Sashe 63
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
shiru ko ina kamar ba mutane mota na parker na fito ina kullewa naji muryan shi a bayana yana fadin. Barka da fitowa Zarah na sheda muryan shi don haka na juyo ina fadin ina kwana brother lafiya ya bako jiya kin taimakemu sosai wallahi da yau saje zamuyi dagani har tsohuwar kakata a gidan mu. Ban tashi ganin sakon ba sai bayan har nayi alwala ina shirin fita sallah na dauko waya nagani mun gode kwarai Allah ya nuna muna karshen shi lafiya nace Amin. Kana ta godiya kamar wani abu wanan hanyace ta taimakon juna ai nasan ko kai kaji zaka aiko muna da hakan ya dan murmusa kafin yace. A gaskiya zarah naso ganin ki dama muyi magana kan wanan dawainiyar da kika dauko yi muna a gidanmu haka ina gudun abinda mutane zasu fada kan hakan . Gara mu tsaya da mutunci haka a tsakanin mu don kinsan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba a duniyan nan hakan zai jawo dan tsegumi da zai iya bata muna suna ga alakan mu dake. Ban tsanmanin duk abinda da za a fada na bataci ne a tsakanin mu don kowa yasan mutuncine tsakanin nida kai hakama wasu dauka suke cewa mu yan uwane na gaskiya dani dakai din yanzu. Don ganin irin mutuncin dake tsakanin mu dakai so duk abinda zasu fada su fada nidai nasan nice ke karuwa dakai yanzu ba abinda kake gudun su fada ba din ne. Amma dai duk da hakan don Allah ki dan rage nayi murmushi kafin nace dashi abu daya zai saka na rage shine wanan akuyan dake firgitani gidan ku da ba hakan ba kullun sai nakaiwa kaka abin shan ruwa da kaina gidan ku. Haka kike da kafiya ba kafewa bane na bashi amsa ina dan murmushi nace idan munbi ta mutane ko gaisawa zai zama matsala a tsakanin mu nan gaba don ko yaushe idon su akan gulma yake. Tare muka jera har kofa building din mu ya kaini mukai sallama ya juya ya wuce wanan rana shine zance rana ta farko da muka tsaya nidashi mukai magana mai tsayi a tsakanin mu irin hakan. Bayan shan ruwane da yamma suna zaune tare da Dije a kofan dakin Dije din da suka shimfida tabarma su biyu a gida ya dauki waya ya danna kira a layina. Na dauka naga sunan shi na danna dauka yayi sallama na amsa yake fadin Allah yasa nine mutum na farko dana fara maki barka da shanruwa kada wani ya rigani samun ladan dake cikin hakan ? A gaban ummah nake hakan bai hanani yin murmushi ba nace ai kuwa kayi sa,a kaina na farkon kirana amma ga hannatu nan yanzun tana kirana kuma. To ki gaidasu mama ina masu barka da shan ruwa Allah ya bamu ladan dake cikin sa ya yafe muna kura kuran mu yasa muna cikin yan tattatun bayinsa na amsa da amin mukayi sai anjima dashi. Na dauki wayan hanne nan ta hauni da fadin ke mutumiyar ina ta kira kina busy haka ko kiyi sabon kamune banda labarin hakan . Mikewa nayi nabar falon ina fadin ke dai hannatu haka zaki kare da sheri har da watan nan mai albarka sai kinyiwa mutum sheri. Brother ne fa ya kirani yau yana min barka da shan ruwa muke magana zakice wani sabon kamu kai kice master da kanshi ya kawo gaisuwan girma ashe shima muka taba hira sosai kan lecture din ranan kafin mu kashe wayan nikan na kwanta ban sake fitowa ba saida asuba da muka tashi yin sahur. Yana aje wayan ya kalli inda Djje take tana cin abinci yace wasu mutanen akwasu da kirki tun suna kanana yarinyar nan fa dije yar gidan mai kudine da garin nan ake ji dashi amma bata dauki duniya da girma haka ba. Idan kin ganmu da ita saiki dauka ba yar kowa bace ita din don sam bata nuna hakan hakama yanayin shiganta kulun na mutunci ne. Ai wasu sun san ya kama ko a cikkn yara sai ka samu masu hali irin na dattako garesu yace hakane ko kudin nan ban fada maki bane natane ta ban na kara nake jan wanan jarin dashi . Ranan da naje kauyen nan buhun gero hamsim na sayo maiwa ashirin sai masara moto guda na dauko ni kadai aka sauke min kaya kuma duk sun shige washe gari mai kudi kuda ya sayesu ya bani kudina kasa wallahi. Amadi kace arziki ya budu muna har kana iya dauko abin dubu dubbai haka ka sayar yanzu a garin nan wallahi Dije haduwana da zarah ya zamo min alheri sosai a rayuwana Allah ke nan. Kaga ubanka yayi watsi dakai a duniya ya manta da zancen ka a cikin duniyan nan gashi Allah yana taimakon rayuwan ka ta hanyar da ba a zata ba. Shiru yayi don ya tsani Dije ta dauko mai zancen iyayyen shi idan suna magana idan ba don Allah da ita Dijen ba sai yace ai shikan baiyi dacen iyayye ba don ko ita mahaifiyar nasa daya sani ya bude ido da ita mijin da take aure ya yanke alakanshi da ita yanzu. Don kuwa ta zabi bin mijin ta can dajin Niger state inda yake noma suke zaune har suka hayayyafa dashi yanzu bata zuwa gida kai da kai saita dibi shekaru take leko su tayi kamar wata daya ta koma garin sai kuma bayan wasu shekaru masu tsayi take dawowa garesu don haka ba zaice shi yasan dadin mahaifa ba saidai kakan shi mace itace Dije. Kawar da zance yayi da fadin waiko yau uwargarke lafiya ta kalau kuwa duk shigowa nayi sai in sameta kwance tana barci ?