← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 286

Sashe 118

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bamu hadu da mommy ba har wajajen goman dare kafin naji muryoyin su kaf diyan dakin su suna magana akan abinda ya shafi rayuwan su. Saidai zancen ya shafi wani rikicin daya tasone a tsakanin su lokacin bukin uwartake kolatin sasanta tsakanin su a lokacin. Saidai duk laifin akan mommy suka dorashi inda ita kuma bata yarda da hakan ba inda nake jin muryan mommy na fada da karfi da alama bata yarda da korafinsu a kanta bane. Kafin naji wace ke biwa babban yar nasu ta sako zancen na a cikin maganan su tana fadin irin abubuwan da mommy din tayi ta nuna mata rashin jin dadin hakan da tayi. Nan ta sake daga murya garesu tana fadin ina dai wanan kuma ba matsalan daya shafeku bane ko kuma ita din ma zaku saka min idone a kanta yanzu kuma. Duk abinda nakeyi sai a zauna ana sakawa mutum ido don kawai ayi mashi sheri ace ga abinda mutum yayi in bashi ba meya kawo zancen yar mijina a bakim ku yanzu ko ita ta fada maku hakan kum ? Bata fada muna komaiba wallshi uaarsu ta fada sai naji tace kada tayi mana ni dama ai don ibanta nake son na taimaka mata tunda taki ai shike nan gata ga fakirin nata da take so ai sai tayi ta kaya. Daga haka na daina jin muryan su ina nan wurin ina tunane har barci yazo ya daukeni na manta da zancensu . Komai nasa ya gama hadawa a lokacin ya shirya tsab don gari yake jira ya waye yayi sallama da masu gidan yatafi don alkawari ya daukarwa kanshi cewa ba zai kara kwana wanan garin ba kuma. Haka kuma yayi alkawarin cewa bai kara waiwayo wanan garin na mambilla a rayuwan shi ya sadakar da zancen zai kara haduwa da mahaifinshi. Yasan cewa babu zancen shi a zuciyan wanan mutumin yanzu duba ga yadda yaji labarin harda da wanda sukai kama dashi sosai yadda mutane suke fada din kuma suke ganin kamar tasu. Yana jin kiran sallah ya fito yayi alwala don har ya riga malam musa tashi shidake tayar dasu a kulun suyi sallah jam,i sai gashi yau shi ya riga dattijon tashi. Daga nan daki ya koma ya fara gabatar da nafila bai dade da tayar da sallah ba yaji fitowan tsohon daga dakinsu shima har ya gama abinda zaiyi yana jin motsin shi kafin yazo yana bugamai kofa yayi gyaran murya dake nuna yana falke a lokacin shima. Tare sukaje sallah sun dan dade basu dawo gidan ba kafin su dauki hanya su dawo gida bayan su gama zikirin safe kamar yadda suka sabayi din. Sai bayan sun dawone ya dibi ruwa da sanyin nan yaje bandaki ya watsa ya fito ya shiga dakinshi ya shirya tsab ya fito a cikin shirin shi ya samu shattu na kashe kuna shi kuma malam musa yana zaune a dan rufar shi yana tulawa. Shattun ya fara gaiyarwa kafin ta dago kai ta sauke ido a kanshi yana rataye da yar jakarshi ta tafiya da yazo dashi garin. Kallon mamaki take mashi ta amsa ya mike zuwa wurin malam musa ya duka yana masa ina kwana ya dago kai yana amsawa tare da fadin yau ba zaka zauna tulawan ba ke nan ? Sai idon shi yai arba da jakar tafiyan shi a bayanshi don haka ya kasa boye mamakinshi a lokacin saboda tuhumar da zuciyan shi ya fara mai zai tafi ke nan kome matashin yake nufi dayin hakan. Ya naganka haka dattijon ya tambayeshi ba tare daya iya amsa gaisuwan daya fara mashi ba tare da kura mai ido cikin son jin amsan da zai bashi din. Baba zan tafi gidane yau din nan insha Allahu don yanzu kuma hankalina gaba daya ya koma gun kakata dana baro gida saboda nasan tana can cikin wani hali na rashin sanin idan na shiga a yan kwanakin nan. Nasan kuma zamana a wanan gari a yanzu haka zai iya haifar da barazana a gareni a yadda na fahinta don haka nake son inyi gagawan barin garin nan a yau din nan. Amadu ya kira sunan shi na yanka kamar yadda ya fada mai din sunan shi tun farko yace nasan kana da ilimin addini dana boko. Don haka zaka iya hango abinda ni ban hango makashi ba a yanzu to amma dai komawan nakane a yanzu tun kan ai wani abu gameda mahaifinka din shine ya daure min kai a yanzu. Babu komai baba saidai zuciyana ta kasu biyu a kan matsayina a zuciyar shine don bansan a wani rukinin nake a wurin shi har in bai fadawa yan uwanshi komai game dani ba kaga hakan zai iya haifar da wani matsala mai karfi kuma a tsakanin mu. Don haka gara in bar garin nan kasan masu kudi yadda suke a yanzu zai iya gano gidan nan ya turo a halakani ko ai maku wani abin da bai dace ba. Indon wanan ne zaka tafi kayi kuskure kuwa koma me zaiyi maka yayi din ka dai tabbata a dansa har in mun zauna dashi din nake