Sashe 121
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ubangiji ka zaba muna abinda yafi zama alheri garemu ka saka tausayi da imanin duk wanda ka zaba muna ya Allah kada ka bashi ikon cutar da bayin ka ka saka mashi tausayi da jinkan na kasa dashi. Allah ubangiji ka jikan magabatan mu kasa Aljanna ce makomar duk kan musulmai albarkacin kalman La,illah ha,illah Muhammadan rasulunlillah ya cece mu Amin. Allah ya taimaka tafiyan dare yayi koda ya biyo layin su ba mutane sosai a lolacin don haka ba wanda ya ganshi dan abinda suke rufe gida dashi ya tura gidan ya bude ya shigo. Ya samu Dije ta kwanta a lokacin yayi shawaran ya kwankwasa mata kofa sai kuma yaga kada ya tashe ta daga barci don haka yayi shawaran ya aje kayan tsaraban daya sayo din a kofan ta kawai. Bayan ya aje ya juyane ba tare daya kulaba yayi karo da kwanon data kife daga gefen dakin daga cikin dakin yaji muryan ta tana fadin wani na nan ? Ido ya dan lumshe kafin yace nine Dije Amadina ya bata amsa daga inda yake tsaye Dije da taji muryan Amadin a bazata tayi wani tsale ta mike zaune tana sake fadin wanena shin ? Amadi kaina kamin gizo ko kunuwana na ka min karya haba Dije ga muryana kina ji zakice karya kuma ko barci kika farane wai ? Ji yayi tana kokarin bude kofan nata daga ciki yasa shi tsayawa ya jira ta bude tako bude din tana fadin Amadi ina ka shiga haka kabar gida lokaci mai tsawo haka ne ? Missa kayi tahiyar ka cikin duniya kabbanni nan ni kadai shin baka tunanen halin da nii shiga bayan tafiyan ka ? A lokacim ta karasa bude kofan ta fito don ta tabbatar inshi dine sukai arba yana tsaye daga kofan saye da taguwan shi da wando baki kaida ganin shi kasan yayo tafiya mai nisa a lokacin. Ina kakshigane danga tahiya haka mai tsawo baka fadawa kowa inda kakje ba abinda baka tabayi ba a ruwanka barin gida haka danisa. Buhun tsaraban shi ya nufa ya dauka yana kokarin shiga dashi daki ta jaye ta bashi hanya ya shiga da kayan cikin daki ya aje kafin ya dago ya fito yana kokarin juyawa don kayan daya bari waje ya dauko sauran yaji muryan dije din na fadin. Shin ina kak shiga hakane ina magana kayi shiru daniya haba Dije kin san dai bani zuwa wurin banza ko don ban taba abin banza ba a rayuwana. Allah baka hakkuri amma ka dau alhakin mu dakka daga muna hankali kwanciya asibitina kawai a banyi ba kowa gari ya dauka wani mugun abuna yassameka. Dauri ka fada muna inda zakana kaga sai mu sani da kyar ya iya budan bakinshi yace kuyi hakkuri ban dauka zan dade bane haka nima don tafiyan da niyar kwana biyu niyishi ko uku sai ya kasance haka. Awo dama tahiya ita tagaji haka kafin kayitana kake da ita da zaran kayita ko ita addakai badai an dawo lafiya ba ta sake tambayan jikan nata don ganin rashi babu dadi a lokacin. Bai bata amsa ba ya kara shiga da kayan ciki tana yada mai haske yaga inda zai aje kayan ta kara fadin dauri ka bugo wanga abin zamanin ko a makwabtana mu sani. Ki kwanta saida safe zanyi sallahna yanzu Dije ya fada yana daukan buta ya nufi bandaki bayan yaji akwai ruwan da zai isheshi amfani a lokacin. Saida ya kewaya ya fito har lokacin Dije ta kasa shiga daki ta kwanta kamar yadda yace din da ita ya duka ya fara alwala yaji tace kaci wani abuna ko a hanya gashi yau ban dahwa komai ba a gidan . Jin hakan yasa ya dago kai da sauri yana fadin saboda me dije babu abinda zaki dahwane ko me ya tambayeta cikin son jin abinda zatace din dashi lokacin. Sai yaji tace kona dahwa ma baci zanyi ba shiyasa na hutar da kaina da dahuwan saidai in kai dan kwano in sayo in dawo gida wani kuka yaji dayasa ya firgita. Ba kuma bakon kuka bane sai sauti muryan uwar garke haka yasashi kaduwa har yaji gaba shi ya fadi lokaci guda da sauri ya karasa alwalan ya mike yana lalubo yar wayan shi daga cikin aljihunshi. Yana haskawa ga dabbobin su biyarne a wurin yagani a daure kuma tabbas uwargarkene wanan a madaurin ta ta mike tana kiwo. Dije yaushe akuyan nan ta dawo gidan nan daga daki dije ta amsa mai da fadin kaidai bari dan albarka aini akuyan nan ta wuce sanina yanzu saidai ido da addu,a kawai. Akuya sai ta kwasa ta tafi sai lokacin da taga dama ta dawo ni na kasa gane me wanan yake nufi da hakan ko wani gidane ta samu take labewa ko wani ke kamata idan taga sarari ta gudu oho ? Bai iya cewa komai ba sai addua da yakeyi a zuciyan shi lokacin don baima san abinda zai fada ba game da uwar garke din data zama mai waibuwa