← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 286

Sashe 95

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tambayan to ko shegene meye laifin shi tunda shi yana da natsuwa bashi ya aikata hakan ba ai. A take wani sashi na zuciyana ya bani amsa da fadin inko hakan ya tabbata ko ummah ba zata yarda ba balle Abba da yake na miji nima kaina duk da nasan za,aita aibantani kan hakan ba yarda zanyi da hakan ba. Ke nan taraiyana da Ahmed din dai akwai matsala ke nan don haka dole in tambayeshi inji gaskiyan abin daga bakin shi don ban taba kawo wanan tunane a kwakwalwana ba. Haka na ajewa raina zan tambayeshi labarin mahaifinshi dana yan uwanshi inji daga bakin shi don komai nason tambaya asan gaskiya tunda Abba ya nace da maimaita kalma daya haka a gareshi . Nasan talauci ba zai hana auren mutum ba tunda Allah shikeyin mai arziki jikin matalauci haka yayo matsiyaci jikin mai arziki don ba a san mai gobe zata zamawa mutum ba ai a rayuwa. Ni kadai a daki nake faman kullawa in warware don banda abokin magana a gidan daga mommy sai yan aikin ta da mukan dayi hira kuma akan abinda ya shafi girkine haka. Don kanen mommy dake gidan zan iya kirga ganina dasu a gidan don basu zama gida ko suna gidan ma ba ruwan su dani nima haka ba ruwana dasu don naga suna da gadara da jin kai sosai a yanayin su. Sallah nayi na koma gado don sam ban jin yunwa a ranan na kwanta a lokacin zancena da mommy ya fado min a raina nace watau ita mommy haihuwa take so a hakan da girman ta gashi ummah ma data haifi Affara mama tana fadin ta tsufa tana haihuwa balle mommy da zata girmewa ummah din nake gani. Ina nan ina mirgina saman gadon naji mommy ta shigo dakina wuta dake kashe ta kunna ta ganni kwance take fadin badai yarinyar nan barci tayi bataci abincin dare ba ? Kara lafewa naji kamar ina barcin gaske naji ta gyara min rufin bargo ta kawar min da rigana dana aje a gefen gadon ta kashe wutan dakin taja kofa ta fita. Ajiyan zuciya na sauke ina bude idona kallon lokaci nayi a wayana karfe goma sha daya na dare saura naga lokacin yayi saurin yi a ranan duk ban sani ba. Wayata din na kalla naji kawai in kira Ahmed mu danyi hira na danna kiran layin shi ya shiga yana ta ringing bai daga da wuri yadda ya saba dagawa ba idan na kirashi din. Sai can wayan na batun tsikewa naji ya daga yana sallama yanayin da nake jin muryan shi din yasa nake jin kamar a mota yake tafiya don karan iska da nake ji a lokacin. Ina kake haka nake jin wata kara kamar kana cikin mota yace muryan shi da nake ji can kamar yana yawo a iska yana fadin gani taraba zahra zanje wurin mahaifina ne. Na ambata Taraba fa kace Brother yace eh ina cikin mota yanzu idan mun sauka zan kiraki idan baki barci ba Allah ya tsare hanya nayi mai ina lumshe idanuwana a hankali daga inda nake kwance din. Baya mun gama wayan ne na ambata Allah mai tsarki da daukaka na godewa Allah da banyiwa Ahmed wanan tambayan ba har na samu amsa a wurin shi haka a cikin sauki. Da nayi masa tambayan dani zan rage da kunyar hakan shiyasa ake cewa komai yana son tunane da nazari kafin mutum ya aikata shi a rayuwan shi ashe . Hakan yasa naji wani natsuwa da dadi a zuciyana kamar an cire min lakkan jikina a lokacin yadda nake jin kaina a lokacin har wani nauyayyen barci ya saceni lokaci daya ban sani ba. Ahmed kuwa yana kashe wayan ya nisa ya lumshe idanun shi yana sauke ajiyan zuciya zakace yasan abinda ke a ran zahra ne a lokacin muryan tsohon nan dake kusa dashi zaune yaji yana fadin ai yanzu mun dan fita taraba bakaji yanayin ya canza maka ba. Yanzun zamu shiga hawan Mambilane daga nan mun fara tasan ma nahiyar mu na mambila ke nan daga nan ya zakaji yanayin garin ya sauya ma daga nan . Saidai tsohon bai gama rufe baki ba yaji driver na fadin banga mota nabi hanyar nan ba idan mun kai nan ga kadan mu tambaya muji lafiyan hanyan yaya yake. Nan yaga yan cikin motan a tsorace suna fadawa driver cewa ya dakata kawai su kwana a dan kauyen gaba zaifi da asuba sai mu kama hanya na gaban motan ya fada. Bari dai mugani malam idan hanyar zata biyu sai mu mike zaifi inji drivern shidai yana jin su yana zaune a bayan mota yayi shiru yana addua. Ummah ce zaune a falonta da safiya Tani maiyiwa ummah din aiki ta shigo ta sameta suka gaisa take tambayan ummah din ko anji mata motsin uwardakinta anyi waya ko da ita ? Ta kira jiya mun gaisa kin santa da shiririta ko sakarcine wai tayi mafalki ta falka da safe duk jikinta ya mutu ita tana jin tsoro ko waya fada mata mafalki gaskiyane oho ? Da sauri Tani din ta kalli ummah tace hjy kune dai baku daukan abu da muhinmanci a yanzu ai bai kamata ko kice haka ba da sau ki tambayeta kiji akan me tayi mafalkin aji ? Duk da dai ba duka mafalki yake zama gaskiya ba amma da haka dan karamin abu yake zama babba watarana saidai sakaci irin namu na mutanen yanzu ke hana mu dauki mataki kan abu sai yazo ya girma yadda bamu iya dauka muce muna neman sauki a kan abin. Yarki ta girma yanzu ba za,asata a sahun marasa wayau ba don tasan ciwon kanta yanzu kama yayi kiji irin mafalkin kinga in na sadakane sai ai mata sadaka a nan Allah ya tsare zaifi. Wanan ne kuma Allah bai ban ikon yi ba ko ince zan mata sadakan banyi ba gaskiya ummah ta fada a dan damuwan hakan don maganan Tani din yayi tasiri a zuciyar ta. Tasani cewa tun tana karama wani lokaci manya kance sunyi mafalki bari suyi sadaka don Allah ya mayar da abinda sukai mafalkin alheri garesu. Amma gashi ita bata bada daman hakan ba ga yarta sai binta da tayi da fada tana kira mata sakarci komai sai ta saka arai ya dameta don mafalki zatace tana jin ciwon jiki. Iyayye mu farga da wanan maganan a yanzu a kan yayan mu don a yanzu zamani na tafiya ne da nau,i biyu wayewa da jahilci don har yanzu akwai masu jahilci dake sihiri akan mutum kuma Allah zai iya nunama a mafalki wanan baiwane da yawancin mutane da yawa kedashi a cikin rashin sanin hakan garesu. Mata mu farga da yawaita yin sadaka ga yayan mu don min sadaka riga kafin masifa ne ga bawa sadaka baya tafiya a banza inji masana addini komai kankanta abin sadakan zaiyi amfani ga maishi. Musan man sadakan abinci, kudi, tuffafi kosai sugar kuli,kuli alewa naira darin ki sai yai maki riga kafin rayuwan ki dana yayan ki duniya da lahira. Amma yanzu wata ana sati daya ko fiyema da hakan bata mika wani abin ba da sunan sadaka saboda Allah da Annabi Allah ya kare ya tsare ya bada ikon yin hakan Amin.
Chapter 95 · 0% Book details