Sashe 183
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har na kwanta naji waya na ringing na dauka hannatuce cikin damuwa take fadin don Allah zahra kiyi hakkuri bansan cewa ranki zai baci haka dani ba. Na dauka yadda nayi zai taimaka maki gun mahaifinkine amma naga ranki ya baci da hakan kiyi hakkuri don Allah ta sake fada a sayaye. Bakomai amma gaskiya banji dadin hakan ba wallahi wanan matsalance ta cikin gida Hannatu bai kamata ki zake irin haka ba tunda nima kinji nayi shiru a lokacin gaskiya ban fatan irin hakan ya sake faru garemu. Na fahinta yanzu Zahra in Allah ya yarda hakan ba zai sake faruwa ba kuma na kirga kudin da Abba ya bani har dubu talatin nagode kwarai wallahi. Bakomai nina kwantane saida safe nace da ita ina hamma tace Allah ya bamu alheri amma barci da wuri haka ni dai na kashe wayan don ban iya surutu a lokacin. Sati daya kacal da hakan sai ga kiran wayan brother Bisi fitowana daga aji ina bakin masallacin mu zan shiga naji waya na ringing na tsaya na ciro da sauri ina dubawa naga sunan shi a rubuce a screen din wayan yadda nayi serving. Na dauka da sauri tare da sallama ya fara fadin takardun sun iso an kuma yaba da kwazon mijinki sosai a takardun nan. Saidai zai barki ya taho nan suyi interview yaya kika gani ya tambayeni cikin son jin amsan da zan bayar a lokacin da sauri nace haba brother koya kama ya zauna can ne aiba abin damuwa bane agareni yanzu . Muna maka godiya da wanan kokarin dakayi muna sosai saidai zuwa America yanzu gaskiya ba karamin abu bane a garemu gaskiya. No kubar komai a hannuna nine zan dauki duk wani nauyin tafiyan nasa har yaje ya dawo insha Allah fatana kawai ya yarda da hakan don mu cinwa manufar mu na taimaka mashi da nake sonyi ? Insha Allahu ba matsala don ya yarda dakai saboda na fada mai halakarmu dakai kana matsayin babban yaya a garenine sai naji yayi murmushi yace amma baki fada mai nine naso auren ki kamar in mutu ba ko ? Nima dan murmjshin nayi tare da fadin ba aure a tsakanin mune sai zumunci irin haka shiyasa Allah bai kaddara muyi aure ba na dora mai da gidiya bisa karamcin da yai muna din don a katse wanan zancen na tuna baya. Mukai sallama ya fada min na turo mashi da account dina dana mijina nace yayi hakkuri ya karbi na mijina kawai yakece min kona raina da abinda zai turo min din ne nayi min kadan ? Da sauri nace a,a ko bansan ko nawa bane nasan masu yawane kuma mai amfani a gareni yace to na turo zai kara kirana insha Allahu. Har na fito sallah ina tunanen zancen mu dashine haka kuma ban fadawa hannatu ba tun farko don na kula tana da yawan surutu Allah daine ya hadani da ita. Bayan na dawo gidane na danyi girki nakaiwa Dije don na kwana biyu banyi girki ba shiyasa na dora donta kawai dama tun a get din school na sayo danyen nama da kubewa da alaiyahu nazo dashi gida. Girkina a natse nakeyi yadda na saba har na hada tuwone Aisha data shigo ta karba ta tuka min shi muna hira muka saka a leda na bata ta mika min zuwa cikin gidan . Wanka nayi na fito na tayar da sallah don lokaci har ya dan shige muna kitchen din bayan na idar na zauna na dan jawo jakata ina duban a lokacin idona yakai kan ledan da ummah ta bamu ranan bacin rai ya hana in duba tun ranan. Danbun kifine dana naman kaza sai sai yaji naci a ciki da wani kwalban tutare mai kyau itin na Dubai din nan da ganinshi zaiyi tsada sosai don har da armpit dinshi daga gefenshi an rubuta mai Noor haiyat a jikinshi da larabci da kuma boko. Bayan na gama duk sallolina na fito na dauko leda a kitchen na diban masu wanan dambun nashiga cikin gida dashi na kai masu. Na gaidasu da wuni dije ta karba min tana kiciniyar bude ledan dana mika mata din daga can naji inna na fadin wai wai wai yarinyar nan ina kika fito da kayan dadin nan haka ? Nace wallahi ya dade a dakina ummah tace tabani shi tun ranan da mukaje gida gaisuwan yar anty Aisha din nan ban bude ba sai yau shine na debo maku. Nidai naji Dije na munko gode Allah ya karawa arziki albarka nace amma Inna ko uffan batace min ba sai zuwa can naji tace ai irin wanan abin haka bai kamata a fitar dashi a gidan nan ba tunda tayarwa mutum da kwadayi za ayi ga banza. Jinta fara sakin magana haka yasa na mike tsaye lokaci guda ina fadin to saida safe ku zanje in kwanta. Ban karasa fitaba naji Dije na fadin wanan rayuwa naki baiyi ba ke kan data cinye bata bamu ba shine nufin ki tunda bai isheki ba watau ta karo maki ko ? Kai umma zaki fara juya zancen ki ke nan duk akai maganan daya