← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 286

Sashe 165

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy daddy lafiya yake kuwa ta fada tana shugowa dakin a firgice yau bakiji irin voice din da yayi min ba don na sameshi natambayeshi abinda ya faru. Na fada maki aida baki jeba don akwai matsala dake shirin faruwa da nake hangowa don haka dole mubishi a hankali har mu gano inda matsalan yake. Mommy mu hadashi da Grandma kawai ita zata taka mashi burki don ba zan juri ganin hakan ba gareki dolene daddy ya dawo normal. Zan fada mata amma ba yanzun ba sai nan gaba idan abin yafi karfina zan nemi taimakonta ta fada tana kawar da kai daga kallon yar nata dake tsaye a kanta lokacin. Cikin takaici ya kawar da fuskanshi daga kallonta na dan lokaci kafin ya dora hannayenshi saman haban shi ya shiga dogon tunane akan matakin da zai dauka yanzu ga iyalin nasa. Har daki ya sameta bayan sun gaisa yai mata ya karfin jiki ta amsa da lafiya Alhamdullahi jiki yayi sauki sosai na rage wanan mafalkin da nakeyi mai firgitani yanzu. Alhamdullahi Allah tsare gaba saidai inna ya kamata wasu abubuwa yanzu ki daina don in kaiwa wani ya kyale ka wani ba zai kyaleka ba hakama dabbobi tsakanin mu dasu tausayine da jin kai. Don baka san irin baiwan da Allah yaiwa wani dabban ba kana tabashi bai baka bashin hakan Allah ya tsare gaba tace amin ya mike ya shige wurin Dije su gaisa da ita. Ya fito daga sashen sune ya dawo daki ya karya ya fita don yana son yai sayayya don ya koma makaranta wanda sayayyan duk na gidane shi a can yakan dan sayi abinda zaiyi amfani dashi. Gashi dan break yazo don matsalan fargaban dake damun shi sai laluran ciwon inna din ya tsayar dashi har tsawon sati biyu ake nema yanzu sai faman kiranshi abokin karatun shi keyi akan ya dawo zasuyi test. Hakan ne ya daga mashi hankali yake shirin komawa a lokacin bayan fitan shine ina zaune a falo ina kallon wasu photuna a wayana na bukin wasu diyan abokin Abba da akayi akai shagalin karya sosai sabanin na bukin koda yake aurena ne ba ai wanan ba da aurensu Aisha sun dayi wasu event da akeyi cikin gari. Naji wayana yana kara na dauka na duba ummahce a layi take kirana lokacin na dauka da sauri tare da sallama muka gaisa tayi min ya mai jiki na amsa da ta samu sauki sosai yanzu. To na kira in fada maki cewa yar uwarki Aisha ta haihu dazun da safe yanzu haka tana gidan nan sun dawo daga asibiti idan kin samu lokaci ki shigo ki dubata. Murnane ko mamaki ya rufeni nace ikon Allah ashe cikin dama har ya isa haihuwa to Allah ya raya yasa dadin musulmine tace amin zanzo ko yau ko gobe insha Allahu. To sai kin shigo kidai ta hakkuri komai na duniya dan hakkurine wata rana sai abin ya zama labari idan bawa ya iya hakkuri daga jerabawanshi. To ummah nagode na bata amsa tare da fadin zanshigo kafin Master ya koma Allah bada iko ta fada ta kashe wayanta lokaci guda na lumshe idona har lokacin ina jin wani iri a zuciyana. Kamar yadda duk wata mace keji a rayuwanta a lokacin da taji wani ya haihu ko wata nada ciki yar uwan aurenta don abin yana taba zuciyar mace sai dai idan hakan bai sameka ba. Gashi yan uwan master ko ince mahaifiyar master tana ganin cewa nice banson haihuwa da danta nake planing don kada in haihu dashi har take ikirarin cewa zata auro mashi wata mace a lokacin duk da bamu dade da wani aure ba. Balle yanzu taji cewa Aisha da akai muna aure rana daya da ita harta haihu ni ko batan wata ban taba yi a gidan nasu ba ai nasan zata sake min zance a ranan. Nisai nasan Master gwarzo a wurin kwanciya duk da yasan nidin ba gwanan hakan bane amma bai kyaleni sai bukatanshi ya biya yakan barni. Don haka nasan abin na Allah ne shike bayarwa a inda yaso kuma yaga daman hakan ga bawanshi a lokacin da kuma yaga dama. Anan ya dawo daga kasuwa ya sameni saida ya nuna mamakinshi a fili yake fadin badai wai har yanzu kina wurin nan zaune ba ya fada. Na dan rausaya kai tare da fadin harka dawo ina nan ina kallon waya photuna bukin gidan Dr nake kallo tundazun sai naga yayi murmushi tare da fadin ance ansha buki kan gaskiya a wurin. Ga kayan nan ki duba abinda na manta sai na koma na sayo ya fada a lokacin da nake mikewa zuwa kitchen ruwan da muke sakawa a gora na dauko mashi tare da cup na kawo mai duk da baida sanyi sosai. Ya karba tare da godiya yana sha na bude kayan ina duba tare da fadin ai akwai komai nake gani yace a,a ki dai duba naga kamar na manta da wani abu a ciki. Idan na tuna sai in aika asayo min ai a, a