Sashe 194
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
jinya a hankali na bude idona ina bin dakin da kallo kafin in juyo ina kallon mutanen dake cikin dakin a lokacin. Daga can naji muryan gwaggona Shafa wace autace a dakin su Abba tana fadin kin tashi mahmah ya jikin naki jin hakan yasa kowa ya kallo inda nake kwance suna min sannu da jiki. A daidai wanan lokacin akai sallama a kofan suka shigo su ukune tafe mamace tare da yaranta Aisha da Rukkaiya dake dauke da ciki tsoho. Nan aka fara gaisuwa tsakaninsu da wa yanda suka sama a dakin sai jan kamshi da mere baki mama din take faman yi kafin tace to ya mai jikin da sauki ko , ? Yanzun nan falkawanta ke nan daga barci ance tun safe take barci sai yanzu ta tashi saita juya tana kallon inda nake kwancen tace Zahra ya jikin naki ? Kokarin bude baki na nayi in amsa sai na kasa na dai gyada mata kai alaman amsawa a lokacin gareta wanan karamin asibitin za a kawota haka yaushe mutum zai samu sauki a nan ? Aiko nan din ma suna kokari gaskiya gwaggo taba Aisha da tayi maganan amsa ballema ina ruwanta aida sanin uwarta aka kawota nan din kece mai bakin magana yanzu. Kowa yai shiru kafin can ta fara fadin yaya za ayi in ta fada ace ankawota wanan wurin haka amma sai a dinga yin wasu abubuwa a boye kamar ba a son ka sani. Ku daiyi hakkuri mu ko hakan ma munga sauki sosai wallahi ciwone inyazo sai hankalin na tare dakai ya gushe duk dabara saita bacewa mutane. Dije dake zaune gefe ta fada cikin wani yanayi na fahintar abindake faruwa a dakin Rukaiya data fara tafiya tana toshe hanci alaman warin dakin ya isheta lokacin. Mu zamu tafi mama din ta fada Allah ya sauwaka wasu suka amsa da amin suka fice ba tare da ko mutum dayansu ya karaso zuwa inda nake kwancen ba a lokacin. Ganin hakan yasa na lumshe idanuna cikin takaici dajin zafin irin cin zarafin da suke min din yanzu don na fahinci suna kokarin nuna niba kowa bace a yanzu din cikin gidan mu. Muryan mama din na jiyo tana fadin shafa mun biya mu dauko hjy muzo tace ita bata zuwa taga takaici tsuntsunda yaja ruwa shitaka doka suka fice. Sai naji wata daga cikin matan da muke makwabtaka tace wanan fa wacece ita kuma matar babantane gwaggo shafa ta basu amsa taci gaba da fadin kinsan su yan gayu komai nasu na nuna haline asibitin ne bai masu ba wai yayi karami da kawo zahra nan da akayi. Duk hiransu idona yana rufe har lokacin jin sallamanshi yana gaisawa da Dije yasa na bude idon don lokacin an rage yawa a dakin naji yana fadin gwaggo ashe kina nan har yanzu na zata zan dawo in samu kin tafi ai. Tace haba dai na tafi kuma ai dole wanin mu ya zauna nan din a watse gaba daya kuma aiba komai kinyi kokari Dije ta karba don tana son labarta mashi zuwan su mama cikin hikima. Wasu aiko zama sin kasayi a dakin sunce dakin yana wari yau aini naga abin mamaki dakin nan ko naga komu muna faman tsabatanshi ai don ko yar nan hannatu yanzu data shigo tana shareshi har ban dakin. Baidai iskanci bane su nunawa mutane isa da gadara sufa haka suke duk inda sukaje sai sun rainawa mutum suna shiba kowa bane garesu. Cikin kaguwa da tambaya yake fadin su waye sukazo dije din tace dashi hjyn gidasuce tazo da yaranta shine yar take fadan an kawo zahra asibitin yaku bayi. Murmushin bakin ciki ya sauke a fuskanshi kadan yace lafiyan ta muke nema ba kyawon wuri ba ai dije ta tashi kuwa ya fada don kawar da zancen nata. Eh ta tashi amma bata