← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 286

Sashe 53

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsuki naji ummah tayi ta mike ta shiga dakinta tana fadin kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi bayayi dan sheri kika matsa muka dawo garin nan muka zauna. Alh ne zai iya zama shi kadai ba tare da mace tana masa miko min ba yi wancan yi min wanan yanzun dai ai kanku akeji nabi ummah da kallo . Don na kasa fahintar ajin da take lokacin shin taji zafim abin itama ko kuma hakan bai dameta ba take nufi don banga alaman komai ba ga jin hakan. Ina nan falo ni kadai naji an turo kofa na dago kai mamace tsaye a kofan ko wanka batayi ba lokacin don masifa ke ina uwarku tana daki na fada ta bini da harara tare da daka min tsawa tana fadin ba zaki shige ki kira min itabane ? Na mike tso na shiga na samu mama tayo alwala na fada mata tace nace gata fitowa saida ta dan gyara ta fito don ni dana fadawa mama dakina na shige ban tsaya ba. A nan ummah ta sameta tana fitowa tace salma kada ki dauka ni kadai Alh yaiwa haka ki dauki auren nan da zai kara ba ruwan ki kema din da ruwanki har da tsaki kuwa don har kina rawan kan dauko masi key ki basu don kawai a cusguna min ko ? To bari kiji abinda ya kawoni dama ki sani ke din nan sai kinfi kowa matsuwa a cikin maganan ki rubuta ki aje na fada na kara banga matar da Alh zai auro gidan nan ta daga min hankali ba. Tana fadin hakan ummah tace wai maimuna mai kika daukeni a gidan nan ne don Alh zaiyi aure sai ki dauki kowaakiyin ki koda zaiyi auren shi nina bashi shawaran yayi ? To bari kiji in sha Allahu alheri zan gani don nani ganin komai sabanin hakan da kike fada din don haka ki fitar dani a cikin zancen ku. Au haka kika fada ummah tace kwarai kuwa ke baki iya hanashi ba nice kike son na hanashi ko me ko ya shawarce nine lokacin da yayi shawaran hakan ? Itama ummah din ta hayayyoko mata lokaci guda ta juya tana fadin aimu zuba shege ka fasa zaki gane baki da wayau don ke ba makira bace dama ai a zuben yake ummah ta bata amsa tana juyawa zuwa ciki taci gaba da fada har naji tayi shiru nasan ta tada sallahne lokacin. Shigowan kannena yasa nace suyi wanka muje mu gaida hjy suka shige suna ihu na bi bayansu nayi masu wanka na shiryasu muka fito nake fadawa umma zamu gaida hjy. Tana zaune tana lazumi ta amsa da kai na juya zan tafi naji tace dani gaskiya da badon kun saba zuwa irin ranan ba da sai ince kada kuje gidan nan yau amma ku tafi kada dai ku dade idan kunje. Mukai mata sallama muka tafi mun samu dakin a cike da mutane don muna ta sallama ba,a amsa muna ba saida karamin yaron ya leko yana amsa muna. Ya koma saiga gwaggo ta leko tana fadin aiyah su maamahne ku shigomana muka kara sallama zamu shiga hjy ke fadin me kuma ya kawosu yau gidan nan gulma ko me kuma ? Haba hjy maamah ce kuma zaki fadawa haka yau yaran nan duk sati suna gidan nan wurin gaidake fa don Allah dai hjy kibar wanan halin gaskiya hakan baida kyau. Tsohuwar tayi wani irin da fuska tare da kawarda zancen ta hanyar fadin ke miko wancan ledan a zubawa gidan Tella nasu . Kayane dakin irin na buki baja baja a falon hjyn cikin manyan robobi sai rabawa sukeyi wasu kuma nacin nasu a tsaye muka gaidasu da kyar hjyn ta karba muna hankalinta na kan kayan da take rabo din nabuki . Gwaggo shafa ta debo t mikowa kannena sai hjy din tace a, a haka kuma ga nasu da za a kai gidansu nan a raba zaki dauki wanan ki basu kuma ? Haba hjy gwaggon mu daya ta fada wai missa kike haka don Allah mi aan ciki don an basu waga din don Allah dai ki bar wanga halin. A daidai lokacin na fisge na hannun yaron na mayar inda gwaggo ta ballo ta basu nacewa kannen nawa su tashi mu tafi muryan su gwaggone ke fadin ke maamah mi ? Mi halan halim hjy na a baki sani ba kuma yanzu gwaggo ta dauko tana mikawa yaron da sauri ya girgiza kai don munada kwabo sosai mun samu tarbiya daga wajen mahaifiyar mu. Nake fadin gwaggo sai anjiman ku mun barku lafiya wai har zaku tafi yanzun da shigowan ku kai ku dawo ku zauna kunji ku kyale hjy ai kun saba da halinta. Ku barta dan Allah karku zauna mana ta fada tare da kirana da ja,ira ta kara min da ubanki ma baikai yayi fushi dani ba balle ke ko iyayyen naku basu kai can ba. Hakan baisa na tsaya ba sai murmushin da nayi nasa kai kannena nabina a baya muka fice daga gidan ummah na zaune falo tana kallo