Sashe 25
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da uwar garke a hannun shi yana ja zuwa wurin dattijon dake zaune saman kututuren da malam tanimu ya heke ya hada ice da ice a kofan gidan yana zama a sama. Yazo gab dashi ya mike tsaye yana fadin kai wanan ai zatayi kudi da yawa da daidai yar madaidaiciya ce sai insaya ai Zaka iya saya idan zatayima baba lalura yasa maishi fitar da ita aiko lalura yakai lalura wanda zaisa a fitar da guzuma haka iri mai kyau da ita yanzu zata kai nawa wanan ? Tau baba maishi tace jakka arba,in amma sai ka taya a, a yaro ba zan taya ba idan har ta bari ga kudin Allah yasa ta amfana dasu har abada. Kallon tsohon yayi cikin mamaki jin ko gardama baiyi ba daga sa suna har ya yarda da hakan shi ya banye wani kulli ya fito da kudin ya bashi ya karba cikin mamaki. Dubu biyar ya kirga ya mayarwa tsohon dashi sai lokacin suka hada ido dashi gabanshine ya fadi ras lokaci guda duk da tsohon yayi saurin kawar da kanshi gefe daya. Kai ya girgiza mashi tare da fadin jeka dasu yaro Allah yasa masu albarka abinda ka dafa yazama alheri a rayuwanka ya sake amsawa da amin baba yaja akuya ya tafi shi kuma ya koma gida cike da mamaki da al,ajabin wanan bawan Allah. Mama ya akayi Zahar take amfani da wanan tsohon motan bayan kowa saya mai sabuwa akeyi idan zai shiga jami,a amma ita sai naga tsohuwar mota take amfani dashi na Aisha ? Uwartace tace kazo ka tambayeni ko wa ? Haba mama ya ummah zatayi min wanan maganan kuma nidai na ganta yanzu ta shiga wanan mota yasa zo na tambayeki meyasa haka mama ? Haka naga daman yi don haka ka barta dashi amma mama baki ganin hakan ba da, , , , , , hannu ta daga mai tare da fadin kaga na fada ma ra,ayina don haka kada ka dameni. Koda aka bata tsohuwar tafi katfin shiganshine ita din uwarta yar waye da yarta ba zata shiga motan da Aisha ta ajeba ? Amma ainan gidan uban zarah ne bana wani ba don haka zarah daidai take da kowan mu a gidan nan ke nan irin wanan wallahi mama tauye hakkine fa hakan nan ? Baba ni zaka tsare kanayiwa fada kome koni zaka nunawa hanyar gaskiya a yau din na bata wanan din kaje kayi yadda zakayi ina jiran ka. Mikewa yayi tsaye ya saka hannayen shi cikin aljihunshi yana fadin alright ya fice daga part kai tsaye dakin shi ya nufa ya shiga wanka zuciyar shi na masa tukuki hakan da sukayi da mama din. Yana fito part din ummah ya nufa falo ya sameta ita kadai bayan sun gaisa tace har ka karyane ko baba naga kamar fita zakayi ? Eh wallahi ummah yau zan koma ka karyane ko haka zaka tafi tana kallon shi cikin tsure shi da idanunta a zuboma kunun gyada yace eh bani nasha kada nabi hanya ban karya ba. Bayan ta debo mashi ta kawo mai inda yake zaune a lokacin yasa hannu cikin aljihu yana fadin ummah wanan sakon Zarah ne idanta dawo abata na fada mata zan barmata a wurin ki. Kunyi sallama ke nan da ita ummah ta tambayeshi yace eh a gabana ta fita dazun amma ummah kina kallo akaba zarah wanan motar tana shiga ? Murmushi ummah ta sauke a fuskanta tana fadin me motar tayi ai da lafiyanta wace Aisha ta ajene aka bata yafi ta dinga zuwa ana haya ai ko ? Fuska ya bata ya dauki kunun yana kurbawa a hankali bai dade ba ya mike zuwa part din mama bayan tayi ma ummah sallama bai samu mama a falo ba sunce ta shiga wanka. Ya bar sako idan ta fito a