← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 286

Sashe 131

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da dan baranda is ok mana na fada yace nasan abinda yasa ta tambaya don yanzu ko yar tallakawace yarinya sai kiga an jera mata daku fiye da daya zuwa uku. Balle ke yar gidan masu gari haka da Allah ya banke a a kyauta ubangiji ya dubi maraicina ya hadani da yar baiwa salihan mace irin ki mai tausayi da jin kai. Ban taba zaton alakan mu zai kaimu ga aure ba zahra shiyasa har yanzun nake kwankwanton hakan duk da nasan wani kuline hakan da zai zama muna alheri insha Allahu. Zan kwanta na fada a kasalance yace har kin gaji da hiran nawa ke nan nace No dama nayi shirin kwanciyane a yanzu zan turo ma wanan kudin sai ka kara kayi abubuwan daya kamata kayi tunda akwai hidima a gaban ka gashi Allah ya kawo saukin sa. Hakane wallahi Zahra kedin alherice gareni don tun haduwana dake na fara ganin haske a rayuwata amma ki dan ban minti daya naji yaushene Abba zai shigo garin don iyayyena da yace in turo mashi. Ok ina ganin this weekend zai shigo don naji ya musa yace tare zasu shigo da Abba din idan zaizo sai naji yace Allah ya taimakeni na tambaya da wuri don kinsan ba nan kusa suke ba sai sunyo tafiya mai nisa. Munyi sallama dashi na kashe wayan ina faman tunanen daga wani kasa iyayyen nasa zasuzo na dai bar komai a cikina sai sakon ko daki nawa din da yace a bari ya gani ko za a tayar da wani idan ba,agama ba din. Zaune yake gefe daya yayin da Dije da mahaifiyan shi ke dayan barin dan barandan zaune suna sauraren shi eh Dije wanan dai yarinyar da kika sani wace suka zo nan gaidani da yan makaranta mu din in zaki gane ta. Yar gidan wane na a garin nan Dije din ta tambayeshi tana mai kura mashi ido don son jin abinda zai fada mata din lokacin shima a bakin shi. Ya danyi shiru kafin ya dago kai yace yar cikin manyana maici yanzune Dije wane mayana mayanan garin nan wadda nas,sani mai kudin nan da akace yana da arziki sosai ? Shiya dije ya fada yana kallonta tace wai shi yar rikone ko yar cikin shi ta Amadi hwada min in jiya da kyau don Allah ? Walle yarshi ce ta cikin shi Dije ina miki karyane akan mi zan hwada maki abinda bashi ba ? Dan Dije yar cikinshi hwa kace ina kai ina yan gidan manyan mutane irin haka ko dai yar yan uwanai na kaka hwadin diyatai kasan yanzun haka akayi niggani. Walle mama Diyatai ta cikinai na wai a,a zan maku karyane wai Amadi ina kaga kudin auren yar wanan babban gidan ? Dije zancen kudine wai wanga abu kekin san mukaddarina kwai daga Allah amma ni ko dan ga aikin gidan nan na isa inyi balle intai neman yarshi nihin Allah na kawai. Yanzun dai yace in turo mai magabata na suzo ya gana dasuwa a aje ranan buki don so yake a wanke su dai rana akai ko wace gidan mijinta . Wane gida zaka kai ta kanka daya kuwa kake wani zagewa haka kasan abinda kake hwadi kuwa ina kaga kudin auren yar manyan mutane haka ? Ko so kakai ka tonawa kanka asiri cikin garin ga a samu abin hwada muna bayan wanda muka hwama da shiya kace sunce katuro iyayyen ka waka zuwa ma wanan gidan neman aure ? Kasan dai irin zaman da mukeyi da dangin uwarka garin nan ko bakin ciki na hana masu zuwa inma sun sani zuwa sukai su hana su aibanta ka wurin su. A,a dangin ubana dai ka zuwa min ai ko wane da da ubana yaka kuri nima insha Allahu kamar kowane da haka yan uwan mahaifina ka zuwa min neman auren. Kkagansu ina wanda ko