dadeba ta koma barcin ai idonta biyu koda suka shigo din ya tako zuwa inda nake yana fadin sannu zahra ya jikin naki. Lokacin nayi kokarin bude idona na sauke akanshi ya kara matsowa kusa dani yace zakici wani abu da hannu na nuna mai ruwa nakeson sha. Yace ruwa na gyada masa kai alaman eh yace da sauri ya dauko goran ruwa ya miko min yana kokarjn tayar dani gwaggo ta taso ta kama mashi goran ya gyara min kai ya ban nasha kadan na cire bakina . Na koma saman filo gwaggo na kalla nan na hango tausayina zallah a idanunta take fadin ko zaki watsa ruwa ko zakiji dadin jikin naki ? Na gyada mata kai alaman eh tace to bari a hada ai akwai ruwa a flask sai a juye kiyi wankan dashi inta fito taci abinci hakan akayi naji dadin wanan wankan don jikin nawa na danji ya kara sakewa ba kamar yadda na falka ina jin nauyinsa ba. Washegari na samu sauki sosai a haka kuma yake fakan idon mutane yana shaka min magani sauki na kara shigata likita dayazo round yace zasu sallameni tunda naji sauki ke nan nayi kwana uku kwance asibitin. Muka dawo gida ko nan bai bar min maganin ba saidai ban yawan magana sai abin ya kara damunshi dama can ba mai yawan surutu bace ni. Ganin hakan yasa ya fara tambaya sosai a can wurin tambayan ne ake fada mai abubuwan shege dana tsohon kakana na Funtuwa da yaje. Maganan dai dayace shine shafata akayi akwai makiya a tare dani mata biyu sune kebina da sheri amma iskan dake kaina basu yarda sun tabani ba. Kaddaran mu daya dashi ba abinda zai cutar dani sai wani ikon Allah don muna da mabiya masu karfi a tare damu. Yakanyi tunane wanan wani irin kaddarane haka maigirma da kowa ke fada ma har dai yakai ga tambayan mutumin daya tafi wurinshi a karshe yake fada mai cewa . Ita kaddara basai ta wani abu ba ai kwai ya barwa Allah sanin sa amma gaskiya tsurarin mu iri dayane a tare suke tafiya daidai. Tun Daga wanan lokacin ya natsu gida yana jinyata bai koma wurin kowa ba kuma na samu sauki sosai har ina zancen komawa school inci gaba da karatuna don ma Allah ya gyara ba a fara test din exam ba a lokacin. Kwatsam kira yazo min na bisi cewa goma ga sabon watane tafiyan su zuwa interview don haka ya shirya dama da mukaji shiru an dan dake program din ne zuwa wani lokaci. Nayi mai godiya tare da fada mai cewa nima nayi ciwone amma naji sauki na zata ai har anyi interview din ko ban sani ba ya tsusaya min tare da tambayan idan banji sauki ba mu shirya tafiyan dani muzo nan a dubani nace na samu lafiya. Duniya ke nan wanda ban hada komai dashi ba ya nuna min kauna ta gaskiya har yana kokarin fita dani waje a duba lafiyata ga wa yanda muke uba guda suna nuna min kyama a yanzu don kawai ina matar fakiri. Da yaya musane ya nuna kamar zai tausayawa lamarina amma yanzu har na manta dako yaushe rabon da muyi waya dashi don da farko muna waya amma daga baya kona kirama baya dauka hakan yasa na daina kiranshi. Ashe abinda ban sani ba shine kamar yadda Abban mu yayi warning din kowa a kaina mama ma ta kara warning din diyan nata sosai kaina da ummah yanzu . Shiyasa suka fita zancem mu ga baki daya ko ummah din sun daina waya da ita balle dan aiko mata da aike irin yadda sukeyi a baya. Tun takwas ga wata ya bar Gusau zuwa Lagos abinka da dan tallaka tafiyan mota yayi bata jirgi ba hakan yasa ya wahala a hanya kafin yakai yana zuwa ya samu wanda aka hadashi dashi a cikin daren nan baiko gama hutu ba suka bar kasa zuwa us din.