Sashe 113
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
mashi zafi. Dan aikin dole yayi ranan da gaiya don ji yake zuciyar shi na shirin buga mashi zazzabi ne mai kada mutum ya buga mai nan take ya fara rawan sanyi sai amai kuma ya biyo baya. Hankalin mutanen gidan ya tashi sosai da ganin hakan malam musa ka fada yakewa Shattu cewa aikin da yayi ne yaja mashi hakan. Da kyat ya bude baki yace ai da zazzabin ya kwana zuwa safene yaji saukin shi shine yanzu kuma ya tashi mai fita maigidan yayi ya dan jima sai gashi ya dawo da ledan magani a hannun shi. Ya dan sha ya samu ya kwanta sai barci mai nauyi ya daukeshi bai kara falkawa ba ganin haka suka fice suka barshi ya samu barcin lokacin. Nan hankalin kowa dake wurin ya tashi ganin yadda hankalin maigidan nasu ya tashi lokaci daya haka gashi duk wanda aka tambaya ina yaga yaron nan yabi sai yace dashi ai bai ganshi ba. Sai wani mutum dayane yace yaga sun bi nan da sauri sun tafi amma bai kula da hanyar da suka bi gaskiya. Kudin da baici gaba da rabo ba ke nan ya juya ya shiga gida a rikice ba tare da yayiwa kowa bayanin abinda ya faru ba. Dakin shi ya shige yasa key bai sake fitowa ba donko matanshi basu ganshi ba a ranan sai washe gari yadda yaga dare haka yaga da safiya don ya kasa barci yana son tuno abubuwa da dama a rayuwan shi game da yaron nan amma ya kasa hakan. Daga cikin makarraban shine aka samu wanda ya tseguntawa matanshi abinda ya faru hankalin ta farkon ne ya tashi sosai don tunawa da abinda bokatan ya fada mata cewa. Kada ta yarda suyi ido biyu da yaron don duk ranan dayayi arba da wanan yaron asirin kwalban daya bata din zai kare . Ba komai bane kuma sai adana duk wani tunanen shi kan yaron daya fada yana dashi a can inda ya fara zama din daya bata. Sai gashi yau duk da ba a tabbatar ba an fada mata wani mai kama dashi yazo gidan har yaga Alh din inda hankalinta ya dan kwanta mai bata labarin ya fada mata cewa ai sam basu da kama ko ina da yaron na jini. Hakan yasa ta kwantar da hankalinta tayi barcin ta harda nasari washe gari kuma tana tashi ta shige zuwa yola wurin buki dama shi suka shigo yi. Don haka bata dauki wanan da cewa komai bane ta dauka gajiyane ya kama mijin nasu sai bayan tafiyantane balli ya tashi don Alh ya tubure kan cewa lalai danshine ya gani a jiya yazo gidan nan. Abu tun matarshi ta biyu tana daukan hakan wasa har yakai ta bugawa yan uwanshi waya tana sheda mashi suzo babu lafiya fa don bata gane kan mijin nasu ba yau. Bayan sunzo ne sai gashi ya fito falon suka gaisa nan suke tambayan shi meke farune wai ya dan murmusa yana gyara zama tare da fadin. Yaya sale nayi sakaci da yawa sosai don tun dawowana garin nan na fada maku nayi aure a can har matar ta haihu dani mun haifi da daya. Amma kuma sai wanan zancen ya fita min rai ga baki daya don ban taba zancen yaron nan ba daga baya ma sai na manta dashi sam ga baki daya a zuciyana. To jiya yaron nan ya biyoni suna jin hakan suka fara kallon junan su kamar suna zargin ya tabune don dama zargin da sukan masa ke nan wani lokaci tunda ya taba barin gida da girman shi. Yace kwarai don yanzun haka zancen nan da nake maku yaron nan yana cikin garin nan tare damu sai dai bansam a ina yake da zama ba. Don jiya yazo nan wurin amsan taimako tabbas akwai kama sosai dani dashi dayasa na danji faduwan gaba lokacin dana kalleshi . Amma kuma abinda ya fada min kafin ya fita shine ya tabbatar min da cewa shi din ne dai ya biyoni garin nan don cewa yayi. Sai kuma yai shiru ya dukar da kanshi kasa kamar yana tunane ko takaicin abinda zai fada jin shirun yayi yawa daya daga cikin su yace muna jin ka . Dago kai yayi da niyar magana amma kuma hawayen da suka zobo mashine suka hanashi magana suma jikin sune ya mutu don ganin halin da dan uwan nasu ya shiga ciki a lokacin sun san ba karamin zance bane wanan.