← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 286

Sashe 110

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yarda bane gara kasan komai a kan wanda duk kake tare dashi a zamanin nan don boyon baya da amfani ga dan uwa yanzu. Allah ya tsare a dawo lafiya dattijon yai mashi hakama Shattu dake madafa tana shirin dora masu abincin rana tayi mai Allah ya tsare a dawo lafiya. Ya fito ya samu dan bayaron suka fice daga unguwar sai binsu ake da kallo don ganin danbayon tare da bakon fuska da yanayin shigarshi ya nuna ba daga nahiyar su yake bashi. Akwai dan tazara da inda gidajen su yake da cikin gari don haka suna tafiya dan bayon yana masa bayanin komai ba abinda tafi tsaya mai a rai kamar ganin wasu kabila da yayi a cikinsu. Gasu dai fulanine su amma kuma ba musulmai ba nan dan bayaron yake mai bayanin cewa a cikin su akwai musulmai da kafirai da masu zuwa coci. Sun isa kasuwan garin ba zaka kira garin da birni ba haka kuma ba zakace dashi kauye ba garine mai abubuwan mamaki ga ni,iman ubangiji a wurin don ko tsaunukan dake zagaye da garin lub suke da korayen ganyayaki. Shanuko shi zai iya fadin a nan asalin shanun duniya suka fito ga farare ga jajaye ga masu fari da baki ko wani kuma zaka gani garkene tafe sai inda idon ka ya tsayama da kallo. Basu sha wuya ba samun yadin dan bambamcin kudin yadin kadan ne suka yanka mai yadin ne yayi masu kwatancen tellan da zasu kaiwa dinki yaimasu irin wanda sukeso din yayi kyau . Don haka dan bayaron yabi dasu inda zasu kai ga tellan da akai masu kwatance din wuri ne mai kyau da aka gyara ga telolinan a shaguna zazaune suna aikinsu. Ya fadi sunan wanda suke nema din aka nuna masu shi suka karasa shagon nasa tun kan su isa danbayo ya fara fadin aradu wajen nan sai sunci kudin dinki sosai kai malam da ganin yadda aka gyara shagon nan kasan sai wanda ya isane ke kawo dinki wurin nan. Sallama sukayi shagon suna tambayan Isa tella aka nuna masu shi ya juyo yana fadin wake nema na idon shi ya sauka a kan masu neman nasa sai ya sake murmushi yana fadin. Ah a a malam Yasir saukan yaushe haka kasan banda labari nazo amsan tsarabata kaga ko shekarab jiya mun hadu da mummuni amma bai fada min ka dawo ba. Sam shi Ahmed din bai san dashi ake zancen ba sai da ya dan waiga yaga dai shi matashin tellan ke kallo a lokacin . Hannu ya mika masu suka gaisa a nan ya dan kallesu tsab ya gane cewa ba wanda yake zato bane ashe a cikin yaresu na mambilla yake fadin wallahi nayi zaton Yasir ne dan gidan Alh dan gaske. A,a wanan kan bakone shi daga wajajen sokoto yake dan bayaro ya bashi amsa yace ikon Allah malam wallahi kana da kama da yaran gidan dan gaske sosai don har kamar ya baci. Tellan ya fada da hausa danshi da gani ya dan taba barin gari yasan ta kan duniya sosai a, a bashi bana Ahmed din ya fada ya fara yiwa tellan bayanin abinda ya kawosu din yace ya gane a wurin cinikin dinkin ne dan bayaron ya tsure don jin kudin da tellan ya tsaga mashi ya bayar. Kaiko dai ina laifin kace muna dari biyar shikanshi Ahmed dinn murmushi yayi don jin abinda abokin tafiyanshi din ya fada a lokacin. Jin yadda dan bayaron keson badasu yasa yace kai mune dubu da dari biyu yasa hannu ya ciro kudi yabawa tellan yace yaushe zamuzo mu karba. Ikon Allah halin ma iri dayane wallahi tellan ya fada koshi yasir baya son dogon jayayya sosai haka yake min idan yazo ya samu muna ciniki da wani a nan. Murmushi kawai yayi ya kara fadin yaushe zamu zo karba tellan ya dan tsaya yana tunane kafin yace kuzo ranan jumma,a da karfe hudu in sha Allahu zaku samu na hada don ma kaidin ne don da sai bayan sati biyu kuzo ku karba din. Sukayi sallama dashi yana jin suna maganan shi a shagon ta kamarsu da wancan da suka kira da yasir yasa kai ya tafi yana jin wani abu a zuciyar shi game da hakan. Sayayya dan bayaron ya danyi shi kuma bread da kayan tea ya sayo masu sai kayan miya daya rikowa shattu masu yawan gaske. Har sun kamo hanya sai dan bayoron yake fadin barin bi dakai ta cikin gari don kaga garin mu da kyau kasan garin mu ba kauye bane Allah ya albarkaci garin nan da arziki mai yawa sosai ga kiwo ga noma da mutanen mu keyi duk da bamu da wajen noma sosai amma haka mutanen wanan yankin namu ke kokari. Madaran shannu daga ko ina har kasan waje ana zuwa a dauka nan suna tafiya dashi kasashe da dama shiyasa mu nan da kiwo muka dagora sosai a nan. Kaga ikon Allah ashe rabo ke kiran mu ga dangaske gari ko bamu samu komai ba masha kallo a gidan nasa ai kaga inda daulan duniya ta yanke saka a nan. Shi din mai kudine sosai suke kuma da sauratan garin nan a yadda naji ana fada a gari cewa kaf karkaran nan daga chedi wuro garba chedi gembo duk babu wanda yai arzikin shi a kasan nan. Baffa na ban tarihin shi cewa a baya an turashi cikin duniya saida aka tashi tsaya rana tsaka sai gashi ya dawo gida kwantsam ba zato ba tsamanin hakan . Acewar mutane shidin ya gaji arziki ta uwa ta uba duk ko wani bangare nasa suna da manyan garakan shanu a nahiyar nan . Yanzun ko ya hada da ilimin zamani sai abin nasa ya kara bunkasa sosai don yanzun ma a Abuja yake da zama saidai yana yawan zuwa gida sosai idan yazo kuma yanawa mutane alheri sosai shiyasa kaga mutane suna ta tururuwa a gidan shi yanzu. Lalaima wanan mutumin ya riku a kasa yadda danbayarin nan yake fadin dukiyan shi in dai ba abin fulani ba ace dukiya a daji suke aida yanzu sunan shi ya karba kasa ke nan . Amma ba a gane hakan garesu don dukiyan a dawa suke sai wanda ya ganewa idon shi zai gano hakan su dai a kirga yawan shanun mutum daya tara ace wani yana da Nagge dari kaza ko wani ya tara nagge kaza shine alfaharinsu ba yawan kudin bane ya damesu . Shiyasa hukuma sarakuna ko yan doka suke son yin sharia da bafalatin daji da mafi yawan yaransu na yanzu ke dauko masu magana zakaga sai an ware wasu garke an sayar kafin sharia ya mutu. Wanda sam ba a san bafilatanin da da daukan magana ba haka don ko yaushe su a daji aka sansu da zama sai lalura ke kawosu cikingari a da can baya Haka yan asibiti sunfi son bafilatanin daji ya kawo masu mara lafiya yanzu ne koda flagyl zasu bashi zasuce dashi dubu goma bajin zafin hakan zai fidda ya bayarne. Fulani akwai arziki a garesu sosai saidai abin sirine a gareau ba kowa ke gane hakan ba garesu.
Chapter 110 · 0% Book details