Sashe 138
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sautin kukan ne ya kara dakan kunnuwa lokaci guda zakice a cikin dakin akuyan ke wanan kukan jin hakan yasa na zabura da sauri na mike na nufo kofan falon da sauri mukai karo da juna dashi har sai da kowan mu ya kadu. Shi yayi saurin fadin subbahanallahi zahra lafiya kuwa na ganki haka a firgice a daidai lokaci akuyan ta sake sake wani kukan da karfi kuma jere da juna batako ajewa take sake wani. Ai bansan lokacin da nayo cikin shiba a firgice na cakume shi ta baya shiko yana fadin wai akuya kikewa wanan tsoron haka dama zahra ? Akuyatace kila abinci takeso ko wani abin barin fita in dubata ga kayan karyawa nan a falo na aje maki don na shigo na samu kina barci na fita zuwa wurin su Dije. Ganin har lokacin a tsorace nake don ban sakeshi ba yasa shi fadin dawo nan ki zauna a falo har in dawo sai in hada maki ruwan zafi kisha. Sallaman hannatune mukaji tana ta kwada sallama daga waje bata kai ga shigowa cikin part din namu ba, ba kuma wanda ya karba mata sallaman ta a lokacin. Saishi ya daga murya daga ciki yana amsa mata tare da dan takawa nima nabishi baya don har lokacin duk a rikice nake ta turo kofa tana fadin gaku kamar fita zakuyi mana naganku ? Ke san amaryan tawa motsoraciyata akuya kawai tayi kuka shina kika ganta haka a firgice ta barima in fita in duba me akuyan keso ta hana yanzu. Ashe ciwon kan ya lafa dan hakane fa na fito don hankalina jiya wallahi ya daga sosai yadda muka barta a kwance ashema da sauki don gata na ganta garau yanzu. Gaskiya master ka iya jinya daga dare zuwa yanzu jikin har ya lafa haka a cikin sauki sai naga ya sake wani shu,umin murmushi a fuskan shi yana kokarin jayewa daga rikon da nayi mashi Sai lokacin na sakeshi nima don na fahinci me take nufi, na nufi wurin kujera na zauna ina sauke nufashi koshi don naga hannatu ne a dakin nasan koma meye zata iya cetona kanshi ai. Daga haka shi kuma ya fice ya barmu tare hannatu din ta kalleni tace aina dauka ko kofa baku bude ba yanzu har inno tana ce min wai waya fada min ana wanan sakkon haka gidan amarya da ango ? Wani kallo na watsa mata tare da fadin ai gaskiya ta fada maki uwar gulma kin dako uban safiya haka kinzowa mutane gida don ki damesu. Yar iska da ace kedin ba matsoraciya bace zakice min haka jiya nan kika tayarwa mutane da hankali waike ciwon kai don bakin tsoro kawai kin dagawa dan mutane hankali har yana sabari a gaban abokanshi. Tsuki naja tare da fadin dama shi ya kawoki ko yanzu sai ki kara nadewa ki tashi ki gyara min wajancan don bamson kura kin sani. Ai wallahi baki isa ba ni fa naman nan nayo samako naci don nasan baki iya cinyeshi duka jiya tunda tsoro ya hanaki lakka. Kaji munafuka amma cewa kikayi don jikina kikayo sanmako yanzu din kuma kin buge da fadin a baki ragowan nama kici to anki a baki din . Nasan koma zakici ba zaki cinyesa duka ba don haka ba zan wani damuwa ba don nasan yana nan nawatsa mata wani kallon takaici nace idan kina so je yau a daura maki aure kici. Ai muma zamuyi auren nan dai muji don gashi jiya jiya anfara muna gorin akanshi babu ko kunyar hakan kamar ba jiya kike nan kinawa su mommy raki ba. Murmushi na sake daga inda nake zaune nace kedai kika sani in zaki tashi ki dauko cup kizo ki karya ki tashi kafin wani ya shigo kuma. Ai kuma kin fada min gaskiya abari ya huce shike kawo rabon wani ta mike tana fadin hakan ta fita zuwa kitchen din kafin ta dawo nakai kwance saman kujeran. Ta shigo tana fadin waini har yanzun ina mamaki na shigo ina ta sallama ga kannen Master ina gani amma sunki karba min saida naji muryan master na shigo nan. Wata kila basu jiki bane amma ayi sallama su kyaleki kuma a lokacin ya shigo da alama ya dauraye hannayen shine don ganin damtsen hannun shi da nayi da ruwa. Hannatu dake duke tana hada shayi taji kunya sai cewa taji yayi kinko kyauta min hannatu da kike hada maku tea din nan bari ni in shiga in dan watsa ruwa in fito. Ya shige ya barmu nan muna hiran bukin wanda hannatun ce ke firan sai jefi jefi nakan dan bata amsa don irin yadda nake jin kaina a takure a sabon wuri ji nake kamar bakunta nazoyi a wanan wajen da anan yanzu zanyi rayuwa. Ire iren wanan tunanen ne suka tsaya min a zuciyata inda nayi sa,a shine na kula Ahmed mutum ne mai tsabta sosai shi da wana na danji daman wani a rayuwata yadda nake da tsanda din nan yasa ko a gida kowa baya shiga dakina