shafi yarinyar nan saiki mayar ya zama naki ni bansan abinda yasa kike haka ba wallahi. Banji amsan da Dije ta bata ba don nayi nisa a lokacin ba kwanciya nayi ba a lokacin don na samu wayata da miscalled dinshi don haka na sake kiranshi ya dauka yana fadin barin kiraki. Bayan na kashe ina gyara kwanciya naji ya sake kirana lokacin na dauka muka gaisa yake tambaya mutanen gida da karatu na amsa da lafiya. Kina cikin gida halan bakiga kirana ba ya tambaya na amsa da eh naje kawai Dije abune dama naso na kiraka tundazun sai aiki yai min yawa ban samu lokaci ba. Meya faru nace dama brother Bisi ne ya kira dazun wai ka shirya zakuje interview a can kuma, , , ban karasa ba naji yace inafa ke nan zamu tafi ? Can America din yace sai naji yayi murmushi yace kai zahra akwaiki da son wasa wanda ko lagos bai taba zuwa ba shine zai tafi har kasan America yin me a can ? Allah kuwa kuma yace ka turo mashi da account din ka na bank zai turo maka da kudin da zakai visa da sauransu nima kuma na tura nawa ya bani wanda zaka barmin a nan yace. Anya zahra abin nan baiyi yawa ba kuwa mutum ba dan uwanka ba ya kashe maka wanan uban kudin haka gaskiya ya kamata muyi nazari akan maganan nan. Amma kasan bamu rokeshi ba shine yayi niyar hakan don ya samu lada masu halin alheri haka suke abinsu sai su duba inda akafi bukata su taimaka don ladan hakan ya kai garesu. Tunda nasan shi da wanan halin na sanahi dashi gaskiya don lokacin daga mu har yayyen mu maza haka zai kaimu ayi shopping kowa ya dauki abinda yake so a dawo gida shiyasa muke jin dadi idan yazo hutu lokacin. Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke kafin yace to shike nan ba kinada account dina ba ki tura masa mu gani idan abin mai yuyuwace garemu sai naje. Mun dan taba hira mukai sallama na kashe wayan ina tunane kafin barci barawo ya daukeni can tsakiyar dare ina barcin na fara mafalki wai nakaiwa dabbobin su ruwa sai wanan bakar akuyar da suke kira da uwar garke take ce min. Kinyi kokari zahra dadin hakkurin ki yana tafe insha Allahu a sanadin ki yau Allah zai cika muna burinmu mu bar bawan Allah yayi rayuwan sallama. Zakice mutumce yar uwana muke hira a lokacin da ita sai har nake ce mata kuda suwaye tace nida na tare damu ai tun yana goye muke bibiyan lamarinsa. Tun ranan da uwarsa tayi fushin zuciya ta barshi waje a tsakar gida shi kadai ya kwana don mahaifinsa zai wuce ya barta tun wanan ranan muke bin duk wani al,amarinshi. Wanan mahaifiyar nasa tayi watau da yawa akan zafin kinshin barin mijinta har ta dorawa dan yaro laifin dabashi bane yayi shima mahaifin nasa ai kiran gagawane ya samu bai isa ya kara kwana uku a wanan garin ba lokacin. Amma duk basu gano hakan ba a lokacin saboda idanunsu ya rufe sun kasa fahintar ba tafiyan lafiya zaiyi a wanan lokacin ba. Ki tambayeta kiji a cikin darene suna kwance ya zabura yake fada mata inane nan meya kawoshi nan ita din waye har taso dora mai rashin hankali a lokacin. Amma da akai mai bayani ya gamsu bai kisu ba ya kuma karbesu hannu bibiya har ya bukaci a barshi yaje dasu garinsu amma iyayyenta sukai tsaye ba zasu yarda da hakan ba. Munturashi garin baban shi mun hadashi dashi ya ganshi duk ta hanyar hikima irin namu mune kuma mukasa a karya asirin a yanzu haka yana gab da haduwa da mahaifinshi insha Allahu. Munyi maganganu da dama da ita har da wanda ya shafi rayuwata dana gidan mu wanda hakan ya bani mamaki sosai a lokacin. In kina son ki gaskanta hakan ki tambayi tsohuwa yadda akayi rikon mijinki ya dawo gareta don sunso ya mutu a lokacin daga mahaifiyarshi har yan uwanta sai tsohuwar nan da mijintane basu yarda da hakan ba. Ki fadawa mijin ki in mahaifinshi ya zo gareshi kada ya nuna masa bacin ransa don shima ba yin kansa bane hakan duk da an fadamai a baya. Ni zan koma gida dama nazo mu gaisane kuma in isar maki da sako gareku daku kara hakkuri farin cikin ku yana tafe bada dadewa ba amma sai kin hada da hakkuri ga abinda zai biyo baya. Ina kallonta sai naga ta shige cikin icen tumfafiyan dake daga can gefen rumfarsu sai wani haske ya baiyana kamar walkiya a lolacin ta bace. Sai lokacin wai naji tsoro na yanka wani irin ihu ina salati hakanne ya farkar dani daga barcin kuma ina ihu ni kadai a cikin daki ga wani irin duhu daya mamaye dakin bako dan haske sai hakan ya kara ban tsoro a lokacin. Can naji kamar abu yana bin wuyana da sauri na shafa saidai bani ganin komai a lokacin amma ina tamtaman zufa don yadda naji goshina ya jike a lokacin.