fada mata cewa ta wuce zuwa Abuja daga can zai koma lagos jin haka yasa Aisha mikewa da sauri tana kiran uwar duk da tana cikin bayi haka bai hana ta fada mata gashi zai wuce ba. Saidai kafin su fito harya fita ya kuma kashe wayan shi da bai kara budewa ba sai bayan ya sauka Abuja ya nufi gidan Abba ya bude wayan nasa. A lokacin ne sakon ya jafar ya shigo ya bude yana fada mai mama ta kira tana fada sosai don me bai jirata ba ya tafi ido ya runtse ya kashe wayan nasa ya tura aljihunshi. Ya samu Abban mu baya jin dadi yana kwance ranan bai fita ba nan ya soma fada Abba ga irinta nan ummah na nan zaune ka dauketa ka mayar gusau gasu can basa komai suna zaune kawai kai kana nan kana wahala kai kadai sai yan aiki. Murmushi Abba yayi yana gyara zama yake fadin to ya na iya maimuna tace sai su koma gida dukkan su ita ta baro lagos ita wana dake nan dole itama ta dawo gida su zauna tare dasu. To amma Abba ya akayi Zarah take hawa wanan motar tana fita a cikin shi Abba wanan baiyi ba wallahi zan hada duk abindake gareni in sayawa zarah mota amma ba zata kara amfani da wanan motar ba daga wanan satin. Dakata malam ai abin baikai can ba wanan zancen da kakeyi ban taba sanin motan da Zarah take jaba a yanzu ni dai na san muyi magana da maman ku cewa za a samawa zarah mota in kawo kudi. Kuma na bata saidai bazan iya tuna komai yanzu ba kan hakan amma dai nasan an karbi kudin a hannuna kuma na bata yanzu kaje kafin tashin ku sai ka duba mata mota daidai da ita. Kabar kudinka wanan nauyinane yin haka amma gaskiya Abba ku kula don abubuwa suna son suna son rikicewa fa yanzu gidan nan don a gaskiya ummah tana hakkuri da kawar da kai ga komai amma ya kamata a duba mata hakan gaskiya. Baba nima nasan da hakan a yanzu na fara fahintar wasu abubuwan da nakeyi bai kamata ba amma ba yadda na iya don ban iya rikicin mahaifiyar kune. Abba kaika ajesu fa bai kamata ace ka fadi haka ba idan baka fitowa mama ta baya ba gaba dayan ku zaku halaka kan nu baku sani ba Sun jima suna magana na fahinta da dan nasa kafin ya fita zuwa ya duba motan kamar yadda Abba ya umurce shi dayi ya duba kuma ya samu mai kyau daidai dani anyi service din ta anyi komai ya dawo da ita gida Abba ya gani. Duk da saurin da yakeyi don ya fita zuwa school tunda sauran duhun asuba haka bai hanashi gane cewa uwar garke tana kwance cikin yayanta ba lokacin. Salatin daya sakane ya fito da Dije daga dakin yana fadin uwar garke kece kika dawo ko idona ke gizone wai yana kara nufar wurin da dabbobin suke kwamce fuskanshi dauke da mamakin hakan. Dije cikin dan dingishawa ta fito tana dadin sai naji kana zancen uwar gareke ko saboda sabo da itace yasa kake ganin tana ma gizo a idanun ka kuma ? Itama fitgita tayi tare da sake salati tana fadin Allah sarki uwar garke dawowa kikayi ta nufi waje tana cire mata igiya. Dije daga gidan wanan mutumin tagudo fa ra dawo nan to kuma aishi yace min daga kauye mai nisa yake dakatar da abinda takeyi rayi ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki. Kana nufi ba garin nan yake ba maishi yace haka ya fada min sai da sauki don abokin malam tanimu ne ai kuma yaga gidan dana fito da ita ai. Zan fadawa malam tanimu din tana nan ta dawo sai suzo su kama abinsu su tafi dashi Allah satki sabone sabo yasa tayi hakan ai Dije ta fada.