Sashe 169
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
dole ke nan yaron a yanzu yana can cikin wahalan rayuwa. Bayanshi yana nan da nasa iyalin a cikin daulan duniya da jin dadin rayuwan da bai musaltuwa a lokacin son shidin ba mutum bane mai tauye iyalinshi. Yanzu ina zai fara bullowa wanan matsalan da wani ido yanzu zai baiyana garesu yace yana neman dansa dan da baisan cinshi da shansa ba har ya rayu yakai wanan shekarun masu yawa haka ? Dolesu jauro zai nema a asirce kamar yadda yanzun ma suka tunatar dashi hakan asan yadda za a bullowa maganan da wuri kada ya mutu ya bar baya da kura kuma don yasan halin matarshi ba yarda zatayi da hakan ba shi yanzu ina zaikai wanan alhakin a rayuwan shi. Godiya da tasbihi ya shiga yi a zuciyan shi yana mai lumshe idanuwan shi kadai yasan yadda yake ji a zuciyanshi yasan alhakin hakan dole ya kamashi a wani bangaren rayuwa. Hjy Yabi ce ta shigo part din a lokacin jin motsin mutum yasashi dago kai ya kalli mai shigowa dakin a lokacin matarshi ya gani hakan yasa ya sauke kanshi kasa daga kallonta. Barka da hutawa yaji bakinta na fadi yau karo na farko azamansu kunuwanshi ya jiyo mai hakan a bakinta a ciki ya amsa mata ta samu wuri ta zauna tana mai kallon fuskanshi dake daure lokaci guda. Alh wai da wani matsalane ka canza gabadaya cikin yan kwanakin nan mu bamuji dadin kaba kai kanka bakaji dadin kanka ba kuma kaki fada muna abindake faruwa mu sani ? Lafiya nake haka dai naga shine daidai yanzu don naga kina kokari dake da diyanki ku maidani mace ke ki zamo miji a gareni yasa na daukarwa kaina matakin hakan shine kawai ya fada yana dago kai tare da kallonta. May ya kawo wanan zance kuma ana zaune kalau zaka fadi haka a cikin mu waya nuna maka cewa baka a matsayin ka na ubangidan nan yamzu ? Nina gani na fahinci hakan don haka nake shirin daukam matakin daya dace dani a yanzu wanda shine daidai gareni gako wani magidanci kuma. Gaban hjy yabine yake wani irin faduwa don abinda take tunane shidin take ganin ya faru a lokacin hakan na nufi duk wani shiri na sihiri da kulli da sukai mai suka daureshi abin ya karye a yanzu haka ke nufi. Cikin karfin hali irin na hamshakan mata tace dashi kai Alh wanan zance ai bai kamata a bakin ka wani power naka zan dauka ko yaran nan su bani bayan kowa yasan a karkashim innuwan ka muke rayuwa a gidan nan. Idan ma Baku sank ba said Ku fara sank son Abubakar din da kuka sank a baya bashi bane yanzu kuke kallo wanda kuka mayar dashi da banza duk days a wurin Ku. Shiru tayi tana Dan kakaro murmushin dole a fuskanta don tunanen ta ya wuce abinda takeji a gareshi yanzu dole wani aikinsu na baya ya samu matsala a wani bangaren . Inko haka tasan akwai aiki a gareta babba yanzu don't yaushe zata iya tuna wani abinda akai mashi a baya ga kuma hjy Korau uwar rikon nasu sun samu matsala yanzu da ita akan yayanta. Zakace ba haihuwa akayi ba a lokacin don't yadda naji gidan shiru koda yake darene a lokacin watakila kowa ya nufi gidansa sai kuma gone su dawo ga yadda nasan aal,adan yan uwan my ko garin mu In an haihu kai maigida ka shiga uku don yawancin yan uwa a nan suke tarewa kullun suna gidan sai dare za a watse said bayan suna kafa ya dauke. Shine abinda ya bani mamaki a was a wanan karon data kofa muka tsaya muna sallama kusa sau ukku ba a amsa muna ba kallonshi nayi ganin haka yasashi daga muryanshi da karfi ya kwada sallama a daidai lokacin aka bude kofa. Mama hafsice zata fito tsci karo damu tsaye a kofan dakin cikin mamaki ta amsa muna sallaman tana fadin ashe bakine daga can ciki naji mur I an mama tana tambayanta da su wayene a kofan ? Nice mama nayi saurin bata amsa kafin mama hafsi din ta bata