muka shigo ta dago tana fadin. Bakuje bane ko mey ? Mun tafi ummah mun dai dawone yau gidan nasu a cike yake da mutane yasa muka dawo bin kujera tayi ta kwanta ba tare da magana ba . Nikan na shige ciki abina na barsu a falon kallon hannun kanin nawa dake rike da alkaki tace kai kuma nan yaran sukai mata bayanin komai. Duk da ran ummah ya baci amma bata yarda ta nuna min hakan ba koda alama haka na wuni a daki ina karatu rabi tunane har akai sallah na fito bayan nayi sallah. Missalin uku da rabin na rana mukaji dawowan Abban gidan ana ta bude get ta ko ina kara motoci mukeji Alh ne kuma da rana haka yau ya dawo ? Sai ga Tani da sauri tana fadin hjy Alh nefa yazo da Amaryan shi yadda naga ummah ta dan kadune yasani natsuwa don cewa tayi Amarya fa ? Tani din data kawo mata gulma tace saima kinganta ai yar gayuce sosai itama kamar ku haka saidai ba yarinya bace don da gani ta dan manyanta. Kallon ummah din nayi kafin na mike da kanwata a hannu na shige dakina na rufo naji ummah ta kwala min kira na dawo take fadin kika sani ko zasu shigo nan din duk da part din bai wani dattiba ku dan gyara keda tani tana fadin hakan ta shige ciki ta barmu nan muna kara gyara falon take muka gama muka saka kamshi ta ko ina a falon har zuwa ciki . Kamar yadda ummah bata sanda zance ba hakama mama don Abba auren bazata yayiwa su ummah din kuma yazo da matar gida kowa ya ganta. Ranan kan mama kamar ta hade zuciyarta tana jin tare suke tace aja mata kofanta tashige daki ta kira maman Dele abokiyar cin mushen ta suka hau tsara mafita a garesu. Muryan su gwaggon mune a falon suka shigo suna suratai da fadin ina hjy salma din ina falon zaune na natsa yan kanne muna kallon cartoon suka shigo na fara gaidasu gwaggon namu daya tace ina hjy salma din ta shiga ga Amarya nan zata shigo gaida ita. Tana ciki na basu amsa take kira muna ita kodai barin lekata da kaina gwaggon mu daya ta fada tare da nufar dakin ummah din kai tsaye suka barmu a falo. Ke kuma ja,ira dazun sai kikai fushi da hjy kija kannen ki kuka taho ana fadin ku tsaya gwaggo abinda hjy ke muna dinne ba dasi wallahi laifine don muje gaida ita kuma , . Fitowan su ummah da gwaggo daga dakin ne ya katse mu ummah na fadin baku sanarda mutum ba sai kawai muji wai ga Amarya nan zuwa gaidani ku dai baku dauki cin amana bakin komai ba wallahi suna ta cacan baki mukaji muryan Abba na sallama zasu shigo ashe shine tare da sabuwar matar nasa . Da murna kanne suka nufi Abba suna mashi oyoyo da zuwa kamar yadda suka saba yana shafan kansu zuwa wurin kujera matar tana biye dashi a baya. Yes farace bata kai ummah na fari ba saidai tafisu tsayi da jiki ma,ana tana da nata irin kiran itam mama wankan tarwadace ita don ita ba baka bace kuma ba fara ba. Daga inda nake zaune na mike na nufi wurinsu na dan rage tsawo ina fadin sannu da zuwa Abbah a a mamana kece nan yau ba school ke nan ya tambayeni yana riko hannuna. Na dan juya wurin matar dake bina da kallo nace sannu da zuwa tace yauwa sannu ko idonta tar a kaina daga cikin glass din idon ta tana karemun kallo. Hannuna rike dana Abba din ya nufi kujera ya zauna ni kuma na zauna a makarin kujeran sai kuma na daga ina fadin ga wuri ina nuna mata dayan kujeran dake kusa da wanda Abba din ya zauna. Tace na gode takai zaune tana gyara lafayan jikinta data lalaye saman wani rantsatsen lace dake jikinta daga can inda ummah take zaune take fadin sannuku da zuwa. Yauwa Abbah ya fada ya juya wurin sabuwar matarshi yana fadin hjy karima ga salma nan uwargidana itace matana ta farko ga yaranta nan kuma kina ganisu. Iya makirci sai ta dan zamo daga yadda take zaune da farko tana fadin mun sameku lafiya ummah ta amsa daga can da fadin Alhamdullahi ya hanya ya akabar mutanen gida kuma ? Lafiya kalau ta fada tana dan murza hannun ta tare da fadin akwai nisa kan nan da Abuja gaskiya na dauka tafiyan ai ba wani mai nisa bane sosai yadda yake fadi. Da akwai nisa sosai gaskiya aiku isa ku huta sai a kawo maku abinci daga can gwaggo shafa ke fadin ai akwai abinci da aka kawo daga gidan hjy ma. Au to ai shike nan har ina zancen a shirya wani a nan din akai masu tunda mungama tun dazun Abba ya juyo yana fadin daga gida hjy kuma nan din ba akwai abinci ba tace sunyi wai dama don zuwan kune ai aka hada din acan tunda su nan basu sanda zuwan kuba. Ba,a fada masu
Chapter 53 · 0% Book details