← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 251 OF 286

Sashe 251

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas Aljanni na tsoron hatsabibin dan adam hakama maye yana tsoron cin mai baki hakika haka zancen yake kuwa don ni na sheda hakan . Tabbas Ahmed yasan meya taka ya kuma san ko meye yake bibiyan mu fadi daine kawai baiyi don haka maza suke koda sun san abu haka zasu danne a zuciyarsu. Su nuna basu san komai ba hakan kuma ke faru damu din saidai koda wasa bai nuna hakan gareni ba ko a wani nawa. Sannu a hankali cikin jikina yake girma amma saboda lafafen cikina ba zaka dauka cikin ya girma sosai ba a lokacin don bai wani taso ba da za a gani sosai ba. Zuwa da dije ya taimaka min matuka don da ita nake zama inyi hira sai yamma idan ya dawo yake dan zama damu ayi hira a irin hakane muna zaune ranan wayanshi yayi kara ya dauka yake fadin innace fa. Amma ai yanzu dare yayi sosai a can mana yake fada lokacin da yake daukan wayan yayi sallama ta amsa mai gaisuwa ya fara mata bata amsa ba sai cewa da tayi dashi. Duk yadda ka daukeni dai uwarkace ni kuma nina kawo ka duniyan nan da har wasu suke kallon ka a mutum yanzu har suke ganin sunfini iko ko wani abu dakai. Kai ya dago ya kalli Dije ya kara sautin wayan yana fadin meya kawo zancen nan kuma inna na taba fadin bake kika haifeni ba ki na taba wani magana da bai dace ba a kankine ? Aiko bakayi ba ka nuna hakan tunda ga zahiri mun gani ni kuke dauka manya ko wata muguwa da har zaka hada kai da mahaifinka da iyayyen matar ka ka dauke matarka a gabana zuwa wata kasa don kar na cinyeta ko me ?. Innalillahi ni akace na fadi hakan akanki ko wa don ni bansan da wanan zancen ba sai yanzun da kikeyinsa eh ba zaka sani ba amma gari yanzu kallon da ake min ke nan ai. Ko ita umman mu din da aka hada baki da ita ana min kallon zargi yanzu ba zance komai ba amma kuje can din inda bani ku haihu din wai ashe matarka cikine da ita don kada in sani har ake min boye boyen hakan. Kuka hada baki da mahaifinka ya kirani yana kokarin fada min maganan banza ban san hakan ba a lokacin dana fada mai yana sonkane balle abinda matarka zata haifa ? Ko yanzune har yasan zafika su kuma gidan matar naka dana fada masu cewa ai sunsan nice uwarka suka baka diyarsu inma ruwan kasari mukesha musha tare da yarsu a nan. Yanzu inna duk meya kawo wanan magana me zafi haka akan son Dije da zahra sunzo nan don jikinta kike wanan zance haka a cikin bacin rai ? Har kina kokarin ki batawa kanki suna ki kira kanki da manya to nidai ko wani na kusa dani Allah ya sheda bamu taba fadin haka ba kuma ba wanan zancen a zuciyar mu. Zakace haka yanzu ai tunda kagama bata min suna a gari ana fadin don ni aka dauke ta akabar kasan nan da ita saboda halina. Allah ya baki hakkuri inna ya fada ya kashe wayan koda ya dago kai ya dubo inda muke ban wurin na shiga daki sai dije da tayi shiru tana saurarensu tace. Halin Rashida sai ita wallahi wanga magana haka ina ya fito zancen bata san matarka nada ciki ba idan ita a matsayinta na tsohuwar mace a yanzu bata gane haka ba har sai an fada mata . Wa take son ya tareta ya fada mata zancen cikin matarka ko kai take son saika kirata ka fada mata don ta samu wurin yi maka iya shige. Dama abin Allah haka yake da zaran anyi mace gorin haihuwa a cikin kwanakin Allah sai yaji tsusayinta wani lokacin ya bata ciki da wuri ta haihu. Don nan da kace zaka zo nan take fadin zaka tafi ko kwai matarka ta kasa nasawa a gani inka dawo dolene tayiwa danta aure ka auri mai haihu ba wace keci kullun tana kaiwa masai ba. Na san kuma da matarka take wanan zancen a fakaice bandaiyi mata magana bane lokocin don akwai mutane a wurin sosai yasa na kyaleta ban tankata ba. Amma na rasa gane dalilin dayasa Rashida ta tsani yarinyar nan duk da hakkuri irin na matarka wani lokacin sai Rashida ta kaita iyaka wanan halin dame yai kama haka don Allah ? Alkawari na daukarwa kaina Dije akan zahra don nasam me inna take nufi sarai akanta don haka nima nayi alkawari a raina kuma ina rokon Allah ya cika min burina a kanta din insha Allahu zan gwadawa duniya niba butulu bane. Mum suwaye daddy ke magana a kansune haka don ni har yanzun na kasa fahintar ko suwaye sukai masa hakan a cikin labarin daya bamu din. Tunda bai fada ba ai shike nan ko meye na tambayana abinda ban sani ba yanzu saidai zancen wanan yaron dayake ikirarin cewa dansa ne shine ban yarda dashi ba har sai