na fada maki banson kina min ciko komai da yake hakkina ki dinga fada min in saya don Allah don in sauke nauyina akanki. Sabulu da omo ya rage na fada yace da man shafaki naga ya kusa karewa ai eh amma akwai wani wanda ban budeba ai yana cikin drower aje. Ok ita inna tace saina karo masu kayan miya don in na wuce sai ta saya wani abin wani lokacin wai ina bambanta sayaya in sayo maki mai yawa su kadan bai kaisu har inyi sati biyu in dawo. Tana ganin kamar nafi sayo maki kaya mai yawa fiye dasu kinga dole in koma kasuwa in karo masu in ba hakaba magana zai zama min nan gaba. Murmushi nayi nace nace a fili dole kan ai sai an kara don suna da yawa balle mace sai tayi cikon wani abin dama girki ke kammala. Amma kinga abinda na sayo masu kuwa hali daine irin na inna nason kure mutum don har Dije saida tayi magana kan hakan itama amma bari dai din na karo. To shi dai yafi gaskiya inda hali ka karo masu ai ba komai bane ina fadin hakan na bashi ina kwasan kayan yace yanzu dana huta zan koma na sayo masu ai. Ya fada akasalance nasan ya gajine sosai lokacin yana so hutu nidai na dauki kayan na nufi kitchen dasu nakai kofa na juyo tare da fadin. Aff kaga na manta ummah ta bugo waya dazun tana tambayana jikin inna, kafin naci gaba da magana yace Allah sarki ummah akwai kokarin kulawa wallahi nima takirani shekaran jiya tana tambayana jikin nata ai. Tace Anty Aisha ta haihu yau da asuba ta samu ya mace har an dawo da ita gida tana nan gidan ban karasa ba yace wace Aisha dai kike magana wai ? Nace Anty Aisha tamu dai ta gidan mu mana ita nake nufi ta haihufa kikace yana kallona cikin mamaki nace kodai baka gane Anty Aisha din bane ? Nagane mana gani nayi dai tare akai bukin mu aiko nace ashe kaganeta yace shine kuma ta haihu yanzu ko wata takwas din bamu cika sosai ba ai don saura kwana goma sha yanzu mu cika wata takwas. Gabanane ya fadi don sai lokacin nagane mai yake nufi ai da sauri nace to shine abin mamaki mata da mijinta yanzu ina abin mamaki ciki . Kuma kasani dan wata bakwaine yaron yace zai yuyu kuma gaskiya Allah ya raya nace amin a sanyaye gabana yana faduwa. Idan hakane kuwa akwaita kenan na fada a zuciyana na shige kitchen din mu ina aje kayan don a nan nake akewa duk da nagane ana diban min wasu kayan aikin nawa wani lokaci idan na aje a nan irinsu maggi tomatoes curry da mai tundai mangyadana na miya. Don hakane su na barsu a dakin sai na dawo na adana a cikin dakin gashi na fara jin inna tace abinda aka sayo masu baya isa kenan dama da nawa ake karawa ayi yanzu kuma nayi wayau ina sakawa daki dukda haibaicin da inna kan min da ba kayan gidan ubbana bane dai saukin abin. Nasaba da irin gorin inna son haka abin bai damuwa nake shayewa sai in nuna kamar bansan dani takeyi ba ma idan tanayi don kawai a zauna lafiya. Kodana koma dakin yana zaune yana gyagyadi lokacin ya ban tausayi nasan in nayi motsin daukan ledan zai iya falkawa don haka nabarsu a wurin na shige uwardakan mu na jawo wayana. Hannatu na kira na samu ta dauka na fara labarta mata zancen haihuwan Aisha din amsa dayane tabani irin nasa cewa wata Aisha dai kike nufi zahra ? Tamu mana sai naji tace innalillahi auren kufa baiko cika wata takwas ba sosai nace ba a haihuwa hakane wai hakamafa master yace min da nake fada mai zancen haihuwan. Wallahi akwai rikici har in yar nan ta rayu don ko saidai idan da cikin tashiga gidan dama nace don Allah kibar zancen nan wani iri nake ji a zuciyana tace na bari amma dai akwai magana gaskiya. Bari na kira ummah naji na fada sai naji da sauri tace min ki rufawa ummah asiri don Allah don baki san dasuwa take ba yanzu tunda haihuwane. Muka dan taba hira can naji motsinshi ya tashi ya shigo dakin nayi mata sallama ina cewa ka falka ke nan yace wallahi nagajine ga zafi kuma koma na tayar da injin din nan ne yanzu ? Da darefa idan ka tayar yanzu yace saina nemi kudin wani mai mana a saya nace ai kaji zancen muje falo kawai ka kwanta nayima fifita zaifi. Da sauri ya juyo yana fadin wa ki rufa min asiri kada anji ki kaini asibiti kuma kice ba lafiya ai gara naje darbejiyan malam Tanimu insha iska zaifi. Ni kumafa na fada cikin gatse yace shine kuma ai to mu zauna din ta waje amma gaskiya zafi nakeji sosai wallahi aiko da mamaki son yau gaskiya ba zafi yadda kake nufi na bashi amsa mu kafita na dauko center carpet dina na shimfida muna muka zauna a dan barandan mu akwai iska sosai a wurin dake hurowa daga baya ta inda dabbobinsu suke. Barci
Chapter 165 · 0% Book details