← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 240 OF 286

Sashe 240

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

da bai dace ba gareta ai hakan sai ya jawo rainima a gareku wata rana. Inna yanzu dije ke fadin fa ashe bata da lafiya tun safene fa muma yanzun mukaji dije na fadin hakan da kike magana . Tana fadin hakan ni waya fada min ai ina gidan da zai tareni da maganan banzanshi can tunda ya samu diyar shi ko ta fada a hasale wucewa yayi zuwa wurin mashin din yana kokarin jayeta a inda tace ya tare masu hanya dashi. A lokacin still akuyan ta dauki kukan nan nata ba wanda yabi ta kan hakan wanan ranan anyi sa,a dije bata fito ta saye fadan ba shi ta bari da abinsa. Har ya dawo ciki ya kwanta a falo ina dai jin jukan har cikin raina na daure na fito mm ace a duba akuyan can mana kukan nata yayi yawa fa tun dazun take wanan kukan haka . Barta kila muryana da take ji yau a gida yasa take kuka haka ya fita batun nima na koma na kara kwanciya zuwa azahar yayi wanka ya fita don yaje yayi sallah. Sai gashi ya dawo a gigice yana fadin zahra na amsa har lokacin ina kwance yace wallahi an dauke min mashi dana fita dashi waje dazun da inna ta matsa min. Ai bansan lokacin dana mike ba ina fadin subbahanallahi an dauke fa kace yace wallahi don bata a inda na barta dazun din bari naje nayi sallah in dawo kada in biyu babu kuma. Haka na lalaba zuwa wurin dije nake fada mata abindake faruwa nan ta saka salati har su Aisha suka fito muke fada masu muka kwasa muka nufi wajen don dubawa babu mashin din a wajen. Kin gani ko kunga abinda son kan uwarku yajawa yayan ku hasara yanzu ko mutum shi baida tunane baisan ya kamata ba sai bin zuciyan shi saboda hauka da batar basira irin na Rashida. Wallahi kan inna ta taja mashi haka mashin din nan na ciki aje tasashi a gaba wai sai ya jaye yaba mutane hanya ga abinda ya faru yanzu ai muna samu ana kaimu school da ita yanzu kuma shike nan dada an sace kuma. Haka ya dawo ya samemu tare da wasu mutanen unguwa ana jajantawa Dije sai gashi tun daga nisa dije ke tambaya ba a gani ba ko yace wallahi dije ban gani an daukene ai shiyasa nake ajeta a ciki ai. Ko yau din fitan rabone don tun da safe na fita na sayo kosai da zansha kunu dashi shine na dawo na samu zahra bata da lafiya na shagala har na barta nan don na ajetane da niyar in nayi wanka in fita zuwa kasuwa dama idan na sauke zahra gidansu. Yanzu ai dada shike nan taja maka wanga hasaran ai kowa yaji a jikjnshi don ba kai kadai kai hasara ba ai ni halin rashida yana damuna wallahi. Muryan Asmauce ke fadin hello inna ki dawo gida an sace mashin din yaya da kikasa ya fita da ita dazun ya fito yanzu bai gani ba an dauke. Sallati ta saka ba a dade ba sai gata saman mashin tayi wani urin hawa yana ganinta shi kan ya shige gida nima na mara masa baya a can suka kwasa da dije. Tana sauka tace kodai yaran nan ne dake zaunen innuwar can na malam tanimu don na gansu dama ban yarda dasu ba don bansan fuskansu a unguwar nan ba gaskiya ashe dama barayi ne. Ke rufa muna baki duk wa ya jawo hakan in bake ba tana ciki aje kika saka masifan ya fito ya jaye maki mashin ke zaki fita da kaya ya tare maki wuri ai gashi yanzun abjnda kikaja masa. Babu kowa a falon amma duk da hakan bai hana falon yin kamshin dadi ba a lokacin ko bai tambaya ba yasan aikin hjy murjace don ita din ma,abociyar son kamshine sosai. Balle yau da yake ranan girkintane yasan duk cikin aikintabe wanan don ta farauta mashi rai idan ya shigo abinda hjy yabi bata da lokacin yi ke nan gareshi da sunan farauta mashi zuciya. Maimakon ya wuce fata din shi sai kawai ya nufi wajen hjy murja din kai tsaye uwa uba wani kamshinne na daban ya kara dakan hancin nasa yayi masu sallama ya shiga. Lokaci daya duk suka gyara natsuwan su cikin girmamawa har kasa yan matan suka kai suna fasin sannu da zuwa Abba lokaci guda ya amsa masu fuskanshi yana kan matar tasa da a yanzu yake jinta a zuciyar shi. Itace karshen fadin sannu da dawowa tana mikewa don karba jakar data gani a hannunshi din lokacin ya mika mata yana amsawa ta karba tare da dan rusunnawa gareshi. Juyawa yayi itama tabi bayansa zuwa part din shi inda suka hade da hjy yabi wace ta fito tana mamakin rashin ganin shi a part din nasa bayan ta tabbatar da shigowanshi cikin gidan daga window dakinta lokacin daya dawo din. Ba sannu da zuwa sai cewa tayi ina ka tsayane naga shigowan ka tundazun gidan dama nazo fadamane yasir ya samu accident dazun bayan fitan ka. Amma da sauki muje asibiti an dubashi a kafane ya dan samu targade yana daki kwance ta dauka zai gigice yadda ya saba ga mamakinta sai taji yace. Oh Allah sarki halan yasha giysrshine daya saba sha yaje ya bugu indai bai bugawa mutane mota ba ya dauko min magana kuma a garin nan ? Kallon mamaki tayi mai jin abinda ya fada game da dan nasu dayafi so fiye da komai a rayuwanshi ta bude baki tayi magana lokacin ta farga da hjy murja dake bayanshi dauke da yar brief case dinshi ta zuwa office.
Chapter 240 · 0% Book details