gani. Kayi hakkuri baba ka barni in tafi a yau din don nasan daga baya zaka fahinci manufata da abinda yasa na yankewa kaina wanan hukuncin a yanzu. Saidai taimako daya da nake son kai min baba shine duk sanda na tashi nunawa wani ahalina zan nemoka a matsayin dan uwan mahaifina din don girman Allah. Shiru dan dattijon yayi na dan lokaci kafin yace wanan yafi komai a wurina yanzu da zaka yardama ni har gida sai in kai ka amma ko yanzu ma hakan bai baci ba garemu zanyi kokari nan gaba inzo har garin naku na ganka a matsayin dan uwa a gareka ni da wasu. Godiya sosai ya karawa dattijon kafin shatu ta iso wurin da kwanon kunnunta tana fadi a cikin yarensu naga kamar yaron mu zai tafi ko ? Mijin yace haka ya kuduratawa zuciyan shi duk da banji dadin hakan ba don baso ya tafi hakan cikin bacin raiba gashi ni kaina bai fada min komai game da haduwan nasu da mutumin wanda yake zaton mahaifinshine shiba mu sani. Ban rike sunan shiba nadai san cewa shidinne ta maganan dana fada mai duk da bai ban amsana daga bakin shi ba amma yanayinshi gaba daya ya gama nuna min shi din ne. Duk yadda malam musa uaso ya dakatar da matashin yaki yarda da hakan karshe dai malam musa din yace ba zaka bi hanya ba batare daka karya kumallo a gida ba . Wanan ya dan tsayar dashi ya tsaya yasha kunun sama sama malam musa din ya kalloshi yace kana da guzurin da zai kaika har gidane ya dago kai yace insha Allah kudin dake wurina zasu kaini har gida baba. Bayan ya dan kara kurba kunun ya mike yana masu godiya ya sallami shatu ta nuna mai damuwanta a fili kan rabuwan su dashi a lokacin. Tare suka fito da malam musa din sai dai ba mutane don safiyane sosai kowa na gidanshi lokacin yana rage hantsin safe da iyalanshi agida. Malam musa din baiyi aune ba yaga ya nufi wurin garken shi ya dan tsaya kadan kafin ya juyo su kama hanya saiga mai mashin suka tare yayi jinga ya kaishi tasha nan malam musa din ya mikowa Ahmed din wasu kudi masu yawa yana fadin ka karbi wanan ka kara kayi amfani dashi . Ahmed din ya durkusa kasa yana kada kai alaman bazai karba yace ashe baka daukeni ubaba a wurin ka ka karba kuma ina rokon ka idan kaje ka kirani muji saukan ka yace insha Allahu baba. Ya mike yana dan goge hawaye a fuskanshi ya tafi yana dagawa malam musa din dake jin wani abu a cikin zuciyar shi game dasshi lokacin hannu. Yayi sa,a yana zuwa mota mota mutum daya ake jira ys biya ya shiga ba bata lokaci suka bar garin mambilla din suka dauki hanya bin garin yake da kallo kafin ya mayar da idanunshi ya lumshesu. Fada takeyi sosai a wayan kafin ta mike tana fadin gida zata koma mambilla don maigidanta baida lafiya hankalin kowa ya tashi da jin haka. Anzo dadi dadi ana buki gashi yanzu kuma mumunan sako ya risketa kowa da abinda yake fada a wurin ita kan jinsu takeyi kawai don ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta lokacin. Don hankalinta yayi kololuwar tashi sosai ga abinda yaronta aminta kuma hadimin maigidan nata ya fada mata a safiyan ranan suna kama hanya tadauko wayan ta daga cikin jakar ta tana neman wani layi. Ba adauka ba saida ta kara kira aka dauka yaren su takeyi na mambillawa tana fadin su hadu da mai wayan gata nan ta kamo hanya zata dawo mambilla din yanzu . Ta dan jima tana waya da wace ta kira din a wayan kafin ta kashe wayan tana han tsuki duk a zatonta driver su din baya jin me take fada don bata taba sanin ya iya yaren nasu ba saboda bai taba yi a gabanta ba taji. Tafiya sukayi sosai a ranan karfe daya suna cikkn garin mambilla din suka karasa gida direct part din mijin nasu ta nufa tana son sanin halinda yake ciki. Zaune ta sameshi shi kadai yana tunane gabantane ya fadi ras ras don dan canjin yanayin data ganshi a ciki don a cikin kwana daya ya fada yayi dan duhu sosai a lokacin. Jin an shigo yasa shi dago kai yana kallon kofan itace ta shigo yake binta da kallo kamar yana son ya tuno da wani abu lokacin amma ya kasa hakan. Kofan aka sake turuwa lokacin duk suka juya don ganin ko waye ya shigo dayan kishiyar tace tashigo dauke da kayan abinci a hannunta tana sallama. Saidai tana ganin ta tadan shiga rudu tana fadin au ashe kun dawo sannuku da zuwa ta dan tsuke fuska kafin ta amsa tana fadin eh mun dawo yanzun nan. Abincin ta aje tana kokarin jerawa a gabanta take fadin barshi kawai aiba yanzum ne zaici ba ko tace cikin murmushi shiya umurceni na kawo mashi yaci yanzun din. Kallon mamaki ta jefi kishiyan dashi na yadda ta bude baki ta iya bata amsa kai
Chapter 118 · 0% Book details