ke nan da sauri nace a, a ummah wallahi banda nan ban taba zuwa gidan kowaba wallahi ko in group mukaje yau kuma tare dasu hanne kawayena mukaje gidan. Ban dai son hakan idan zaki wani wuri daga school ki dinga fada min na sani kada ki kara zuwa wuri ba tare da sanina ba a gidan nan nace kiyi hakkuri ummah. Daga hakan ba wanda ya kara wani magana kuma a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi kan hakan daga baya ne na mike nabar falon zuwa dakina. Wajajen karfe hudu na asubahi Dije ce kwance tana barci a dakinta sai tayi mafalki ga mutum tsaye a kofanta yayi mata sallama ta dago ta amsa mai yace. To uwargidan mu ni zanyi tafiya ga amana nan na bari a hannun ki duk da nasan kina da rauni a wani fannin amma ki kula ki kara kulawa don mai yuyuwa zan dauki lokaci ban leko nan din ba. Baki na rawa Dije ta tambayeshi yace amman dai aiba wani sabo bane a wurin ki illa amanan wa yanda kika saba riko gidan nan ga tsiro nan garine wurin wanda yafi garin ga baki daya a wurin nan. Idan kunyi gigi ko gangancin cireshi kunyiwa kanku hasara mai dinbi yawa a nan Allah ya kaddara saduwan mu wani karon idan da rabon mu sake ganawa a duniya . Kamar zai tafi ya tsaya yace kibada goyon baya ki karfafawa mai rauni zuciya ki daure ki bashi goyon baya alheri hakan zai zamo maku wara rana. Yana fadin hakan tanemeshi ko kasa ko sama bata ganshi ba bataga inda yabi ba adaidai lokacin ta falka daga barcin kunnuwan tane ya fara jiyo mata kiran sallah ladanin can kasan unguwar su yana kiran sallah. Ga wani zufa dayake karyo mata ko ina a jikin ta sai zancen mafalkin ya fado mata a rai take takai kallonta ga kofa kofan yana rufe yadda ta turashi ta tangale da katon kuttuture ice yadda take turawa idan zata kwanta. Ladanin masalacin sune yayi kwance kwance ya kira sunan ubangiji da karfi har ta dan kadu don firgicin dake tare da ita a lokacin. Motsin fitowan Amadi daga dakinshi taji hakan yasa hankalinta dan kwanciya budan kofa tayi saidai bata fito ba tana ciki tana dan kimtsawa saida taji fitowan jikan nata daga bandakin tafito daga dakin nata. Kin tashi Dije ya fada yana kaiwa duke eh barkan mu da fitowa an tashi lafiya yaya daren me yuyuwa iya gaisuwan da zasuyi ke nan a ranan sai kuma dare su kara tashi. Tambayan shi takeyi da ba a daiga wata ba ko yace wallahi Dije har na kwanta na dade banyi barci ba ina dako ki za,ayi shelan cewa anga wata mu dauki azumi sai naji shiru. Toh gamu dai sai mu kama baki zuwa safe mu gani ko zamu samu labarin ganin watan a gari tunda mu nan bamu da redio ko abin sani tashige bandaki yayi akwala ya shige dakin shi. Wayan shi ya dauko ya haska sako ya gani a wayan da baisan da shigowan shi ba tun daya na dare sakon ya nuna ya shigo mai number zarah ce take sanar mashi da cewa anga wata . Da sauri ya fito yana nufar inda Dije din take zaune yana fadin Dije wai ashe anga wata tun jiya amma ba a sanar ba ko meyasa basuyi yekuwan cewa anga watan ba yadda aka sabayi a baya can. Ikon Allah anga watan ke nan ta fada saimu wuce da saje ke nan don yanzu ba halin cin abinci don kadan ya rage a kira sallah. Duban lokacin yayi yace zaki iya gagautawa ko ruwa kisha don akwai kusan minti ashirin yanzu kafin a tayar da sallah. Hakan sukayi shi dai Amadin ruwan fura yasha sai ruwa daya kora bayan niya daga haka ya fice zuwa masalaci yayi sallah itama Dije ta shige dakinta ta fara gabatar da Nafila lokacin. Garin yayi tsit baka jin motsin mutane ko ina haka ba yawan mutane a titin sai jefi jefi haka yan makaranta da ma,aikatan dake fita aiki suke dan fitowa a gidajen su zuwa wajajen tsabgogin su. Haka na shigo makarantan shima
Chapter 62 · 0% Book details