ba a kuma taba min kayana. Gashi yanzu zanyi rayuwa tare da wani wanin ma namiji a daki daya tare dashi kaya kan iyayyena sun kashe min kunya gaskiya duk da gidan ba wanigidan fada ba amma gyaran wurin ya tsaru da kyau komai an matsashi an saka min a dan wajen nawa. Ya fito tsab dashi cikin wani sabon dinkin shadda mai ruwan toka sai alaman saura dan ruwan wankan da kakanga shafin a jikin maza wani lokaci idan sunyi shiri wanda suba mata bane da zasu tsaya kakale kansu wurin gyaran jikinsu. Hannatu kina nan ko barin dan fita na dawo don Allah ga matana nan ammana na bar maki sai hannatun tace kai Master ban dauki wanan amanan ba ai saidai ka bar mata ni amana matsayina na bakuwan ku a yanzu. Nikan hannatu karki kasheni don Allah na fada ina dan murmushi ya dan sake murmushin jin dadin ganin mu na fara sakewa shugowan hannatu gidan. Ya dago yana fadin to madam Master ni zan fita ko akwai wani abinda kike so a sayo maki idan na fita ya tambaya yana kallon fuskana na dan girgiza kai ina fadin Allah ya bada sa,an fita ya dawo min da kai lafiya. Amma kuma baka karya ba naga zaka fita daka dan tsaya ka saka wani abu a cikin ka kafin ka fita ai na fada ina mayar da hankali a gareshi. Wanda na fadi hakan ne don hannatu don nasan ba zata kyale ba lokacin aiko ban kai ga rufe baki ba naji muryanta tana fadin a, a, a su aure manya har an fara yiwa miji fatan alheri irin haka ? Da wani marairaicewa missa baki tashi tun asuba kin hada mai abin karyawan ba zaki barshi ya fita haka yanzu ? To Yarsa ido shiya kawoki gidan nan tunda safe haka don ki dinga sakawa mutane ido ni har kinsa ina son auren yanzu shidai ya fita yana murmushi don yasan tsakanin akwai yar haka dama. Yana fita muka canza topic din hiran mu dan cewa hanne tayi a gaskiya zahra kamar zakiyi aiki da mutanen gidan nan don fa yanzu da zan shigo nayi ta sallama ba wanda ya amsa min . Saima lekowa da wata budurwa tayi tana ganina a kofan nan taja tsuki ta juya tun dazun abin ya tsaya min a raina wallahi. To meyasa hakan ke baki kula ko ranan da sukaje gidan ku da sunan zuwa ganin amarya ai haka sukai ta wani mere baki suna maganan gidan naku wai ba a darajasu ba don angasu basu da komai. A lokacin ne mommy ta aiko a kawo masu abin zama da drinks a nan fa suka so raba hali a tsakanin don sun manta ina wajen don akwai yan unguwar nan dana sani cikin su. Har wata na fadin waisu ba a basu abincin da suka gani ana ta rabone saida wata cikin su ta tsawata masu tace kada su barwa Master abin kunya don Allah suka natsu. Saiga abincin kuma mommy ta aiko masu dashi suka kuma karba murmushi kawai nayiwa hannatu din kafin nace kai irin wanan ni bai faye damuna ba yaushema nake da lokacin suni ? Ai dole kiyi lokacin su tunda yanzu dasu zaki zauna ya zama dole kiyi taka tsantsam da kowa ki fahincesu kada kiyi saurin sakewa dasu tundai kanen nan nasa da alaman rashin kunya a fuskan su. Shiru nayi ina tune kafin na nisa son na hango alaman wani matsala kuma a nan bayan wanda na baro a gidan mu can anayi wanda har yanzu ummah tana cikin fuskantan shi. Da farko dai ki mayar da hankalin ki sosai Zahra wurin yiwa mijin ki biyayya ki nuna masa kauna kamar yadda shima yake nuna maki a gaban kowa don tsakanin daren jiya zuwa yau na fahinci wasu abubuwa game daku. Kada ki yarda koda wasa a samu matsala a gurin ki zahra don mutane sun bude kunnuwan su sun kuma baza ido sugani ko zaki iya zama da master a hakan. Ko ita mama data masa sunyi hakane don su bata maki suna a karshe a koma ana zagin ki cikin gari wanda kuma su da kansune zasu baza maganan naki a gari. Sun dauka ba zaki iya rayuwan talauci irin haka ba don idan anyi daga baya kin kasa zama a dawo ana maki lissafin dakin auren ki. Hausawa sunce idan ka kure dakin farko yanada wuya ka sake samun irinshi a rayuwan ka din haka zahra ki kwanta ki bisu da halinsu ki kara hakuri bisa ga wanda kike dashi a baya. Shi aure dama dan hakkuri komai dacen mace da gidan hutu ko inda takeso saifa ta hada da hakuri a zauna lafiya don haka ki zamawa Master diya . Shima haka ya zama maki da don kinyi mai abinda bako wace yarinya bace a yanzu zata iya hakan ga namiji duba ga yadda rayuwan ya koma yanzu kowa na son jin dadinsa. Amma in akwai ci dasha da sutura duk wanan mai saukine sai mace ta zauna tayi hakuri don ba wanda yasa ya gobe zatazowa bawa karshe. Haka ki jajirce dkn Allah ki kula wurin bashi hakkinshi