gwaji ya tabbatar da hakan. No no no mum kada kice zaki hakan don kema kinsan daddy ba dan iska bane don sanin halinsa nema har watarana nakan yi tunanen ina muka kwaso namu halin ne wai ? Don haka ki barshi da dansa mutumin daba zama zaiyi a nan tare damu ba shimafa yana da nasa iyalin yanzu daddy yafada don me zaki tsaya bata lokaci kuma akansa yanzu ? Au bata lokaci mane kake gani ko to bari kaji idan har ya shigo cikin mu yau Alh ya fadi ya mutu dole a raba dukiyan Alh dashi shine zakace na barsu nabarsu don me zan barsu su yaudaremu. Mutumin da yake aiki yanzu under UNICEF wani dukiyan daddy zai dameshi yanzu kai da bakasan ciwon kanka ba kake ganin hakana amma ko kwandalace sai ya karbi kasonshi. Don haka ba zan zuba ido har a kai ga hakan ba sai dolene in dauki mataki a kansa kafin lokaci ya kure min inzo ina dana sani daga baya. I am out of dis mission don badani za ai wanan ba all what i know shine idan har yazo din yana zaman dan uwane a gareni koma din baizo ba shidin dai dan uwanane tunda mahaifinmu daya dashi. Idan kinbita tawa kawai ki barsu don banga wani abin tsayawa yin jayayya akai ba na fada maku i am out dis ya mike ya fita tace mahaukacin banza kawai wanda baida tunane. Ta kallo inda Salima take zaune ta ishishire kafa saman dogon kujera tana dakalan wayarta tace ana magana kinyi shiru tun dazun ke. Mum me zance ni wanan ba zance na bane ai don haka ba matsalata bace ta mayar da kanta ga waya taci gaba da dakilan wayanta da takeyi din. Ran hjy yabi din ya baci lokaci guda takaicin diyan nata ya rufeta ta rasa me zatace dasu a lokacin maganganu ta farayi kamar zararra ganin hakan yasa salima din ta bar mata dakin. Takaicine ya cika hjyn don ganin bata samu goyon bayan diyanta ba yadda take son samu a wurinsu su hade kai su yaki daddy nasu akan basu yarda wanan yaron da yake ikirarin cewa dansa bane ya shigo cikinsu yanzu don ba dan uwan daya san dashi a baya. Tunane yakai tunane gareta sai batan basira ya shigo mata azuciyar ta aje shawara kan zata nemi hadin kan hjy murja kishiyarta su jajirce mijin nasu akan basu yarda da hakan ba su. A karo na farko da zatayi amfani da murja din ke nan don a ganinta a baya murjan ba a bakin komai take a gidan ba balle ta nemi wani abu a wajenta. Sai gashi a yanzu bukatan hakan ya taso mata ya zama dole tayi amfani da murja din wajen cika burin ta ga mijin nata idan tana son abubuwa suje mata daidai a lokacin. Don haka ta shirya yadda zata tunkari murja din da zancen cikin daure zuciyan ta don sai ta danne zuciyar ta akan hakan zata iya cinwa manufarta akanta in yaso daga baya bayan bukata ya biya sai ta koma kanta itama ta gama da ita. Kwana biyu faran faran takewa hjy murja din wanda yasa har murja din ta fahinta da akwai wani kulli da matar keson mata a lokacin saidai bata san ta inda kullin zai fito ba akanta don haka. Take shan jininta da matar tana dan kame kanta taki yarda su sake jiki da juna kamar yadda hjy din take nuna mata a lokacin na ita yar uwane ai a gareta. Yauma kamar kullun girkin hjy yabice don haka da kanta ta fito tana ba yan aiki umurni ga abinda zasuyi hjy murja data fito daga dakinta zata shan iska waje ta samu hjyn gidan da kanta a falon tana ba masu aiki umurni. Bata tsaya ba amma ta gayar dasu da aiki zata wuce taji muryan hjy din na fadin wai murja dama ashe haka kuke wahala da aikin nan gashi banice keyi ba amma duk na wahala a wurin magana kawai. Ay,yah Allah sarki ako son baki saba bane aikin aiba wani wahalane dashi ba hjy ta fada cikin muryanta mai taushi tare da yanayin irin na kamala kamar yadda take ko yaushe. Tana fadin hakan tasa kai zata shige ta kara jin muryan hjy din na fadin af kingako tun dazun na fito da niyar aika maki anjima mu shirya zuwa gaida dan abokin Alh dake asibiti. Wani irin dagowa hjy murja din tayi lokaci guda tana kallon hjy yabi din a cikin mamakin dake baiyane a fuskanta a lokacin don maganan haka yazo mata a bazata. Yau itace wai hjy yabi da kanta take son fita da ita a mota daya har take taya mata fita a tare da ita da bakinta lalai duniya me juyi ga bawan daya gane hakan. To hjy tarene zamu tafi bakinta ya tambaya a cikin mamaki lokaci guda eh karfe biyu sai mu tafi mu lekoshi kafin mu isa an budewa yan ziyara kofa ina ganin haka zaifi ta amsa da to hjy. Ta juya ta wuce cike da mamakin hakan zuciyarta yana faman saka mata maganganu iri daban
Chapter 251 · 0% Book details