a garesu yanzu. Haka ya ja kafa ya shige dakinshi da a yanzu yaji shi daban sai zafin daya doki fuskanshi haka ya daure ya tayar da sallah bayan ya dan kakkabe wurin yayi shafa,i da wuturi ya samu wuri ya kwanta zuciyan shi cike da tunane kala kala. Ban samu ganin su yaya musa ba don tun dana shige daki ban fito ba sai washe gari inda na tashi na samu su yaya din a falo tare da Abba suna magana. Suna ganina ko wanin su ya washe baki a cikkn mamaki da sauri na nufesu na durkusa ina gaidasu ya musa ke fadin dama kina garin nan ne yan mata ? Tana nan tazo hutu kasan mama da son zaman abuja dama dolene ya kaita gusau ta zauna dama don rashin mace ce a gidan yasa ban daukota duk hutu don tafi sabawa da nan din. Nima nashayin wanan tunanen cewa na samu lokaci in daukosu dukan su har ummah suzo nan su dan kwana biyu ko din makwabtan dasuke damuwana da tanbayan su idan sun gani. Ai yanzu tana jin dadin garin tunda ta hadu da wani dan iskan yaro daya fara hure mata kunne a yanzu Abba ya fada daga inda yake zaune. Gaba dayansu suka kalloni sai ya jafarne yayi saurin magana yace haba dai Abba dama ace su Aisha ka fada zan yarda don sune rawan kansu yai yawa. Gata dai wanan din yana nunani da cokalin dake hannunshi lokacin yace shiyasa naga gara da anyi hutu ta dinga zuwa nan kusa dani zaifi. Ya musane ya kalleni yace wai hakane kanwata da sauri na girgiza kaina alaman ba hakana bane daga inda Abban yake yai min wani irin tsawa yana fadin. Karya zan maki kome ku diba yarinyar nan wai har zataje ta dauko min wani fakirin yaro mara asali har yana zo min har kofan gidana don uwarta ta daure mata gindi yin haka. Abba be cool don nasan haka kawai Zahra ba zatayi abinda bai dace ba kuma ummah ta sa mata ido kila dai wani abin ne ya hadasu daban ko ? Ya juyo yana ajiye cibin dake hannunshi da yake shan tea yace zan zauna da ita inji abinda ke gudana Abba no ai basai ka zauna da itaba don naga tana son ja dani akan wanan yaron dam matsiyatan. Ko zuwa kanon nan da sukayi ace wani dan mutunci yazo neman ta amma yarinyar nan ta rufe ido taci masu mutunci dagashi har ita hjy karima din karshe ma taso hadata da yan uwanta a kan maganan fada. Wani irin dagowa nayi na kalli inda Abban yake cikin mamakin jin abinda ya fada din lokacin kafin nayi kasa da kaina hawaye yana zuba min a idona mai nuna alaman kazafi akaimin ga hakan. Abba yaci gaba da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba sai ya musa ne ya mike ya kama hannuna zuwa dakina don nan yaga na fito lokacin. Har ciki ya shiga dani ya zaunar dani saman gado yana fadin ya akai hakanga zahra a sanina kedai ba mai rigima bace zahra ga kuma Abba yanzu yana fadin zance mara dadi a kanki ? Da kyar na iya dago kaina don jin ya sake maimaita min tambayan nace wallahi Allah yaya ba hakana bane nan na kwashe komai na fada mai har da zancen mommy din ban boye mai komai ba. Zuwa lokacin ya jafar ma ya shigo dakin yace shi yaron Abba ya fada min wai baida baba ke nan shegene kome zahra ? Kai na girgiza mashi nace ba gaskiya bane yaya last da mukai waya dashi ya fada min yana taraba zaije gun mahaifin shi ne. Da baida baba aiba zai fadi hakan ba kuwa ya musa ya amsa daga inda yake zaune is OK ya jafar ya fada ki bari zanje Zamfara yau zan zauna da ummah akan zancen. Da sauri na dago kai ina fadin don Allah ya jafar ka wuce dani wanan matar makirace sosai bana jin dadin zaman gidan nan sam wallahi. Idan nayi hakan Abba zai dauka wani abune no kaje kawai zanzo da ita zuwa jibi don na fahinci wani abu cikin zancen zahra din ni zanzo da ita gida ka wuce kawai zamuzo tare ya musa ya fada. Sai safa da marwa takeyi a cikin dakin nata kafin can wayanta ya dauki kara kobata duba ba tasan me kiran nata don shi ta sakawa irin ringing tone din wani wakan larabawa ne da akewa habibi. Ta dauka cikin saita muryanta yake fadi daga bangaren shi kizo ga sakon yasir an kawo ta karba da gani fitowa saida ta dan bata lokaci ta nufi falon. Mijin nasu ne a zaune tare da amininshi Jabbi sai tellan yaranta maza dake gefe daya a takure ta shigo falon cikin isa da izza da takama kamar bataga jabbi din ba ta fara fadin. Yau Isah tellane gidan eh hjy naji ance kunzo shine nace barin sheko in kawo dinkin nan nasu oga yasir don yace akwai wanda zaikai mashi can idan na kawo maku. Eh nima yayi min waya kwanaki idan nazo na karbo mashi dinkin yana cirowa yake fadin kai hjy ashe