amsa ta bude muka shiga au Zahrace ashe yanzu like tafe aina dauka bakiji haihuwa ba ma son ban ganki ba ? Naji mama dazun nan ummah takirani tana fada min anty Aisha ta haihu barkan mu da arziki ubangiji Allah ya rays muna bisa kan sunna amin. Nafada freely da murmushi a fuskana tace amin gaba daya hankalinta na kaina tana kallona daga samana har zuwa kasana lokaci guda nikuma na fahinci hakan. Nasan ba komai take kallo ba sai shigana na lokacin duk da ba laifi amma ita taga kasawa a hakan dama shi take son gani a gareni don' komai daya shafeni baya burgeta ita. Ki shiga suna ciki tare da hjy tsohowa cewa kakan mu sai nace a cikin kunya tare muke dashi yana kofa yazo yai maku barka shima OK tare da mijin naki kike ashe ? To kije ki shigo dashi ciki mana ta fada a cikin izza da isa iron nata na mike na fita ta bini da wani kallo mai kama da harara tana jan tsoki tare da kawar da kai gefe daya. Nayi masa iso da mu shiga daga ciki na juya zan shige naji ya dan jawoni na juyo kudi ya danka min bansan ko san ko nawa bane nayi godiya yace No da sauri. Ina gaba yana biye dani a bayana zuwa ciki yayi sallama suka amsa mai su ukune zaune a falon lokacin har kasa yakai ya gaidasu kafin ya fara masu barka da karuwan da aka samu din. Rakiya kira masu hjy nan su gaisa ta fada a gadarance don mama badai magana a gadara ba kan balle ta samu wurin yi a yanzu. Jin hakan yasa nasan ba sai mun shiga ciki ba kenan a nan zasu zo mu gaisa dasu son azato har maijegon din amma sai naga hjy ta fito ita kadai dakin itama saida ta jima ta ja muna rai tabarmu a zaune shiru a falon kafin can ta fito tana Dan dingisawa irin na manyanta. Su waye ke neman ta fada a gyatsire tana kaiwa saman kujeran farko dake falon bayanta kalle mu gata nan takwarankice ita da mijinta sukazo barka mama ta fada har lokacin tana mike a saman dogon kujera da waya a hannunta. Waye takwaran nawa ta fada kamar bata shedani ba tana wani gimtse fuska a cikin daurewa mama tace gata maisunan kicefa ta nan gidan. Yanzun taga daman zuwa ita issasa duk yan uwa dake nuna farinciki sunzo sun tafi wani iri naji a lokacin, bansan lokacin da nace muma ai farin cikin mukazo nunawa kedai hjy duk da kin dade bakiga mutum ba sai kin yaba masa magana son ranki. A,a makka kikaje karshen dadewa ina kina cikin garin nan dai karshen dadewa unguwar sullubawa da kika zabi zama. Sai naga mama ta kalloni ban fasa maganan ba naci gaba da fadin yanzu da naji din bagashi munzo tun ba,a kwana ba ? Ke kada ki shiga min ido ana magana kinayi har wani aure kikayi na gwadawa tsara da kike ganin wuyan ki yakai yanzu da zaki fadawa mutane magana yadda kike so . Tashi muje ya fada a hankali daga bayana inda yake zaune din itako taci gaba da fadin masu manda da uhumm basu rawan kan aure. Naji zafi naji ciwo a raina amma saina dake INA fadin in auren banzane kije kiyi mana ai naggidan ai zawarawan fake sonki had yanzu na mike da zuman shiga dakin naji mama Rakiya na fadin Aishan ko ta samu barci fa. OK in ta tashi a gaida mun ita muna mata barka da sauka lafiya ya mike yace mama zamu tafi Allah ya raya muna na mikawa mama rakiya kudin daya bayar abawa jaririya nace ga wanan inji shi asaiwa jaririya kwali. Kai haba dai kana fama da kanka da iyali cikin Dan kunya yace ba komai mama ayi hakkuri dashi son Allah to an gode ta fada nayi mask saida safe muka fito zuwa part din mu. Nan ma bamu dade ba min gaida ummah ta tambayemu mutanen gida na barsu tana kara mashi nasiha na shiga wurin kannena har sunyi barci a lokacin. Mukai mata sallah muka fito bar muka hau mashin din my banji yayi magana ba a lokacin zuwa gida don haka nasan ranshine ya baci sosai nima nayi shiru.