← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 286

Sashe 184

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amarya lafiya kike kuwa ta dai bude kofan mu shiga naji muryan Inna bayan na Dije dake tambayana a lokacin hakan ya sanar dani cewa ihuna yakai ko ina a gidan ba iya cikin mafalki nayi wanan ihun ba ashe ? Wayata na laluba inda na ajeta saidai ban jitaba a inda na aje din haka yasa na fara lalubenta da sauri kafin naji wani motsi a dagan dakin kamar wani abu ya fita dakin da sauri lokacin. Jin hakan ya kara min kaimi wurin lalubo wayan najita can karshen gado na dauko na haska ina amsa kiran da Dije din ke min a lokacin a gagauce hankali tashe. Na samu na amsa ina kokarin bude kofan dan falona jin ina budewa inna ke fadin ko lafiya dai kike wanan ihun haka da tsakar daren nan na bude ina fadin lafiya inna kila mafalki nakeyi. Wanan mafalkin ko ba maikyau bane da jinsa tunda baki taba irin sa ba a gidan nan kai wallahi duk munji tsoro mun daukama wani katone ya shigo maki ai kike wannan ihun hakan. Kaiya ina wanan zancen ya fito maki kuma haka babu dadin ji a bakinki wanga wani irin fatan banzane kuma ga sarakuwan ki da zaki mata zaton kwarto a dakinta ? To umma nidai ban iyawa a cikin daren nan yadda tayi ihun ne yasa na fadi hakan ke wuce muje mu karasa daren tare a nan Dije din ta fada yaran nan na tayaki kwana amma saida aka san yadda akayi aka hanasu kwana tare dake dakin nan. Ni ban hanasu ba itace dai take nuna bata so don kafin suzo ta rufe kofanta ta juya ta tafi tana fadi adan hasale tabarmu da Dijen nan muka kwana tare da ita a part dina. Washegari sai bayan mun idar da sallah wuri yayi haske ta fita zuwa dakin ta tana min adduan tsari daga duk wani shedani dake bin bayana a rayuwana na amsa da Amin. Har nagama shiri na tafi makaranta duk da akwai barci a idona sosai don rashin samun safiya da banyi ba na karfe hudu zuwa biyar da bawa kanji dadinshi a lokacin fiye dana tsakiyan dare. Sai wajajen karfe ukune wani irin zazzabi ya fara ziyartana a lokacin sai gashi duk dauriyan da nakeyi na kasa hakan don jiki har yana kaduwa hakorana suna hadewa wuri daya a lokacin don zafin zazzabin daya sauka min lokacin. Da taimakon su hannatu na samu na dawo gida tare da ita a ranan haka muka shigo gidan ina gigice cikin wani yanayi. Hankalinsu Dije ya tashi ainun don inna batama gidan a lokacin ganin haka yasa Dije fadin Aisha maza karbi canjin nan kije wurin mai kemis ku sayo mata paracetamol ta hade. Ta karbi kudin da sauri zuwa wurin mai shago din tasayo maganin aka kawo min ko kallonshi banyi ba don ban masan inda nake ba lokacin. Ganin yadda nake hakan ya tayarwa hannatu da hankali tashige daga kuryan dakin ta kira ummah tana fada mata abindake bata wani daga hankali ba sai cewa datayi da hannatun ga Tani nan zuwa ta gani. Zuwan tani tazo min da magani daga wurin ummah na tasa akai min hayaki a dakin takumayi dabaran shaka min a hancina lokacin sai da aka dauki lokaci na dan samu nayi attishawa maidan karfi Allah dai ya taimaka iya mune a dakin lokacin daga haka kuma barci ya daukeni lokacin. Wayana ke ringing ta dauka master ne jin an daga wayan yake fadin haba dai my princess kinsan ina exam shine koki kirani kiji ya pepper ? Hannatu ce master muna gida zahra ce ba lafiya wallahi sai yanzu ta dan samu barci tayi yanzun hakama tana barcine. Subbahanallahi bata da lafiya meya sameta ya tambaya cikin damuwa take fada mai dai dukkan abinda ta gani tace kuma a karshe zazzabine dai mai karfi ya rufeta. Bakuje asibiti bane da ita hannatu ya tambaya cikin damuwa a muryanshi sai tace munje asibiti sun bata magani nan school cleanic . Daga school din muka dawo gida da ita ina gudun mu tafi FMC daga can ya zama magana kuma amma yanzu ummah ta aiko da magani tasha shine harta samu barcin. Ok kun sanar mata ke nan to yaya jikin da sauki yanzu ko ya kara tambaya tace da sauki gaskiya bisa ga dazun din don yanzu har gata tana barci Dije ma tabada kudi kuma an sayo wani maganin chemist dazun da muka dawo saidai bata samu sha ba. Don Allah hannatu idan ta falka kikaga tana jin jikin ki taimaka min ku tafi asibitin zaifi tace insha Allahu, master and please call me indan ta falka tace mai tau. Gida kan yanzu ya canza don da can gidan shirune don sauran yaran gidan dake makaranta a lokaci amma zuwan su hjy murja yasa gidan ya rayu tsakanin jiya dayau din nan . Har zaka danji hayaniyan mutane jefi jefi babu komai a ran hjy murja din a lokacin sai fargaba da tsoron hjy yabi don sanin halinta da tayi na rashin barwa Allah zance. Gashi tun zuwan su garin ba wanda ya lekosu daga bangareta son ko yarta murja bata kara bi ta kansu ba lokacin asalima ta manta da zancen wasu baki a gidan lokacin. Andai kawo masu abinci da suka iso haka an kawo masu na dare sunci tun lokacin ba wanda ya kara leko part din nasu sai su kadai ke sha,aninsu suma di cikin sakin jikinsu suke komai. Washegari misalin karfe bakwai da rabi na safe wanan mai aikince tayi sallama ta sake shigo masu dauke da manyan kuloli ta aje masu kana ta gayar dasu da kwana. Suna gaisawa ta daga zata wuce taji dayan na fadin mama kece mai aikin gidan nan ko ta juyo tana dan murmushi tace nice dai daga haka tayi sauri ta fice part din. Tana fita dayan ta bude dayan kulan taga soyayyen kwaine da irish acikinsa saida aka cika har baki dayan kuma ferfesun kayan cikine a cikinsa mai yawa wanda zai ishesu sai dayan cuscusne yaji hadin kayan labu an zuba mai kamshi da kalan abinci ya canza kala. Itace ta dawo dauke da kofuna da bread manya guda uku sai kayan shayi ta aje masu a inda ta aje na farkon suna mata sannu ta dawo da flask din ruwan zafi ta aje ta fita suna mata godiya. Wanka suka fara shiga sunayi kafin su zauna gaba dayansu suna karyawa a lokacin nan dayan kewa yan matan fada cewa su dai iya kansu a gidan yadda sukaga yar uwansu tanayi banda rawan kai da saka ido ga komai. Sai bayan sun gamane an dan jima Alh ya shigo suka gaisa yake kara masu bangajiya kafin ya dago yacewa matar nasa murja.
Chapter 184 · 0% Book details