kamanin ubanai bai kawowa ko haya zaka kayi ka tudar muna da mutunci a gari yace a a muna zaman mu lahiya. Shin dije in bansan suba ina hwadin haka ki bari ki gani kina zaune zasu shigo nan su hwada maki komai ki kijiya kila ki yarda dasu. Wayan shi yai kara ya ciro gaba aljihun shi yana dubawa ya mike tsaye ya nufi hanyar fita yana fadin gani tafe nan ya barsu dije na mamakin maganan shi din. Wai danga kanshi dayana kome yaka hwadi kamar almara mutumin da yai tahiyanai tun kana goye a raga kaka hwadin ka ganai har yan uwanai ka zuwa maka neman aure . Barshi dai ya dawo mu jiya ai mara rai akewa karya indai ba hauka yayi ba shin ina danga ina yar irin gidan saidai in bata da lahiyana suka bashi ita uwar nasa ta fada. Shi naka tunane a raina amma in har ba matsala agareta ba su da suka dace da diyan gwaunoni ko wasu hamshakan masu kudi a,a suka daukan diya suba mutum kamar Amadi. To walle ban yarda ya daukowa kanshi jarabar tsaya yazo duk dan zarahinai da aka gani su kare ga gindinta suka koma yi mai gwi Allah. Akwai dai magana amma haka zikau mai kudi bai daukan diyanai ya bashi don jin dadinai ko wani shaharanai wurin karatu nai. Barshi dai ya dawo ai zama mukai dashi mu jiya kaka haka yya hwaru ina kuma yanemo ubanai da shika hwadin wani shirmey yanzu. Basu daga wurin ba sukaga ya shigo dame awo suna auna fili tare da kara fasalin ginan dake wajen suka kwasa kuma suka fice daga gidan lokaci guda. Duk suka bishi da kallkn mamaki basu samu karin zama dashi ba sai baya kwana biyu da yazo masu da kayan abinci da za a dafawa bakin shi da zasu zo wanda yace yan uwan ubanshine. Dije kan ta kasa boye mamakinta dakinshi ta bishi ta sameshi tana fadin wai kai da gaske kake zancen ka dangin ka zasu zo garin nan nema maka aure ina ka samu dangin naka ? Kai tsaye ya bata amsa da garin mu naje kwanaki da kuke shelan cewa an saceni naje na nemo ubanane kuma na ga dangishi ya ganan yanzun yan uwanshina zasu taho su tsaya mani . Ikon Allah yanzu Amadi dama neman ubanka katahi yi ka kasa hwada muna ka barmu nan mun shiga tashin hankali aina hwada maki tahiya zanna kuma kin sani amma kika biyewa malam Tanimu tayi ta rudaki a gari. Yana fadin haka ya rabata ya fice daga gidan ta dawo tana sallati take gayawa yarta abinda ya fada mata din duk suka dauki sallati mahaifiyar nasa cewa tayi waya hwadamai inda zai samai ? Dan yau da zamani ki barshi kawai kai inna ni ban yarda ya samo mutumin nan ba dije tace nima abinda zuciyana ya bani yanzu ke nan. Sayayya yayi sosai don bakin shi don kowa bai yarda da abinda ya fada ba an dai dauka wasu mutane na daban ya dauko suzo su tsaya mashi matsayin dangin ubanai don sunsa babusu ba kuma wanda yasan inda ubanai ya hito. Abinci kan anyi unguwa ya dauka ai yan uwan mahaifinai na zasu taho nema mai auren da ya kakabawa kainai auren diyan mai kudi shina yayo hayan ubanan banza. Mota biyu ras sukazo dashi kana ganin su kaga fulanin usuli dogaye farare dasu tas ga kama na jini da suke dashi da mahaifninasa basai an tambaya gaduk wanda yasan habu dan filo kamar yadda suke kiranshi a zamfara din. Nan su malamTanimu aka fara kus kus lailai yan uwan ubanai na lalai suna sai wani kanin malam ladan yace meye shedan ku na yarda da hakan. Sai kuma aka koma aka sare ai babu tabas dasu din ne daya ya dauko hoton mahaufin nasa ya nuna sai kowa jkkkn shi ya mutu aka yarda da zancen su.
Chapter 131 · 0% Book details